Me ya sa EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun?

Govnor Ademola Adeleke and Oluwakuyode Olukoyede

Asalin hoton, Ademola Adeleke/X, EFCC/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Jihar Osun ta fara ɗaukar matakin shari'a kan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC bayan hukumar ta rufe asusun bankin gwamnatin jihar, kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna na jihar.

Gwamnan jihar, Ademola Adeleke, ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa, inda ya ce a safiyar Laraba bankinsu ya aika musu da wasiƙar EFCC da ke umartar a rufe asusun gwamnatin jihar.

EFCC ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne domin hana zargin karkatar da kuɗaɗen jama'a. Hukumar ta ce tun daga watan Maris 2026 take binciken gwamnatin jihar kan zargin almundahanar kuɗi da suka kai Naira biliyan 11, waɗanda suka haɗa da kuɗaɗen tallafi da na kyautata muhalli da kuma kuɗaɗen ɗauni daga gwamnatin tarayya.

Hukumar ta kuma ce ta yi tambayoyi ga wasu jami'an gwamnatin jihar, musamman Akanta Janar na jihar, a matsayin wani ɓangare na binciken da take yi.

A martaninsa, Gwamna Adeleke ya yi tambaya kan sahihancin matakin na EFCC, yana mai kira ga shugaban hukumar, Ola Olukoyede, da ya bayyana wa al'ummar Osun da 'yan Najeriya dalilin da ya sa aka rufe asusun gwamnatin jihar tare da gabatar da hujjoji.

Ya kuma ce ya umarci Babban Lauyan Jihar da ya ƙalubalanci matakin a gaban Kotun Tarayya da ke Osogbo.

Gwamnan ya ce wannan na daga cikin jerin matsalolin da jihar ke fuskanta kafin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026, ciki har da hare-haren bindiga, tangarda ga tsarin ƙananan hukumomi da kuma kama mambobin.

Dalilin da ya sa muka rufe asusun Jihar Osun" - EFCC

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba cewa tun daga watan Maris na shekarar 2026 take gudanar da bincike kan gwamnatin Jihar Osun bisa zargin almundahanar kuɗi har Naira biliyan 11.

"Hukumar tana gudanar da bincike kan gwamnatin Jihar Osun tun daga watan Maris na 2026 kan zargin karkatar da kuɗaɗen Asusun Muhalli (Ecology Funds), Asusun Tallafi (Intervention Funds) da kuma kuɗaɗen rabon tarayya na FAAC, waɗanda adadinsu ya kai Naira biliyan 11," in ji EFCC.

Sun ƙara da cewa wasu jami'an gwamnatin jihar, musamman Akanta Janar na jihar, sun riga sun amsa gayyata tare da ba masu binciken hukumar bayanai a yayin gudanar da bincikensu.

Me ya janyo kiki-kaka?

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke wanda ɗan jam'iyyar Accord Party ne ya sha fadin cewa gwamnatin tarayya na yi masa bi-ta-da-ƙulli na siyasa domin ganin jam'iyyar tasa ba ta kai labari ba a zaɓen gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga watan Agusta.

Ademola Adeleke dai ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun na shekarar 2022 ne a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, amma daga bisani a watan Disambar 2025 ya fice daga PDP, inda ya koma Jam'iyyar Accord domin sake tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2026.

Gwamnatin Osun ta yi zargin hare-haren ƴansanda kan wasu jami'an gwamnatin jihar, inda suka nemi kwamishinan ƴansandan jihar da ya yi cikakken bincike dangane da zargin hare-haren da ake kai wa jami'an nasu.

Tarihin rikici a zaɓen jihar Osun

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kusan za a iya cewa jihar Osun na daga cikin jihohin da zaɓensu kan zo da sarƙaƙiya da rikice-rikice kasancewar jiha ce da a mafi yawancin lokuta na da banbancin jam'iyya da gwamnatin tarayya.

Hakan ne ake ganin ke rura wutar rikici musamman a ƙoƙarin gwamnatin tarayya na sauya akalar siyasar jihar zuwa jam'iyya mai mulki ta ƙasa, wani abu da ke janyo rikici ba ƙarami ba.

Ko a zaɓen 2022 sai da aka rikicin da ya janyo rasa rayukan al'ummar jihar.

Rikicin dai ya taso ne sakamakon wani hukuncin kotun ƙoli wanda ya mayar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin jihar Osun ɗin na jam'iyyar APC da aka cire a 2022.

Jam'iyyar APC ta ce hukuncin kai tsaye ya mayar da shugabannin ƙananan hukumomin, to amma gwamnatin jihar wadda ta jam'iyyar PDP ce ta musanta cewa hukuncin ya dawo da mutanen da aka cire a 2022.

Bisa dogaro da wannan hukunci ne ya sa jam'iyyar ta APC mai hamayya a jihar ta ɗauki matakin yin amfani da ƙarfi wajen karɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomin da abin ya shafa, al'amarin da ya janyo rikici tsakaninsu da magoya bayan jam'iyyar PDP da suka yi tirjiya.