Waɗanne makamai ne Amurka ta girke a sararin samaniya?

Asalin hoton, Thomas Traasdahl/Ritzau Scanpix/AFP via Getty Images
- Marubuci, Bernd Debusmann Jr
- Marubuci, Chris Graham
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Amurka ta tabbatar cewa ta aika da makamai zuwa sararin samaniyar duniya, wani mataki da ke nuna, a karon farko ƙasar ta amince a hukumance cewa tana da makaman da za su iya kai hari a sassan duniya daga sararin samaniya.
Sakataren rundunar sojin sama ta Amurka, Troy Meink, ya ce makaman, wanda ke kewaya duniya a sararin samaniya, suna da muhimmanci wajen bayar da tsaro ga dakarun Amurka, daga barazanar hare-haren abokan gaba.
Da yake jawabi a wajen wani taro na musamman kan harkokin sararin samaniya, Meink ya ce Amurka a shirye take ta tunkari "barazanar da ke ci gaba da sauyawa", amma bai yi ƙarin bayani game da irin ƙarfin makaman ko lokacin da aka tura su zuwa sararin samaniya ba.
A baya dai manyan jami'an sojin Amurka sun sanar da shirye-shiryen faɗaɗa ƙarfin sojin ƙasar a sararin samaniya, inda suka kafa hujja da shirye-shiryen da Rasha da kuma China ke yi na samar da hanyoyin kai hari ko kawo cikas ga tauraron ɗan'adam na Amurka idan yaƙi ya ɓarke a nan gaba.
China ta yi gargaɗi kan rige-rigen jibge makamai a samaniya
China ta soki wannan mataki tare da yin gargaɗi game da samar da yanayi na "rige-rigen jibge makamai a sararin samaniya". Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya ce ya kamata Amurka ta daina faɗaɗa ƙarfin sojanta da shirye-shiryen yaƙi a sararin samaniya.
Sai dai har yanzu hukumomin Amurka ba su fayyace yadda makaman ke aiki ba.
Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Amurka ya ce ƙara ƙarfin sarrafa sararin samaniyan nasu ya mayar da hankali ne kan yadda ƙasar za ta iya yin gogayya da sauran ƙasashen duniya tare da kare kanta daga duk wata barazana.
Bleddyn Bowen, wani masani kan amfani da sararin samaniya wajen ƙara ƙarfin soja, ya ce akwai ƙarancin bayanai a game da yadda ake amfani da irin wannan fasahar ta tsaro.
Ya ce makaman na iya kasancewa iri daban-daban, ciki har da tsarin amfani da lantarki ko wata na'ura mai iya kawo cikas ga tsarin sadarwa ta rediyo.
A cewar Bowen, wani abu da zai iya yiwuwa kuma shi ne makaman na iya lalata na'urar tauraron ɗan Adam cikin sauri.
Sai dai ya ce irin wannan makami ba shi da tabbas, domin yana iya haifar da ɗimbin tarkacen ƙarafa da kayan aiki da za su ci gaba da zama barazana ga duniya, lamarin da zai iya jefa sauran tauraron ɗan adam cikin haɗari.
Makamai a sararin samaniya da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ce ƙarfin tsaron sararin samaniya, ciki har da makaman kariya masu kakkabo makamai masu linzami, wani muhimmin ɓangare ne na tsarin kariya na Golden Dome, wanda ke kare Amurka daga makamai masu linzami da sauran barazanar da ke zuwa ta sama.
Yarjejeniyar shekara ta 1967 ta haramta girke makaman hallaka jama'a a sararin samaniyar da ke kewaye da Duniya.
Sai dai tun daga lokacin, ƙasashe masu ƙarfin soja ciki har da Amurka da Rasha da kuma China sun ci gaba da bunƙasa ƙarfin sojansu a sararin samaniya a fannonin da yarjejeniyar ba ta haramta ba.
Daga cikin ƙarfin da suke da shi kuwa akwai kai hari kan tauraron ɗan adam na abokan gaba, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci ga sadarwar soja da sanya ido.
A bara, Shugaba Trump ya sanya hannu kan wani umarnin shugaban ƙasa da ya jaddada rawar da rundunar sararin samaniya ta Amurka ke takawa a wajen kare kadarorin Amurka a sararin samaniya da kuma shirin kai farmaki.
An kafa Rundunar Sararin Samaniya ta Amurka a shekarar 2019, kuma ita ce sabuwar reshen rundunar sojin Amurka cikin sama da shekara 70.
An kafa ta ne domin kare kadarorin Amurka a sararin samaniya, ciki har da ɗaruruwan tauraron ɗan adam da ake amfani da su wajen sadarwa da sintiri.
Rasha da China
A farkon watan Fabrairu, an ba da rahoton cewa tauraron ɗan adam biyu na Rasha sun daƙile hanyar sadarwa daga aƙalla na'urar tauraron ɗan adam na ƙasashen Turai 12, tun bayan kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine a 2022.
Wannan tsarin leƙen asiri ne da zai iya bai wa jami'an leƙen asirin Rasha damar karanta muhimman bayanan sirri da ake aikawa ta tauraron ɗan adam da kuma karkatar da su.
A 2024, Amurka ta yi iƙirarin cewa Rasha ta harba wani tauraron dan'adam zuwa sararin samaniya wanda Amurka ta yi imanin cewa yana da ikon kai hari kan sauran tauraron dan'adam.
Rasha ba ta fito fili ta yi wani bayani a kan wannan iƙirari ba.
Rundunar sojin saman Amurka ta ce China na girke sojoji a sararin samaniya kuma wani ɓangare ne na dabarun da take na zamanantar da sojojinta.
Har ila yau ta ce Rasha na kallon sararin samaniya a matsayin filin yaƙi kuma tana da imanin cewa ikon sarrafa sararin samaniya zai kasance mai matuƙar muhimmanci a yaƙin zamani a nan gaba.











