Ajiye makami ko janyewa: Wane zaɓi ya rage wa Hezbollah?

Isra'ila ta yi nasara wajen kashe manyan kwamandojin Hezbollah a watan Satumbar 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Isra'ila ta yi nasara wajen kashe manyan kwamandojin Hezbollah a watan Satumbar 2024.
    • Marubuci, بی‌بی‌سی عربی
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A karon farko Hezbollah ta tsinci kanta cikin wani irin rudani na siyasa da soji cikin shekaru masu yawa.

Bayan harin da ya yi sanadin shugabancinta da tsarin sojojinta, tambayar da ake yi yanzu ba ta yadda Hezbollah za ta mayar da martani ba ne; magana ce kan wanene zai wakilci Lebanon ya kuma yanke hukunci kan tattaunawar da za a yi ta makomar Lebanon da kuma makaman Hezbollah.

Hezbollah za ta iya iko da mkamanta da mayaƙanta idan gwamnatin Lebanon ta ja ragamar tattaunawa tsakaninta da Amurka, ya kasance kuma Hezbollah kuma ba ta son tattaunawar?

Hezbollah na da zaɓuka uku ne kawai kacal: jira kan tsarin da za a yi tsakanin Iran da Amurka da zai haɗa da batun Lebanon.

Yarjejeniyar da ake tsammani da Washignton za ta ɗauki nauyi tsakanin Lebanon da Isra'ila wadda za ta kai ga kwashe mayaƙanta da kuma ajiye makaman 'yan ƙungiyar.

Dawo a ci gaba da yaƙin soji, duk da cewa akwai haɗarin da hakan ke tattare da shi ga yakin Kudancin Lebanon, Beirut da kuma yankin da nan ne mayaƙan Hebollah suka fi ƙarfi.

Ko ɗaya daga cikin waɗannan zaɓukan ba masu sauƙi ba ne.

Yankin Lebanon

Asalin hoton, Getty Images

Ya aka yi Hezbollah ta kawo wannan matakin?

A ranar 2 ga watan Maris ne Hezbollah tace ta shiga wani yaƙin yanki bayan harin da Amurka da Isra'ila ta kai wa Iran. Ƙungiyar ta ce hare-haren da take kaiwa na ramuwa ne ga kashe shugaban addinin Iran Ali Khamenei da kuma karya yarjejeniyar da tsagaita wuta da Isra'ila ta yi ta Nuwamba 2024.

Amma lissafin Hezbollah bai taƙaita ba ne kawai kan aikin soji kawai. Rahotanni sun ce Hezbollah na fatan za a sako batunta cikin yarjejeniyar da za a tattauna tsakanin Iran da Amurka da za ta kai ga dakatar da hare-hare, da kashe-kashe, rushe-rushen gidaje da kuma janye dakarun Isra'ila daga Kudancin Lebanon.

Tun daga nan, an sanar da tsagaita wuta sama da ɗaya, amma bubu ko guda da takawo ƙarshen aikin Isra'ila a kudanci da koma ficewar dakarunta baki ɗaya.

Hanyar tattaunawa da Iran

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi tsakanin Amurka da Iran a ranar 8 ga watan Afrilu da ɓangarorin biyu suka amince a tattauna a Islamabad, Hezbollah ta yi burin cewa hanyar da Iran ta ɗauka mai bullewa ce.

Amma rashin amincewa kan Lebanon wata shida ce tun daga farko. Iran ta nemi dukkan tattaunawar ta haɗa da fagagen yaƙi, ciki har da na Lebanon, yayin da ita kuma Amurka da Isra'ila suka ƙi amincewa Lebanon ta kasance cikin yarjejeniyar.

Awanni bayan tsagaita wutar, Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare sama da 100 a Beirut, yankin dake kudanci, da Bekaa da kuma wasu sauran yankunan kudanci cikin mintina 10.

A cewer hukumomin Lebanon waɗannan hare-hare sun kashe sama da mutane 100 sun kuma jikkata dubbai. Sojojin Isra'ila sun ce sun hari cibiyoyin kwamandojin Hezbollah ne da wasu gine-gine da ke da alaƙa da su.

Daga nan Tehran ta gindaya sharaɗin cewa za ta ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar ne kawai idan aka dakata da kai hare-hare Lebanon. Kazalika ta alƙanta hakan da buɗe mashigar Hormuz don tabbatar da tsagaita wuta ta dindindin.

Bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanya baki cikin lamarin, Isra'ia ta dakatar da kai hare-haren na wani ɗan lokaci samma ta ci gaba da kaiwa a kudanci.

Raunata lissafin barazanarsu

Hassan Nasrallah, wanda shi ne tsohon sakataren janar Hezbollah yana yawan faɗa a bayanansa kan lissafin yadda Hezbollah za ta riƙa kai hari Tel Aviv a matsayin ramuwar hare-haren da ake kai musu yankin kudancin Lebanon. Amma lissafin Hezbollah ya ruguje ne bayan yaƙin 2024.

