Fa'ida 5 da Najeriya ke samu da tura dakarun zaman lafiya ƙasashen waje

Asalin hoton, NAF
A farkon makon nan ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da aika dakarun kasar 86 zuwa ƙasar Guinea Bissau domin aikin wanzar da zaman lafiya, ƙarƙashin kungiyar Ecowas.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da nata matsalolin tsaron a cikin gida.
Kan haka ne wasu yan ƙasar ke sukar matakin da cewa kasar ba ta gama da matsalolin tsaron ta na cikin gida ba, amma take tura wasu dakaru ketare.
Najeriya dai na daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi taka rawa wajen aika sojoji da jami'an tsaro zuwa ayyukan kiyaye zaman lafiya a wuraren da rikice-rikice suka daɗe suna addabar al'umma.
Ƙasar ta jima tana tura dakarunta zuwa ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen duniya daban-daban, ƙarƙashin shirye-shiryen Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka da kuma ECOWAS.
Masana harkokin tsaro sun ce baya ga gudunmawar da Najeriya ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya a duniya, ƙasar na kuma samun wasu fa'idojin daga wannan aiki.
Mene ne tarihin aikin kiyaye zaman lafiya?

Asalin hoton, NAF/X
Group Captain Sadiq Garba mai ritaya, tsohon sojin Najeriya, kuma mai sharhi kan al'amuran tsaron ƙasar ya ce aikin kiyaye zaman lafiya a duniya ya samo asali tun 1945 lokacin kafuwar Majalisar Dinkin Duniya, bayan Yaƙin Duniya na biyu.
Ya ce an fara aiwatar da wannan shiri ne domin ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashen duniya da ke fama da rikice-rikice.
Ya ci gaba da cewa tun bayan fara wannan aiki, aka samu hukumomi da ƙungiyoyin duniya da suke tura dakarun zaman lafiya zuwa ƙasashe ko yankunansu.
Wane aiki sojojin ke yi?

Asalin hoton, NAF/X
Tsohon jami'in sojin ya ce ayyukan da jami'an kiyaye zaman lafiya ke yi sun danganta da yanayin da ake ciki a kasar da aka tura su.
"A wasu lokutan suka shiga tsakani ne takanin ɓangarorin da ke fa da da juna'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa a wasu lokutan idan ana yaƙi ne tsaknain kadsashe biyu a kan mallakar wani wuri, jami'an kiyaye zaman lafiya kan ƙwace iko da wurin kafin a warware matsalar.
''A wasu lokutan kuma fa da ake yi tsakanin wasu ɓangarori a cikin kasa guda, to a nan sukan shiga tsakani ne su hana faɗan, su tabbatar babu ani ɓangare da ya tsallaka iyaka'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ƙara da cewa akwai ma yanayin da ake farmakar dakarun kiyayen zaman lgaiyar har ma a kashe wasu.
"Akwai ma dakarun Najeriya masu yawa da suka mutu sakamakon ayyukan kiyaye zaman lafiya da su ayi a wasu ƙasashe'', in ji shi.
Waɗanne fa'idojin Najeriya ke samu?

Asalin hoton, NAF/X
Captain Sadiq Garba mai ritaya ya ce Najeriya ta shiga ayyukan kiyayen zaman lafiya zuwa ƙasashe fiye da 50 a duniya.
Ya ce ƙasar ta yi hakan ne ƙarƙashin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Ecowas.
''Idan ka cire Indiya babu wata ƙasa da ta kai Najeriya yawan tura sojojinta zuwa ayyukan kiyaye zaman lafiya a duniya'', kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Ya kuma ce akwai wasu fa'idoji da dama da Najeriyar ke samu sakamakon wannan aiki na kiyaye zaman lafiya da suka haɗa da:
Samun kuɗi daga MDD
Tsohon babban jami'in sojin ya ce a ƙarƙashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya duk ƙasar da ta tura dakarunta shirin wanzar da zaman lafiya n aMDD, to majalisar na na biyanta kuɗi.
''Baga ga haka duk abin da kasa ta kashe ajen ɗaukar ɗawainiyar sojojin da ta tura aikin kiyaye zaman lafiya ƙarkashin MDD, to majalisar na mayar mata da kuɗinta, hatta ruwan sha da ƙasa ta saya wa soja, sai MDD ta mayar mata kuɗinsa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ce kuma idan Majalisar ta tashi biyanka tana ninka maka kuɗin ne.
''Duk kusan naira 5,000 da ƙasa ta kashe za ta iya samun naira 15,000 daga MDD'', in ji shi.
Sai dai masanin tsaron ya ce MDD na biya ne kawai idan ƙasa ta cika sharadin da ta gindiya na tura sojojin.
'"Sharaɗin ya ha ɗa da cikakkiyar bataliya da cikakkun kayan aiki, in ba haka ba MDD ba ta biya.''
Ya koka cewa wasu lokutan dakarun da Najeriyar ke aikawa ba sa cika wannan sharaɗi.
Daraja a Majalisar Ɗinkin Duniya

