Me dokokin Najeriya suka ce kan tsare wanda ake zargi da laifi?

Asalin hoton, Getty Images
Mutuwar wasu masu haƙar ma'adinai a jihar Neja ta sake jawo muhawara kan yadda jami'an tsaro ke mu'amala da mutanen da ake zargi da aikata laifi, musamman batun tsare su kafin a gurfanar da su a gaban kotu.
Lamarin ya sa wasu ke tambayar irin tanade-tanaden da dokokin Najeriya suka yi kan kama mutane da kuma tsawon lokacin da za a iya tsare wanda ake zargi kafin a yanke hukunci a kansa.
A Najeriya, kundin tsarin mulki da sauran dokoki sun tanadi cewa duk wanda ake zargi da laifi yana da haƙƙin a ɗauke shi a matsayin wanda ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.
Dokokin kuma sun fayyace sharuɗɗan kama mutum, tsare shi da kuma lokacin da ya kamata a gurfanar da shi a gaban kotu, tare da tanadin kariya daga tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Yayin da ake ci gaba da neman ƙarin bayani kan abin da ya faru a Neja, BBC Hausa ta tuntuɓi masana kundin tsarin mulkin Najeriya don jin abin da dokokin ƙasar suka tanada dangane da tsare mutanen da ake zargi da aikata laifi da kuma haƙƙoƙinsu yayin da bincike ke gudana.
Ya halasta a tsare wanda ake zargi da aikata laifi?

Asalin hoton, Getty Images
Barista Nuhu Hamza Dantani masanin .... ya ce dokokin Najeriya sun yi bayanin hanyoyin da ya kamata a tsare mutanen da suka aikata laifuka daban-daban.
Ya ci gaba da cewa sashe na 36 (5) ya yi tanadin cewa duk wanda aka kama a matsayin zargin aikata laifi a doka ba a ɗaukarsa a matayin mai laifi ba, har sai kotu da same shi da laifi.
''Duk wanda ake zargi, to ba laifi ya aikata ba, har sai an gurfanar da shi a kotu ta kuma same shi da laifi bisa hujjojin da aka gabatar mata'', in ji shi.
Me doka ta tanada kan haƙƙoƙin wanda aka tsare?
Barista Nuhu Hamza Dantani ya ce duk wanda aka tsare dokar kasa ta tanadar masa wasu haƙƙoƙinsa.
Masanin dokokin Najeriya ya ce akwai haƙƙoƙi da dama da ƙundin tsarin mulkin ƙasar da tanadar wa wanda ake tare da shi bisa zargin aikata laifi ba, ciki har da:
- Ƴancin rayuwa
- Kula da lafiyarsa
- Ba shi abinci da ruwan sha
- Yancin ɗaukarsa a matsayin marar laifi har sai an tabbar da laifin
- Ƴancin walwalwa
- Kai shi kotu cikin kwana ɗaya zuwa biyu.
Masanin dokokin Najeriya ya kuma ce ana tsare mutum ne idan aka zarge shi da aikata manyan laifuka, da suka kunshi kisan kai da fashi da makami da sauransu.
Dole ne sai an tsare wanda ake zargi da laifi?
Barista Dantani ya ce bisa tanadin doka ba kowane laifi ba ne sai an kama mutum, kuma an tare shi.
''Ai abin da ya sa ake kama waɗanda ake zargi da aikata laifi shi ne idan ana tsoron za su iya guduwa'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa idan ana da tabbacin cewa wanda ake zargin ba zai iya guduwa ba, to ba dole sai an kama shi ba.
''Abin da ya sa ake kama waɗanda ake zargi da aikata laifi shi ne idan ana fargabar idan an bar su za su iya guduwa ko su lalata bincike ko kuma ba zai iya zuwa gaban kotu ya gabatar d akansa ba'', in ji shi.
Tsawon wane lokaci ya kamata a tsare mutum?
Barista Dantani ya ce doka ba ta damar a tsare mutum har na tsawon lokaci a hannun jami'an tsaro ba, matsawar ana zarginsa ne da aikata laifi.
''Sashe na 35 (4-5) ya yi tanadin cewa idan aka kama wanda ake zargi da aikata a kai shi kotu cikin sa'o'i 24, idan kotu ba ta wuce kilomita 40 ba daga inda aka tsare shi'', in ji shi.
Masanin dokokin ƙasar ya ƙara da cewa ''idan kuwa tazarar kotu daga inda aka tsare shi ta haura kilomita 40 to a kai shi cikin kwana biyu''.
Sai dai ya ce idan akwai hujjojin da jami'an tsaro ke nema daga bincikensu, za su iya neman izinin kotu na ci gaba da tsare shi har sai sun kammala binciken.











