BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Gaske ne Opay zai dakatar da aiki a watan Satumba?
A ranar 30 zuwa 31 ga Agustan 2026, wani saƙo na bogi ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana cewa OPay zai dakatar da harkokinsa daga ranar 1 ga watan Satumban 2026, kuma ya buƙaci kwastomomi su cire kuɗaɗensu.
KAI TSAYE, Iran ta ce ta kai hari kan sojojin Amurka a Jordan
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 31 ga watan Agustan 2026.
Ina ne tsibirin Larak na Iran da Amurka ta kai wa hari?
Wannan shi ne harin farko da Amurka ta kai wa Iran tun bayan ƙarshen watan Yuli. Rundunar IRGC ta Iran ta ce harin ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu biyun, kuma ta yi alƙawarin mayar da martani da hukunta masu kai harin.
Matan da za su yi takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027
Da farko, mata uku ne suka bayyana a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyunsu daban-daban.
Waziri Allah Bar Sarki: Mutumin da ya mulki Kano shi ba sarki ba
A tarihin masarautar Kano akwai sunaye da dama da suka yi fice saboda rawar da suka taka a harkokin mulki, siyasa da gudanar da masarauta sai dai lamarin Allah Bar Sarki ya zo da wani salo.
Hanyar da za ku bi idan kuna son daina shan taba sigari
Wani sabon bincike ya nuna cewa masu shan sigari da ke son dainawa suna da damar yin hakan idan suna amfani da wata na'urar shan sigari ta laturoni da aka fi sani da vape, a turance
Me ya sa wasu sojoji suka yi bore a Nijar?
Boren da wasu sojojin Nijar suka yi ya kasance wata sabuwar barazana ga mulkin Abdourahamane Tiani, wanda ya kwace iko a juyin mulkin shekarar 2023.
Lalurar jego: Ana tuhumar uwa da kashe ƙananan ƴaƴanta uku
A wata shari'a da ta ɗauki hankali, matar ba ta musanta cewa ita ce ta kashe yaran nata ba, amma lauyoyinta suna cewa bai kamata a ɗora mata alhaki ba.
Karin kumallo ko abincin dare: Wanne ya fi amfani ga lafiyar jiki?
Tawagar masu bincike daga Jami'ar Aberdeen ta gano cewa mutanen da suka rage yawan kuzarin abinci (kalori) da suke ci sun kasance suna samun adadin kalori iri ɗaya a duk lokacin da suka ci mafi yawan abincinsu na ranar.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Rana, 13:59, 31 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 31 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 31 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 30 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
Tottenham na son Pulisic, Everton za ta sake karɓar aron Grealish
Hankalin Spurs ya koma kan Christian Pulisic, Liverpool da Everton sun nuna suna son ɗanwasan Stuttgart Jamie Leweling, yayin da Crystal Palace ta nuna ba ta son rabuwa da Dean Henderson duk da Nottingham Forest na so.
Aston Villa ta taya Amad, Arsenal na nazari kan Fernandez-Pardo
Napoli na tuna tana son ɗanwasan gaba na Newcastle Nick Woltemade, Sundaland na son ɗanwasan Manchester City Jack Grealish yayin da Arsenal ke nazari kan ɗanwasan gaba na Lille Matias Fernandez-Pardo.
Arsenal na sa ido kan Rashford, Alvarez ba ya son komawa Man City
Arsenal na sa ido kan Marcus Rashford, Chelsea ma na sa ido kan ɗanwasan Monaco Lamine Camara yayin da Valencia ke farautar ɗanwasan tsakiya na Liverpool Harvey Elliott.
Waɗanne ƴanƙwallo ƙungiyoyinku ke buƙata kafin rufe kasuwar ƴanwasa?
Arsenal har yanzu tana kasuwa tana neman ɗan gaba, kuma ta daɗe tana nuna sha'awar Julian Alvarez.
Baleba da Diallo ba za su buga mana wasa ba - Carrick
Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Mata 6 da suka taka rawa wajen ciyar da arewacin Najeriya gaba
Wasu sun yi amfani da ilimi, wasu suka yi amfani da siyasa, wasu suka yi amfani da aikin jarida, yayin da wasu suka shiga fannonin likitanci da gwamnati.
Yadda minti 20 na shakatawa zai iya inganta lafiyarku
Yin minti 20 kacal a yanayi na iya rage hawan jini, bugun zuciya da kuma matakan damuwa.
Amurka da Isra'ila maƙiya Musulunci ne - Mojtaba Khamenei
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 30 ga watan Agustan 2026.
An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar - Gwamnati
A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce da misalin ƙarfe 12:20 na dare wasu sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
Nepal: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a ƙauyuka
Hotunan gidaje da gadoji da kuma wata babbar hanya a iyakar Nepal da Tibet waɗanda ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su.
Da gaske kurkur na ɗauke da sinadaran da ke inganta lafiya?
Ɗaya daga cikin kayan ƙanshi da aka fi so yana ko'ina a Kudancin Asiya inda akwai imani mai zurfi cewa yana da maganin kashe ƙwayoyin cuta da kuma maganin kumburi.
Hanyoyi 6 da ƴanbindiga ke kashe kuɗaɗen da suke karɓa
Wani rahoto ya yi ƙiyasin cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi kimanin dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa tsakanin watan Yulin 2025 da Yulin 2026.
Me ya sa yaƙin Iran ya zama matsala ga Trump a zaɓe?
Nasarar yaƙin tattalin arzikin Amurka da Iran ta dogara ne kan ainihin haɗin gwiwar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, China, India, Turkiyya da sauran ƙasashen da ke hulɗa da Iran.
Za mu kai hari kan dukkan wuraren Amurka idan yaƙi ya ci gaba - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 29 ga watan Agustan 2026.
Barazana 5 da duniya ke fuskanta a 2026 da yadda hakan zai shafi Afirka
Rashin tabbas na ƙara yin ƙamari a tsakiyar yanayin duniya, a cewar rahoton da ke bayani kan barazanar da duniya ke fuskanta na 2026 na taron ƙolin tattalin arziƙi na duniya wanda aka wallafa a ranar 14 ga Janairu, 2026.
Matsalar tsaro: Buƙatu biyu da ƴanmajalisar Najeriya suka miƙa wa Tinubu
'Ziyartar Tinubu zuwa jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar tsaro zai taimaka wajen magance matsalar'
Illar da Iran ta yi wa harkokin leƙen asirin Amurka da ba a sani ba - NBC
A ranar farko ta wata na shida na yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran, jaridar Wall Street Journal ta ba da rahoton cewa jami'an leƙen asiri da na soja da dama sun yi gargaɗi ga Shugaban Amurka Donald Trump kafin fara yaƙin, amma ya yi watsi da su.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































