Me ya sa shirin Amurka na sayar wa Saudiyya jiragen yaƙi ke janyo taƙaddama?

 Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump da Yarima Mohammed bin Salman a fadar White House
    • Marubuci, Tom Bateman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Weriyaha Waaxda Gobolka
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin shugaba Donald Trump ta amince da saidawa ƙasar Saudiyya kusan jiragen yaƙi 50 samfurin 50 F-35, a wani mataki da ya ɗarsa damuwa a zukatan wasu ƴa majalisar Amurka.

Shekara da shekaru Saudiyya na fatan sayan jiragen yaƙin masu fasahar zamani a duniya da zai ba su damar mamayar abokan gaba ba tare da sun shirya ba, kuma da wuya a kakkaɓo su.

A baya Washington ta sha sukar wannan shiri, saboda ƙasar na samar da jiragen yaƙin ga babbar aminiyarta Isra'ila, kuma ƙarkashin dokokin Amurka ƙasar na da ikon mallakar kowanne irin makami da ta ƙera, ba kamar sauran ƙasashen yankin gabas ta tsakiya ba.

Ƴan mahalkisar Amurka su na da ƙwanaki 30 su gudanar da bincike ko su dakatar da cinikin makaman na dala Biliyan 24, ciniki mafi girma da wata kasa ta yi na sayan makaman Amurka.

F-35

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin sojin saman Amurka samfurin F-35 aircraft

A ranar Alhamis ɗan majalisa mai wakiltar jihar Illinois kuma ɗan jam'iyyar Democrat, Raja Krishnamoorthi, ya soki saidawa Saudiyyar Makamai.

Ya yi gargaɗin "Wannan zai zama saida makamin Amurka mai dauke da kimiyya da fasaha da ka iya faɗawa hannun gwamnatin China".

Su ma wasu ƴan jam'iyyar Democraticda wasu jami'an ma'aikatar tsaron ƙasar sun nuna damuwa kan cikin jiragen ƴakin tsakanin Amurka da Saudiyya.

Sun ce Riyadh ka iya bai wa China damar sanin wasu muhimman abubuwa fasaha, sakamakon yadda ƙasashen biyu ke da alaƙar tsaro.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar Alhamis ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu, tare da cewa wannan zai ƙara yauƙaƙa manufofin Amurka na ƙasashen wanda batun tsaro na daga ciki.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce: 'Yarjejeniyar za ta ƙara matakan tsaro a ƙasashe aminan ƙungiyar tsaro ta NATO, wata ƙungiya da ke taimakawa da wanzar da zaman lafiya da siyasa da ci gaban yankin Gulf.'

Shugaba Trump na da kyakkayawar alaƙa da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad bin Salman, wanda ya kai ziyara fadar White House a watan Nuwambar 2025.

Mutanen biyu sun kuma gana a birnin Riyadh duk dai a shekarar da ta wuce, inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sayen makamai ta dala biliyan 142, da fadar White House ta irinta ta farko ta sayen makamai a tarihi.

Sabuwar bukatar Saudiyya na sayen makaman sun hada da jirgin yaki samfurin 7-35, wanda kamfanin ƙera makamai na Lockheed Martin.

Wannan zai bai wa Saudiyya damar mallakar jiragen yaki shigen waɗanda a halin yanzu Isra'ila ta ke da kusan 50.

HarwayauS ai dai a watan Mayu da ya wuce, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta sanar da sake sayen wasu jiragen yakin samfurin F-35, hakan zai sa wadanda ta ke da su ya ruɓanya sau biyu, ma'ana mallakar jiragen yakin 100, kamar yadda kafar yaɗa labaran Jerusalem Post ta wallafa.

Kamfanin Lockheel Martin na saida jirgin yaƙi ɗaya kan farashin dala miliyan 82.5.

ƴan majalisar Amurka sun ƙara nuna damuwa da ɗisa ayar tambaya kan cinikin makaman da Saudiyya, musamman kan kisan ɗan jaridar kasar Jamal Khashiggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Santambul na kasar Turkiyya a shekarar 2018.

Gwamnatin tsohon shugaban Amurka Joe Biden, na duba yiwuwar saidawa Saudiyya jiragen yaƙin amma idan za ta daidaita alaƙa tsakaninra da Isra'ila, to amma wannan yunƙurin diflomasiyyar ya gaza.

Buƙatar sayen makaman na zuwa ne a daidai lokacin da yaki tsakanin Saudiyya da ƴan tawayen Houthi na Yemen da Iran ke marawa baya ke ƙara tsananta inda Houthi ke iko da gabashin kasar.

A baya-bayan nan ƴan tawayen sun karbe ikon gaɓar tekun maliya, wanda a baya ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Yemen da Saudiyya da kasashen waje ke marawa baya.

Wasu majiyoyi biyu da suka san yadda lamura ke gudana, sun shaidawa kafar yaɗa labaran CBS ta Amuka kuma abokiyar Hulɗar BBC, cewa Yarima Muhammad bin Salman ne ya matsawa shugaba Trump lamba kan ɗaukar matakin soji ga ƴan tawayen Houthi.

Sai dai majiyar ta ce, a baya-bayan nan shugaba Trump ya ki amincewa shigar da sojojin ƙasar kai tsaye a yaƙin.