Tsadar mai na sa ni tafiyar kilomita 10 kullum a ƙafa - Ma'aikacin gwamnati

Wani mutum na tafiya a ƙafa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da farashin man fetur ke ci gaba ƙaruwa ba tare da nuna alamar sassautowa ba, wasu mutanen a birnin Kano na Najeriya sun koma tafiyar ƙasa bayan ajiye ababan hawansu ko kuma sakamakon tsadar sufuri.

Kawo yanzu dai ana sayar da man fetur kowace lita a kan naira 1,470 zuwa 1,500 a birnin Kano.

BBC ta tattauna da wasu mutane a birnin wadanda aka same su suna halin tafiya a ƙsa zuwa wuraren ayyukansu da kuma ziyara.

'Ina tafiya daga Dandago zuwa Matan-fada'

Za a iya cewa idan akwai mutanen da tsadar man fetur ɗin ta fi shafa su ne ma'aikata waɗanda duk da yanayin da ake ciki albashinsu bai ƙaru ba.

"Wallahi tsadar man fetur ce take sani wannan tafiyar a ƙasa ka ga ma na kusa zuwa inda zan je. Da ina biyan naira 500 a kai ni Matan-fada daga unguwar Ɗandago. Amma yanzu an ce sai na bayar da naira 800....

To idan na bayar da 800 nawa ne albashin nawa? Ai ba zai ishe ni ba. Ma'aikacin gwamnati ne ni. Nawa na biya kuɗin ruwa...kuɗin makarantar yara. Magani ma saye ake yi..." in ji wani ma'aikacin gwamnati da BBC ta haɗu da shi yana tafiya a ƙasa.

Ma'aikacin ya ce shi yanzu haka ya mayar da tafiya a ƙasa a zuwan atisaye.

"A ƙafa zan koma gida mana. Shi kenan ka ga na yi atisaye. Ka ga na yi tattaki. Ba ma ni kaɗai ba ne. Muna da yawa. Idan muka ɗauki rukuni sai mu yi ta tafiya duk wanda muka zo unguwarsu sai ya tsaya ni kuma tunda na fi su nisa sai na wuce Ɗandago."

Tafiyar kilomita 14 domin zuwa asibiti

"Daga Masallacin Murtala na taho kuma zan je asibitin Ƴankura domin duba ƴaruwata. Kuma idan na je haka zan koma," in ji wani dattijo da aka gano shi yana tafiya a ƙasa yana sharɓa gumi.

Dattijon ya ce tafiyar a ƙasa ta zama dole ne sakamakon tsadar man da kuma rashin kuɗin da zai biya sufurin da ya yi tsada.

"A yanzun nan inda nake son na je sai na biya naira 500. Kuma idan ba ka da kuɗin fa? To ai dole ka hakura," in ji dattijon.

Yaushe farashin mai zai yi sauƙi a Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin da aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, farashin man fetur ya tashi daga ƙasa da naira 200 zuwa sama da naira 1,000 kan kowace lita, lamarin da ya haifar da ƙarin tsadar sufuri, abinci da sauran abubuwan rayuwa.

A baya dai, man fetur ya fara sauka a Najeriya har zuwa ƙasa da naira 1,200 a ƴan makonnin da suka gabata, lamarin da ya sa wasu suka fara hasashen cewa zai iya komawa ƙasa da naira 1,000 kan kowace lita, kamar yadda yake a farkon shekarar 2026.

A kullum fatan ƴan Najeriya dai shi ne su samun man fetur a ƙasar ya yi sauƙi sosai ta yadda za su saye shi a araha.

Sai dai Farfesa Ahmed Adamu, masanin tattalin arziƙin man fetur a Abuja ya ce a irin wannan lokaci ya kamata a daina maganar ya za a yi man fetur ɗin ya yi ƙasa.

Ya ce kamata ya yi a mayar da hankali ne wajen neman mafita ga ƙasar ta yadda ko an samu sauyi ƴan ƙasar ba za su gane ba.

"Ɗanyen man fetur idan ka ce ka ci gaba da dogaro a kanshi, zai ta baka wahala ne kawai. Dole sai an nemo mata wata madafa."

Me ya janyo tsadar man fetur?

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa sabon ƙarin farashin ya biyo bayan ƙarin naira 85 da matatar Dangote ta yi kan farashin man fetur da take sayarwa daga matatar, daga naira 1,265 zuwa naira 1,350 kan kowace lita, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

To sai dai a wasu jihohin rahotanni sun ce farashin litar man fetur ya haura naira 1,500.

Masana harkokin makamashi sun bayyana wasu dalilai guda huɗu da suka su ne manyan dalilan tashin farashin man fetur ɗin.

  • Farashin kasuwannin duniya: Farfesa Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Abuja, ya ce abin da ke sa farashin ya taɓu shi ne idan wani abu ya faru a ƙasar da ake shigowa da ɗanyen mai daga cikinta, wanda hakan ke sa farashin ya ƙaru.
  • Bambancin tattalin arziki: Akwai tattalin arzikin ƙasashen da yake da ƙarfi saboda suna fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, wanda ya sa darajar kuɗinsu take haɓaka idan ka kwatanta shi da dala. Ya ce irin waɗannan ƙasashe, ko da ɗanyen man ya yi tsada, idan aka canza farashin zuwa kuɗin ƙasarsu, ba lallai a samu wani babban sauyi ba.
  • Rashin darajar Naira: Rashin darajar naira na sa ko da an samu ƙaramin sauyi, darajar kuɗin ba za ta iya kare martabarta da dala ba, saboda komai da dala ake ƙirga shi a kasuwar duniya, sannan a canza shi zuwa kuɗin ƙasa. Darajar naira ba ta kai ƙarfin kuɗin wasu ƙasashe ba.
  • Rikicin ƙasashen duniya: A baya-bayan nan, rikici a Gabas ta Tsakiya na ƙara tsananta, inda Mashigin Hormuz yake kusan a kulle, sannan kuma akwai batun mayaƙan Houthi da suka kai hare-hare a Saudiyya.