Yadda yawan cin bashi ya janyo musayar yawu tsakanin Atiku da Fadar Shugaban ƙasa

Asalin hoton, Tinubu/Atiku/Facebook
Wata sabuwar jayayya ta kaure tsakanin fadar shugaban Najeriya da ɗan takarar jam'iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar, inda ta mayar da martani akan zargin da ya yi wa gwamnatin na kasa amfani da kuɗaden da aka cire a matsayin tallafin man fetur yadda ya dace.
Atikun ya ce duk da ɗimbin kuɗaɗen da gwamnatin Najeriyar ke ci gaba da zaftarewa amma har yanzu ƙasar ta duƙufa wajen karɓar bashi, abin da ke kara durƙusar da tattalin arzikinta da kuma jefa jama'a cikin talauci.
Sai dai fadar shugaban ƙasar ta ce yana cin tuwo ne kawai da miyar bara.
Tun da farko dai ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriyar ta mayar da karɓar bashi tamkar shurin masaƙi da ya wuce ƙima tun daga kasafin kuɗin shekarar 2024.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya kuma nuna shakku kan cire tallafin man fetur, inda ya soki sauye-sauyen haraji da gwamnati ta aiwatar, tare da zargin gwamnati da ƙirƙirar alƙaluman bogi da ke nuna ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
AbdulRasheed Uba Sharada ɗaya daga cikin masu magana da yawun Atiku Abubakar ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin ne domin cimma wata manufa ta ƙashin kai.
"Daga ranar da aka ranstar da shi ya karkatar da tattalin arziƙin Najeriya cikin wannan yanayi na ƙunci da kuma koma baya ga talakan Najeriya."
AbdulRasheed Uba ya zargi gwamnatin da ciwo bashi ba bisa ƙa'ida ba,"Tun daga ranar da aka rantsar da Tinubu bashin Najeriya bai fi, naira tiriliyan 23 ba, amma yanzu ana maganar sama da tiriliyan 40, shin ina waɗannan kuɗaɗe suka shiga?
Atiku fargar jaji yake yi - Gwamnatin Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya ce zarge-zargen Atiku sun ta'allaƙa ne kan tsofaffin bayanai da ba su nuna manyan nasarorin tattalin arzikin da aka samu a shekarun 2025 da 2026.
"Kuskuren da shi tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya yi shi ne, tuni an wuce wannan wuri ba mu sani ba ko bacci yake, ko sai yanzu ne ya yi fargar jaji."
Malam Abdulaziz ya ce bayan cire tallafin ne wasu jihohi suke iya biyan albashi, sannan ana ɗaukar sabbin ma'aikata.
"Akwai da yawa da ba su aikin albashi, amma idan aka yi shi, kasuwa tana motsawa, sannan gwamnati na kashe kuɗaɗe ba kaɗan ba wajen samar da ƙananan tashoshin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, a manyan makarantu da asibitoci da cikin al'umma."
A baya-bayan nan ɗan takarar na jam'iyyar ADC ya yi zargin cewa a kasafin kuɗin Najeriya na 2026, an yi wani cushen da ya zarta naira tiriliyan 12 da har kawo yanzu ba a san ko na mene ne ba, Iinda ya ce an jibge kasafin ne a ma'aikatun gwamnatin tarayya goma kacal tare da watsar da sauran ma'aikatu.
Ba a ga wani alfanun cire tallafi ba - Masana
Farfesa Ahmed Adamu, masani kan harkokin man fetur kuma malami a jami'ar Philomath University da ke Abuja, babban birnin Najeriya ya ce rashin ganin amfanin cire tallafin man fetur a Najeriya na da alaƙa da farashin dalar Amurka.
A cewarsa darajar dalar Amurka ta nunka bayan cire tallafin man fetur, wannan ya sanya alfanun da ake tunanin za a samu daga ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin Najeriya ta samu daga cire tallafi bai yiwu ba.
Masanin tattalin arziƙi Dr Shamsudden Muhammad ya ce "ba a ga wani alfanu da cire tallafin ya kawo wa Najeriya ba ya zuwa yanzu, in baya ga biyan buƙatun wasu ƙungiyoyin duniya da wasu ƙasashen duniya da suka matsa a cire tallafin.
Ya bayyana cewa irin waɗannan hukumomi su ne Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF) da kuma Bankin Duniya (World Bank).











