Madrid ta karɓo Yan Diomande, Liverpool na zawarcin Ibrahim Mbaye

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta cimma yarjejeniya ta fam miliyan 120 da RB Leipzig kan ɗanwasan gaba na Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 19 bayan tsawon lokaci suna tattaunawa. (Athletic - subscription required)
Liverpool na diba yiyuwar ɗauko matashin ɗanwasan Paris St-Germain da Senegal Ibrahim Mbaye mai shekara 18. (Times - subscription required)
Aston Villa ta cimma yarjejeniya tsakaninda da Atletico Madrid kan ɗanwasa baya Matteo Ruggeri, mai shekara 24. (Marca - in Spanish)
Ana alakanta Liverpool da ɗanwasan baya na Real Madrid Raul Asencio, mai shekara 23, bayan sanar da ɗanwasan na Spain zai iya barin Madrid a wannan bazara. (Teamtalk)
Fulham na dab da lale fam miliyan 30 domin dauko ɗanwasan tsakiya na Southampton da Northern Ireland Shea Charles, mai shekara 22, (Talksport)
Trabzonspor na kokarin sake hada ɗanwasan gaba na Uruguay da Al-Hilal Darwin Nunez, mai shekara 27 da tsohon abokin wasansa a Liverpool ɗan ƙasar Masar Mohamed Salah, a kungiyar ta Turkiya. (Spor Depor - in Turkish)
Aston Villa na jiran sabon tayin Arsenal kan ɗanwasan baya na Ingila Ezri Konsa, mai shekara 28, yayin da take ƙoƙarin ya sabunta kwangilar shi a Villa Park. (Mail)
Real Madrid na shirin rabuwa da ƴanwasan tsakiya na Faransa guda biyu Aurelien Tchouameni da Eduardo Camavinga da Manchester United ke zawarci domin ta samu kuɗin da za ta karɓo Rodri daga Manchester City. (El Nacional - in Spanish)