Ƙungiyar ta yi rashin adadi mai yawa na kwamandojinta, cikin har da shi Hassan Nasrallah da Hashem Safi al-Din, mutumin da aka zaɓa ya maye gurbinsa amma aka kashe shi gabanin naɗa shi.

A cewar wasu jami'ai, an riƙa kaiwa tsarin mayaƙan Hezbollah hari ne a wani buɗaɗɗen shiri, ciki har da wajen ajiye makaman masu linzaminsu da kuma tashoshinsu.

Bayan tsgaita wutar watan Afrilu, Mafi yawan hare-haren Hezbollah tana kai su ne kan dakarun Isra'ila da ke kudancin Lebanon. Hezbollah ta riƙa amfani da jurage maras matuƙi da ke cin gajeren zango da suke kai hari kan sojoji da motocinsu da kuma sansanonin sojojin.

Saɓanin haka, hare-haren da take kaiwa arewacin Isra'ila sun ragu. Wannan salon ya ci gaba har zuwa lokacin da aka cimma yarjejeniyar watan Yuni, wanda kuma daga nan ne yawan hare-haren suka ragu sosai.

Lokacin da Isra'ila suka kai hari yankin a ranar 7 ga watan Yuni Hezbollah ta kai hari kan yarewacin Isra'ila, yayin da Dakarun juyin juya halin su kuma suka buɗe wuta kan makaman masu da ke yankin Isra'ila.

Hanyar da Washington ke son bi don tattaunawa

Bugu da ƙari kan dogaron da ta yi kan Iran, gwamnatin Lebanon ita ma ta ayyana nata shirin na tattaunawa ta daban da Isra'ila, wadda Amurka za ta taimaka a cimma ta.

Gwamnatin Lebanon ta ce ƙasar da ke da 'yanci tana son a yi tattaunawar ne a matsayinta na mai 'yanci kuma ya zama abin da ta nema shi za a yi amfani da shi maimakon sakamakon tattaunawar Tehran da Washington.

Wannan ya sa aka samar da wani daftarin yarjejeniyar da zai kori sojojin Isra'ila daga yankin kudancin ƙasar, da kai sojojin Lebanon yankunan da kuma karɓe makaman mayaƙan Hezbollah gabanin faɗaɗa ta zuwa wasu sassa.

Hezboullah ba ta amince da yarjejeniyar ba inda ta yi amannar za a mayar da karɓe makaman mayaƙan ƙungiyar babban lamarin da sai an cimma shi dakarun Isra'ila za su fice daga yankin.

Amma a gefe guda kuma gwamnatin Lebanon ta fara aiwatar da yarjejeniyar, kuma dagarun Lebanon sun isa yankunan da dakarun Isra'ila suka fice daga garin Zutar al-Gharbiya, wani mataki da ake gani a takun farko na aiwatar da yarjejeniyar.

Kungiyar Hezbollah

Asalin hoton, Getty Images

Karɓe makamai za a fara ko ficewar sojin Isra'ila?

Isra'ila ta ce ba za ta fice ba baki ɗaya har sai an kwace makaman da ke hannun mayaƙan Hezbollah, an kuma girke dakarun Lebanon, a wani abu da ake wa kallon barazana ga arewacin iyakarta.

A wani mataki na daban, Isra'ila ba ta son ta tattauna makomarta gabanin Isra'ila ta dakatar da kai hare-harenta, da ficewar dakarunta baki ɗaya, ta koma mahallanta.

Sakatare Janar na Hezbollah Naim Qassem ya dage kan sai an ci gaba da kai hare-haren har sai dakarun Isra'ila sun kammala ficewa daga yankin baki ɗaya.

Amma wannan rashin fahimtar bai tsaya ba tsakanin Hezbollah da Isra'ila

Wane zaɓi ne ke a ƙasa?

Zaɓin farko shi ne ci gaba da jiran yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.

Wannan yarjejeniyar za ta iya sanya dakarun Isra'ila ficewa ba tare da sharaɗin kwace makaman da ke hannun mayaƙan Hezbollah ba tare da gindaya sharaɗi ba. Sai dai har yanzu babu wanda ya san lokacin da kuma yadda sakamakon tattaunawar zai kasance.

Zaɓi na biyu shi ne bin abin da gwamnatin Lebanon ta zo da shi. shi ne ficewar dakarun Isra'ila daga yankin sannu a hankali, da shigar da na Lebanon yankunan da ta mamaye, da kuma fara sabunta gine-ginen da aka lalata yayin yaƙin, sai dai a wannan zaɓin ajiye makaman Hezbollah shi ne ginshiƙin tattaunawar yarjejeniyar.

Zaɓi na uku shi ne komawa filin daga. wannan zai baiwa Hezbollah damat matsa lamba ga Isra'ila, amma haɗarinsa shi ne za a ci gaba da jefa bama-bamai yankin Beirut da ke kudanci.

Sai dai masu suka za su zargin Hezbollah da ci gaba da yaƙi wani abu da ya yi daidai da muradan Iran.

Wadannan zaɓukan ba za a raba su da duk wani ci gaba da za a iya samu ba kan tattaunawar.