Monaco ta shirya sayar da Balogun, Liverpool na sanya ido kan Kees Smit

Folarin Balogun

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Monaco ta tabbatar da shirin sayar da ɗan wasan gaban Amurka Folarin Balogun a watan Janairu, bayan da ɗan wasan mai shekara 25 ya sauya ra'ayinsa game da komawa ƙungiyar Everton a ranar da aka rufe kasuwar musayar ƴan wasa ta bazara. (Standard)

Liverpool ta sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Netherlands, Kees Smit—wanda darajarsa ta kai fam miliyan 51.5—a lokacin da ƙungiyarsa ta AZ Alkmaar ta kara da Sunderland a gasar Europa League a wannan makon; sauran ƙungiyoyin da ke bibiyar dan wasan mai shekara 20 sun haɗa da Chelsea da Tottenham da Nottingham Forest da Aston Villa. (Teamtalk)

Tottenham ce ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan baya na Brazil mai shekarua 19, Arthur Dias, daga ƙungiyar Athletico Paranaense, yayin da Newcastle United, da Nottingham Forest da Brentford suma ke bibiyar ɗan wasan, wanda darajarsa ta kai Yuro miliyan 30. (Teamtalk)

Manchester United na nazari kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan baya na Everton da Ingila, Jarrad Branthwaite mai shekara 24. (Football Insider)

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama na sa ido kan yanayin ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 20, Josh Acheampong, a ƙungiyar Chelsea. (AS)

Ƙungiyar Monaco ta amince cewa akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar cefanar da ɗan wasan tsakiya Lamine Camara mai shekara 22, a watan Janairu, yayin da ƙungiyoyin Liverpool da Chelsea ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan na Senegal. (Standard)

Real Madrid za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ɗaukar sabon hazikin ɗan wasan tsakiya na Morocco, Abdellah Ouazane mai shekara 17, wanda ke buga wa Ajax wasa. (Fichajes)

Newcastle United na shirin sake nuna sha'awarta ta ɗaukar ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Djurgarden, Bo Hegland, bayan da ɗan wasan na Norway mai shekara 22 ya ƙi amincewa da komawa ƙungiyar a lokacin bazara. (Football Insider)

Arsenal da Brighton da Aston Villa duk suna sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Sturm Graz, Luca Weinhandl, mai shekara 17, wanda ake kimanta darajarsa kan fam miliyan 20. (Teamtalk)

Tottenham na duba yiwuwar ɗaukar Mauro Icardi, wanda ba shi da ƙungiya a yanzu, bayan ɗan ƙasar Argentinan ya bar Galatasaray; sai dai ba za ta iya rajistar ɗan wasan mai shekara 33 ba har sai watan Janairu. (Express)

Manchester City da Liverpool na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Jamus, Felix Nmecha, mai shekara 25, inda ake sa ran ƙungiyarsa ta Borussia Dortmund za ta nemi kuɗin da ya kai tsakanin Yuro miliyan 80 zuwa 90. (Fussball News)

Chelsea ta shiga jerin ƙungiyoyin Turai da ke zawarcin matashin ɗan wasan Gambia, Adama Jeng, mai shekara 15, daga ƙungiyar Tromso IL ta Norway. (Football Insider)