Me bayyanar ɗan Osama Bin Laden a sabon bidiyon alqa'eda ke nufi?

.

Asalin hoton, AL-QAIDA

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƙungiyar Al-Qaeda ta fitar da wani bidiyo mai kama da shirin dokumentari mai tsawon minti 52 da daƙiƙa 36, domin tunawa da cika shekaru 25 da harin ranar 11 ga Satumban 2001 da aka kai wa Amurka.

Bidiyon ya kuma nuna Hamza bin Laden, ɗan tsohon jagoran Al-Qaeda Osama bin Laden, a wani bidiyo da ake ganin ba a taɓa ganinsa a bainar jama'a ba.

A wa'adinsa na farko a matsayin shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar a shekarar 2019 cewa an kashe Hamza bin Laden a wani samamen da Amurka ta kai.

Sai dai gwamnatin Amurka ba ta taɓa bayyana cikakkun bayanai kan lokacin da aka kashe shi, inda aka kashe shi ko kuma yanayin da aka kashe shi ba.

A sabon bidiyon farfagandar da Al-Qaeda ta fitar ya nuna Hamza bin Laden yana gabatar da saƙonni kai tsaye ga kyamara.

Lamarin ya sake tayar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu masu ra'ayin jihadi a kafafen intanet, inda wasu ke cewa watakila Hamza bin Laden na raye har yanzu.

Bidiyon mai tsawon minti 52 ɗin na ɗauke da taken: "Shekaru 25 Bayan Harin 11 ga Satumba."

An yaɗa shi ta kafafen Rocket Chat da Telegram, yayin da sashen yaɗa labarai na Al-Qaeda, wato Al-Sahab, ya shirya shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kashi na farko na bidiyon ya ƙare da rubutun cewa: "Za a ci gaba, idan Allah Ya so", lamarin da ke nuna cewa akwai yiwuwar a fitar da wasu ƙarin sassa na bidiyon nan gaba.

Bidiyon ya yi bayani dalla-dalla kan labarin da Al-Qaeda ta daɗe tana bayarwa game da tasirin harin 11 ga Satumba a kan Amurka da kuma harkar masu ra'ayin jihadi a duniya baki ɗaya.

Haka kuma bidiyon ya ƙunshi wasu tsoffin bidiyoyi da saƙonnin da aka riga aka naɗa na wasu daga cikin manyan jagororin Al-Qaeda na baya, ciki har da Osama bin Laden da Ayman al-Zawahiri.

Kamar yadda aka saba gani a wasu bidiyoyin dokumentari da Al-Qaeda ta fitar a baya, bidiyon da aka fitar a ranar 10 ga Satumban 2026 ya yi amfani da wasu kalamai da jami'an gwamnati da na ƙasashen Yamma suka yi, ta hanyar da aka zaɓa domin ƙarfafa ikirarin ƙungiyar cewa tana da wani nau'in goyon baya daga wajen ƙungiyar.

Musamman ma, bidiyon ya ba da muhimmiyar wajen ga Michael Scheuer, tsohon jami'in Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA) wanda ya jagoranci sashen da ke bibiyar da kuma farautar Osama bin Laden.

Wannan bidiyon farfaganda ya yi iƙirarin cewa tun bayan harin 11 ga Satumba, an samu manyan sauye-sauye a cikin Amurka, tare da yaɗuwar ƙungiyoyin masu ra'ayin jihadi zuwa sassa daban-daban na duniya.

Osama Bin Laden

Asalin hoton, Getty Images

Abin da ya sa ba a ga hotunan Hamza bin Laden ba

A cewar masana da ke sa ido kan ayyukan ƙungiyoyin masu ra'ayin jihadi, abin da ya fi ɗaukar hankali a sabon bidiyon da Al-Qaeda ta fitar shi ne bayyanar Hamza bin Laden.

Amurka ta sanar a shekarar 2019 cewa ta kashe Hamza bin Laden a wani samamen yaƙi da ta'addanci da aka kai a yankin kan iyakar Afghanistan da Pakistan.

Sai dai a lokacin da kuma a shekarun da suka biyo baya, Washington ba ta bayyana cikakkun bayanai kan lokacin ko wurin da ya mutu ba.

A baya, Al-Qaeda ta taɓa fitar da wasu saƙonnin murya na Hamza bin Laden, tare da nuna shi na ɗan gajeren lokaci a wasu bidiyoyi na tarurrukan masu jihadi da kuma wajen aurensa.

Sai dai wannan sabon shirin dokumentarin ne karo na farko da aka ga Hamza bin Laden, ko kuma mutumin da aka bayyana a matsayin Hamza bin Laden, yana gabatar da saƙo kai tsaye a gaban kyamara.

An nuna wannan yanayin a wurare uku daban-daban a cikin bidiyon, waɗanda dukkaninsu ke nuna kamar an ɗauke su ne daga rikodin guda.

