'Yadda abokaina suka mutu a gabana a hannun jami'an Civil Defence'

Niger

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ana cigaba da tafka muhawara kan mutuwar aƙalla mutum 37, waɗanda mafi yawansu matasa a hannun jami'an hukumar tsaro ta farin kaya wato Civil Defence a jihar Neja.

A daidai lokacin da ake cigaba da muhawara kan musabbabin lamarin, mahaifin ɗaya daga cikin mutanen ya shaida wa BBC cewa ɗansa Salim ya ba shi labarin abin da ya faru a lokacin da suke tsare a wajen jami'an tsaron.

A cewarsa, lokacin da ake ruwan sama ne zafi da ƙishin ruwa suka dame su, lamarin da ya sa suka shiga wani ƙaramin ɗaki mai taga domin samun iska.

"Na ga mutuwar abokaina na ɗauka ni ma zan mutu"

Mahaifin shaida wa BBC cewa ɗan nasa ya bayyana masa cewa an tara su ne a cikin wani ɗakin tsare mutane tare da abokansa.

Ya ce a lokacin ana ruwa ne, suna kuma cikin zafi da ƙishin ruwa, "sai yake cewa, 'Salim, zan mutu, ina jin ƙishin ruwa. Ka taimaka min da ruwa.'"

Mahaifin ya ce yayin da suke cikin haka ne ɗayan yaron ya faɗi ya fara harbe-harbe.

A cewarsa, a lokacin ne sauran yaran da ke cikin ɗakin suka fara buga ƙofa suna neman a taimaka musu da ruwa kuma a buɗe musu ƙofar, "amma babu wanda ya saurare su."

Ya ce haka suka kasance har zuwa safiya, lokacin da aka buɗe sai aka gano cewa wasu daga cikinsu sun mutu.

Mahaifin ya ce ɗansa ya koma gida kuma yana cikin ƙoshin, kuma yana tunanin cewa matasan ba su shiga wuraren da aka hana haƙar ma'adanai ba.

"Mu dai ba mu da ƙarfin ɗaukar mataki, muna addu'a ga Allah saboda ba mu da ƙarfi," in ji shi.

Jihar Neja na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, ciki har da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa.

'Ɗana ba ɓarawo ba ne'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Iyayen waɗanda abin ya shafa suna cigaba da bayyana yadda suka ji, tare da bayyana alhininsu kan yadda aka gudanar da kame da tsare ƴaƴansu, har wasu suka rasu.

Mahaifin Salim ya ce ya kai ziyara wajen da ake tsare da su bayan sun samu labari, amma aka ce ba za a sake su ba tukuna.

"Ranar farko mun je, aka faɗa mana cewa mu dawo washegari. Da muka koma aka faɗa mana ba za a sake su, sai washegari. A ranar kuma matata ce ta riga ni komawa, sai ta kira ta ce yara fa sun mutu."

Mahaifin ya ce hakan ya sa ya ruga zuwa ofishin hukumar domin su gane wa kansu abin da ke faruwa, amma aka hana shi shiga.

Sai daga baya, lokacin da aka saki gawarwakin, ya je domin duba gawar ɗansa, amma bai same shi ba.

Ya ce daga baya ne ya gano cewa ɗansa, Salim, yana raye kuma ya koma gida.

Shi ma wani mahaifi da yaransa ya rasu mai suna da Malam Abdullahi da zanta da jaridar Daily Trust, ya ce da ya je hedkwatar hukumar, an buƙaci ya biya naira 500,000 ne a matsayin kuɗin beli kafin a saki ɗan nasa.

Ya bayyana cewa ɗansa ba ɓarawo ba ne, kuma yana aikin haƙar zinare ne saboda babu wani aikin da zai yi.

"Kuma da ɗan abin da yake samu ne yake taimakonmu a gida. Ko a daren jiya mun kai masa abinci a wajen da ake tsare su. Da safiyar yau muka je kai masa abinci kawai muka samu labarin ya mutu."

Halin da ake ciki a Neja

Rahotanni sun nuna cewa zanga-zanga ce ta ɓarke a jihar, inda matasa suka fito suna nuna rashin jin daɗinsu kan mutuwar matasan.

Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda lamarin ya faru, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.

A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasan.

Lamarin ya sa gwamna Mohammed Umar Bago ayyana makokin kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.

Tuni kuma gwamnatin tarayya ta hannun ministan cikin gida ta sanar da dakatar da shugaban hukumar Civil Defence din wato NSCDC.