Abin da ya sa gwamnatin Najeriya ta sake buɗe ƙofar tuba ga ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A duk lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta bai wa masu ɗauke da makamai damar ajiye makamansu da miƙa wuya, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: me ya sa gwamnati ke ci gaba da bai wa waɗanda ake zargi da aikata munanan laifuka irin wannan dama?
A Najeriya, wannan tsari ba sabon abu ba ne. A baya dai an fi danganta tsarin karɓar ƴanbindigar da suka miƙa wuya da mayaƙan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, da kuma sauran ƙungiyoyi a wasu sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Yanzu kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa duk wata ƙungiyar da ke ɗauke da makamai a ko'ina cikin ƙasar da ta yanke shawarar ajiye makamanta za a karɓe ta.
A cikin 'yan shekarun nan, yankin Kudu maso Gabas ya fuskanci hare-hare da dama kan jami'an tsaro, cibiyoyin gwamnati da kuma fararen hula.
Saboda haka ne rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da Operation UDO KA, wadda manufarta ita ce tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Wannan sabon matakin na nuna cewa daga yanzu tsarin ya shafi duk wata ƙungiya mai ɗauke da makamai a sauran wuraren da rundunar soji ke gudanar da aiki.
Abin da gwamnatin Najeriya ta sanar
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce ta faɗaɗa tsarin karɓar masu miƙa wuya daga cikin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai zuwa dukkan sassan ƙasar.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana cewa daga yanzu duk wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma su ma za su iya miƙa wuya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da aka tambaye shi ko an faɗaɗa tsarin zuwa sauran yankunan ƙasar, ya amsa da cewa: "Eh. Muna maraba da duk wanda ya miƙa wuya."
Ya ce rundunar sojin Najeriya za ta karɓi duk wanda ya miƙa wuya bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjejeniyoyin Geneva, kafin daga bisani a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin doka.
Janar Onoja ya kuma jaddada cewa rundunar soji na gudanar da ayyukanta ne bisa ƙa'idojin da suka dace, dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa da kuma Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
A cewarsa, ba a ƙayyade wani wa'adin lokaci ga masu son miƙa wuya ba.
"A kowane lokaci suna iya miƙa wuya. Amma kuma muna ci gaba da ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren soji," in ji shi.
Rundunar ta ce wannan matakin ya biyo bayan hare-haren da take kai wa ƙarƙashin Operation UDO KA, inda suka tilasta wasu mayaƙan da ke Kudu maso Gabas suka fara miƙa wuya.
Rundunar ta ce bayan miƙa wuyan, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya jagoranci sojoji zuwa ma'ajiyar makamansu.
Me ya sa gwamnati ke son ƴanbindiga su ajiye makamansu?
Masana harkokin tsaro sun ce dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa, ciki har da Yarjejeniyoyin Geneva, sun tanadi cewa idan mayaƙa sun miƙa wuya ko kuma aka kama su bayan sun daina yaƙi, dole a kare rayuwarsu tare da yi musu mu'amala ta mutuntaka.
Sai dai sun ce wannan ba yana nufin za a yafe musu laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba, domin hakan ya danganta da dokokin ƙasar da kuma irin laifukan da ake zargin sun aikata.
Masanin harkokin tsaro, Group Captain Sadik Garba mai ritaya, ya ce yadda Najeriya ke aiwatar da wannan tsari ya sha bamban da yadda wasu ke fahimta.
A cewarsa, ana amfani da tsarin karɓar masu miƙa wuya ne idan sojoji sun fara samun rinjaye a fagen daga, ba wai saboda gwamnati ta gaji da yaƙi ko kuma tana neman yin sulhu da masu ɗauke da makamai ba.
"Yarjejeniyar Geneva cewa ta yi, idan an zo ƙarshen yaƙi a duba a ga waɗanda suka miƙa kansu ko kuma waɗanda aka kama da ƙarfi a yaƙi ba da son ransu ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa waɗannan su ne mutanen da dokokin yaƙi suka tanada cewa a kare su daga cin zarafi, domin sun daina faɗa.