Asalin hoton, NAF/X
Haka kuma masanin tsaron ya ce wata fa'ida da Najeriyar kan samu daga hakan shi ne karin dakara a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kara da cewa tun shekarar 1960 da lokacin da Najeriya ta fara tura sojojinta aikin kiyaye zaman lafiya ƙasar Kongo.
''Tun daga lokacin duka manyan sojojin Najeriya na wancan lokaci sun je ayyukan kiyaye zaman lafiya karkashin tutar MDD'', in ji shi.
Masanin tsaron ya ce to tun shkearar 1967, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani kwamitin tura sojojin kiyayen zaman lafiya na MDD, wato Peace Mission Commission Najeriya ta rika jagorancin kwamitin saboda koƙarinta.
''tun daga wannan lokaci zuwa yanzu, za ka samu yawancin yan Najeriya ne ke jagorancin wannan kwamiti'', in ji shi.
Ƙarin kwarjini

Asalin hoton, NAF/X
Group Captain Sadiq Garba Mai ritaya ya ce Najeriya na samun ƙwarjini a idon ƙasashen duniya, musamman wa danda take tura wa dakarun.
''Hakan zai sa ta ji ita ma karanta ya kai ana damawa da ita a fagen samar da tsaro a duniya'', in ji shi.
Ya ce idan aka je Majalisar Dinkin duniya ko ƙungiyar AU ta Ecowas Najeriyar kan samu bakin magana idan ana batun tsaro a wata ƙasa da take da ta cewa a ciki.
Fatan shiga Kwamitin tsaro na MDD

Asalin hoton, NAF/X
Wata fa'idar da Najeriya za ta iya samu daga tura dakarunta zuwa ƙasashen waje shi ne yiwuwar samun kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
''A MDD wasu lokuta akan yi amfani da irin gudunmowar kuɗi da kasa ke bayarwa wajen ba ta kujerar dindindin, amma a wasu lokutan akan yi amfani da gudunmowar tsaro da kasa ke bayarwa a duniya'', in ji shi.
Ya ce a irin haka Najeriya za ta iya samun wannan dama a duk lokacin da MDD ta tashi ƙarin kujerun dindindin.
''Don haka ne Najeriyar ke ƙoƙarin tura dakarun nata, duk kuwa da tarin matsalolin tsaron da take fuskanta a cikin gida'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ƙarfin tasiri a Ecowas

Asalin hoton, NAF/X
Group Captain Sadiq Garba ya ce wata fa'idar da Najeriya ke samu daga tura dakarunta zuwa ƙasashen waje shi ne ƙara ƙarfin tasirinta a ƙungiyar Ecowas.
''Ita dama Najeriya a ƙungiyar Ecowas ko ba ka so ita ce babba ta kowane fanni'', in ji shi.
A cewar masanin tsaron tura dakarun da Najeriyar ke yi zuwa ƙasashen ƙungiyar na ƙara mata karfin tasiri da faɗa a ji a yankin yammacin Afirka.
''Idan aka samu wata araka a yammacin Afirka, to najeriyar ce dai ke da karfin da za ta iya tarewa'', in ji shi.
A shekarar da ta gabata ma Najeriya ta tura dakarunta zuwa ƙasar Guinea Bissau a lokacin da sojojin ƙasar suka yi yunƙurin kifar da gwamnatin farar hula.












