Alamomin rashin lafiya 5 da mutane ba su cika ba su muhimmanci ba

Asalin hoton, Getty Images
Kowane mutum akwai yadda yake duba lafiyarsa. Waasu da zarar su ji wasu alamomi sukan yi saurin garzayawa asibiti, yayin da wasu kuma kan yi ta jan ƙafa har sai rashin lafiya ta yi tsanani
Sai dai masana kiwon lafiya sun ce wasu alamomin da mutane kan ɗauka da wasa na iya zama gargaɗin wata babbar cuta da ke buƙatar a fara magani cikin gaggawa.
Canjin launin farce, sauyawar launin leɓɓa, rage nauyi ko kuma yawan minshari na daga cikin alamomin da masana suka ce bai kamata a yi biris da su ba.
Duk wani sabon canji da mutum ya ji a jikinsa, akwai buƙatar a maida hankali kanta, ko da kuwa ana gani ba wani abu ba ne.
Wasu manyan cututtuka irin su kansa kan fara ne ba tare da wata alama a fili ba. Haka kuma cututtuka irin su HIV da ciwon hanta na iya ɗaukar lokaci mai tsawo a jiki ba tare da mutum ya lura ba.
Bambanci alamar rashin lafiya da abin da mutum ke ji
A fannin kiwon lafiya, akwai bambanci tsakanin alamar cuta da kuma abin da mara lafiya ke ji. Alamar cuta ita ce abin da wasu za su iya gani ko kuma a auna da na'ura. Misali akwai kurajen fata, zazzaɓi ko kuma ƙaruwar sukari a jini.
Amma abin da mara lafiya ke ji shi ne abin da mutum kaɗai yake iya ji ko bayyanawa, kamar ciwo, jiri ko kuma jin ƙara a kunne.
Masana sun ce a mafi yawan lokuta, irin waɗannan abubuwan da mara lafiya ke ji su ne kan fara bayyana kafin a gano wata cuta.
Ga wasu daga cikin alamomin da masana suka ce bai kamata a yi watsi da su ba.
1. Rage nauyi
Rage nauyin jiki ba tare da an sauya tsarin cin abinci ba ko kuma ƙara yawan motsa jiki na iya zama alamar wata babbar rashin lafiya.
Likitoci na ba da shawarar mutum ya nemi shawarar ƙwararren likita idan ya rasa sama da kashi 5 cikin 100 na nauyin jikinsa ba tare da wani dalili ba.
Irin wannan raguwar nauyi na iya kasancewa da alaƙa da wasu cututtuka kamar ciwon suga, thyroid, kansa, ciwon zuciya ko kuma matsalolin rashin narkewar abinci.
2. Ciwon ƙirji

Asalin hoton, Getty Images
Ciwon ƙirji, musamman idan ciwon yana ƙaruwa zuwa ƙugu, ko wuya, kafaɗa ko kuma saman baya, na iya zama alamar kamuwa da bugun zuciya.
Masana kiwon lafiya sun ce wannan yanayi na buƙatar a ɗauke shi da muhimmanci, da neman taimakon likita cikin gaggawa.
3. Sauyawar launin farce

Asalin hoton, Getty Images
Sauyawar launi ko kamannin farce na iya zama wata alama da ke nuna akwai matsalar lafiya a jikin mutum.
Idan farce ya koma launin rawaya ko shuɗi ko fari, ko kuma ya fara samun wasu sauye-sauyen da ba a saba gani ba, hakan na iya zama alamar matsalolin huhu, zuciya, hanta, ƙoda, ko kuma ƙarancin wasu sinadaran gina jiki.
Idan irin waɗannan sauye-sauyen suka ci gaba da kasancewa, ana ba da shawarar a je a ga likita, musamman ƙwararren likitan fata, domin a yi cikakken bincike.
A wasu lokuta kuma likita kan ba da umarnin a yi gwaje-gwaje, ciki har da gwajin jini, domin gano musabbabin matsalar.
4. Sauyawar launin leɓɓa zuwa shuɗi
Idan launin leɓɓa ko fata ya koma shuɗi, hakan na iya nuna cewa jiki ba ya samun isasshen iska shaƙa.
Masana sun ce wannan na iya kasancewa alamar matsalar zuciya ko huhu, kuma akwai buƙatar a nemi kulawar likita cikin gaggawa.
5. Yawan gumi da dare

Asalin hoton, Everlyne Juma
Yawan yin gumi da dare ba lallai yana nufin akwai wata babbar matsala ba. Sai dai ida mutum na yawan yin zufa ba tare da wani dalili ba, bai kamata a kauda kai ba.
Masana sun ce yawan yin gumi da dare, musamman idan ba saboda zafin yanayi ba ne, na iya kasancewa alamar kamuwa da wata cuta, sauyin sinadaran hormones a jiki, ko kuma wasu manyan cututtuka irin su tarin fuka da kuma wasu nau'ikan kansa.
Idan irin hakan ya ci gaba da faruwa akwai buƙatar mutum ya ga likita.
A riƙa duba lafiya akai-akai
Masana kiwon lafiya suna ba da shawara ga mutane cewa su riƙa lura da duk wani sauyi da suka ji a jikinsu, ko da kuwa suna ganin kamar ƙaramin abu ne.
Idan wata alama ta ci gaba ko kuma ta ƙara tsananta, yana da kyau a lura da lokacin da ta fara, da yadda take canzawa da kuma ko akwai wasu alamomi da suka biyo bayanta, sannan a tuntuɓi likita.
Gano cuta tun da wuri na ƙara yiwuwar samun nasarar yin magani, tare da rage tsananin matsalar. Saboda haka, idan jikinka ya fara nuna alamun da ba ka saba gani ba, kada ka kauda kai.