Abubuwan da ya faɗa a bidiyon sun fi ƙunsar bayanai da iƙirari da kuma kiraye-kirayen da suka shafi aƙidar masu jihadi.

Sai dai babu wasu takamaiman abubuwan da suka faru da ya ambata waɗanda za su taimaka wajen gano lokacin da aka naɗi saƙonnin.

Saboda haka, ba za a iya tabbatar da lokacin da aka naɗi waɗannan saƙonnin ba, ko kuma ko Al-Qaeda na ɗaukar Hamza bin Laden a matsayin mai rai ko mamaci.

Wani ɓangare na bidiyon ya haɗa kalaman Hamza bin Laden da hotuna da bidiyoyin wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023 da kuma sake karɓar mulki da Taliban ta yi a Afghanistan a watan Agustan 2021.

Kodayake Hamza bin Laden bai ambaci waɗannan abubuwan kai tsaye a cikin jawabinsa ba, yadda aka shirya bidiyon na iya sa masu kallo su yi tunanin cewa an naɗi saƙonsa ne kwanan nan, watakila ma bayan sanarwar da Amurka ta yi a shekarar 2019 cewa an kashe shi.

Haka kuma, abin lura shi ne an ambaci shi ne kawai da sunan "Mujahid Sheikh Hamza bin Laden".

Ba a yi amfani da kalaman da aka saba furtawa a tsakanin masu ra'ayin jihadi ba, irin su "Allah Ya kiyaye shi" idan mutum yana raye, ko kuma "Allah Ya jiƙan sa" idan mutum ya rasu.

A cewar masu sa ido kan harkokin ƙungiyoyin masu jihadi, wannan rashin fito-na-fito kan matsayinsa na iya kasancewa da gangan.

Irin wannan ruɗani ya taɓa kewaye tsohon jagoran Al-Qaeda Ayman al-Zawahiri, wanda Amurka ta ce an kashe shi a wani harin jirgin sama maras matuƙi a birnin Kabul a watan Yulin 2022.

Ko a wuraren da bidiyon ya ambaci al-Zawahiri, ba a bayyana a sarari ko yana raye ko ya mutu ba.

Duk da cewa Al-Qaeda ba ta taɓa fitar da sanarwa a hukumance game da al-Zawahiri bayan ikirarin Amurka ba, magoya bayan ƙungiyar sun daɗe suna ɗaukarsa a matsayin mamaci.

Bidiyon bai kuma bayar da cikakken haske kan matsayin Saif al-Adl, wanda ake kallon sa a matsayin wanda zai iya zama jagoran Al-Qaeda na yanzu ba.

An ambace shi ne kawai da lakabin "Sheikh", tare da kawo wasu kalamai daga rubuce-rubucensa na baya.

Amma bidiyon bai bayyana shi a matsayin jagoran ƙungiyar ba, kuma bai bayar da wani bayani kan inda yake a halin yanzu ba.

Bayyanar Hamza bin Laden ta jawo hankalin masana harkokin tsaro da masu nazari, inda wasu daga cikinsu ke ganin hakan a matsayin wata alama da za ta iya nuna cewa Hamza bin Laden na raye har yanzu.

Hamza bin Laden

Asalin hoton, CIA

Wasu masu sa ido sun yi nuni da cewa a hoton Hamza bin Laden yana sanye da farin rawani, yayin da ake ganin bangon laka a bayansa, irin wanda ya yi kama da hotunan da a baya ake dangantawa da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke aiki a Afghanistan.

Sun ce akwai yiwuwar yana Afghanistan ne a lokacin da aka ɗauki saƙon.

A gefe guda kuma, ƙungiyoyi da ke goyon bayan aƙidar jihadi ba su nuna wani gagarumin martani kan bayyanar Hamza bin Laden ba, a cewar mutanen da ke da masaniya kan lamarin.

Sun ƙara da cewa hakan na iya kasancewa saboda raguwar yawan magoya bayan ƙungiyar Al-Qaeda da ke da tasiri a shafukan yanar gizo a cikin kusan shekaru biyu da suka gabata.

Shahararren mai sharhi kan harkokin ƙungiyoyin jihadi, Hamid al-Qawsi, wanda ke bayyana kansa a matsayin mai bincike amma wasu ke kallonsa a matsayin mai karkata ga Al-Qaeda, shi ma ya yi magana kan bayyanar Hamza bin Laden da Ayman al-Zawahiri.

Ya ce daga bidiyon ba a iya tabbatar da ko mutanen biyu suna raye ko kuma sun mutu ba.

Ya yi nuni da cewa ba a ambaci sunayen mutanen biyu cikin kalmomin addu'ar da ake yawan amfani da su domin bayyana ko mutum yana raye ko ya rasu ba.

A cewarsa, hakan na nuna cewa an tsara bidiyon ne da nufin barin matsayin mutanen biyu cikin ruɗani, ba tare da fayyace ko suna raye ko sun mutu ba.