A cewarsa, idan gwamnati ta buɗe ƙofar karɓar masu miƙa wuya a lokacin da hare-haren soja ke ƙaruwa, hakan na iya zama alamar cewa tana ganin ta fara samun galaba a kan masu ɗauke da makamai.
Ko matakin zai taimaka wajen rage matsalar tsaro?
Ko da yake gwamnatin Najeriya na ganin faɗaɗa tsarin karɓar masu miƙa wuya zai ƙara raunana ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, wasu masana harkokin tsaro na ganin lokaci ne zai tabbatar da tasirin matakin.
Group Captain Sadik ya ce a tsarin dokokin yaƙi, batun karɓar masu miƙa wuya ko yafiya kan fi tasiri ne idan an kai wani mataki da aka tabbatar cewa gwamnati ta samu rinjaye a fagen daga.
A cewarsa, abin da ake gani a Najeriya ya samo asali ne daga yanayin da ƙasar ke ciki, inda gwamnati ke ƙoƙarin amfani da irin wannan tsari a yankuna daban-daban.
Ya ce akwai masu ganin tunda an bai wa mayaƙan Boko Haram da wasu masu ɗauke da makamai a Arewa damar miƙa wuya, ya kamata a bai wa ƙungiyoyin da ke sauran yankunan ƙasar irin wannan dama.
"Wannan na faruwa ne a matsayin wani matakin siyasa, ba wai saboda doka ta wajabta hakan ba," in ji shi.
Sai dai ya jaddada cewa kowace ƙasa na da ikon tsara yadda za ta tafiyar da lamuran tsaronta.
"Ƙasa tana da damar ta yi afuwa ga waɗanda take so, kuma hurumi ne na ita kanta."
Duk da haka, masanin ya ce zai yi wuya a tantance tasirin wannan tsarin kafin a ga yadda rikice-rikicen za su ƙare.
Ya ce a fahimtarsa, har yanzu ba a kai matsayin da za a ce ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun shiga wani irin matsi da zai tilasta musu miƙa wuya ba.
Mene ne fa'ida da ƙalubalen wannan tsari?
Masana harkokin tsaro na cewa tsarin karɓar masu miƙa wuya na iya taimakawa wajen rage zubar da jini, tattara bayanan sirri daga tsofaffin mayaƙa da kuma raunana ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai idan aka aiwatar da shi a lokacin da ya dace.
Sai dai suna gargadin cewa idan ba a gudanar da shi yadda ya kamata ba, zai iya haifar da saƙon da zai sa wasu su ɗauka cewa gwamnati na sassauta wa masu aikata laifuka.
Group Captain Sadik ya ce akwai yiwuwar a fuskanci ƙalubale idan manufar aiwatar da tsarin ta fi karkata ga cimma wata manufa ta siyasa maimakon ta fuskar tsaro.
A cewarsa, idan ana son tsarin ya yi tasiri, wajibi ne gwamnati ta ci gaba da matsa lamba ta hanyar hare-haren soji da sauran matakan tsaro har sai masu ɗauke da makamai sun fahimci cewa ba su da wata mafita face miƙa wuya.
Ya ce a mafi yawan rikice-rikicen da suka faru a duniya, masu tayar da ƙayar baya ba sa ajiye makamansu sai bayan sun rasa ƙarfin ci gaba da faɗa ko kuma sun ga cewa ba za su iya cimma burinsu ba.
Saboda haka, ya yi gargadin cewa bai kamata gwamnati ta fito ta nuna kamar tana roƙon masu ɗauke da makamai su miƙa wuya ba, domin hakan na iya ba su wani ƙarin ƙarfin gwiwa ko kuma ya sa wasu su ɗauka cewa gwamnati na cikin matsin lamba.
"Kamata ya yi a matsa mutum ya kawo kansa tukuna, ba wai gwamnati ta riƙa miƙa masa buƙata ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan gwamnati ta ci gaba da ƙarfafa hare-haren soji tare da rage ƙarfin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, hakan ne zai sa wasu daga cikinsu su ga babu wani zaɓi face miƙa wuya.











