Fitattun matan arewacin Najeriya da ke cin riba da shafukan sada zumunta

    • Marubuci, Kalarawi Badriyya
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Dandalin sada zumunta da muhawara wani fage ne da mutane daga fannoni daban-daban ke haɗuwa domin sada zumunta.

Wani wuri ne da ke hada na gari da mugu, talaka da mai kudi, mata da maza, yara da manya da sauransu.

Baya ga wannan shafukan na taka rawa wajen ilmantarwa da nishadantarwa har da zama kafar tallata haja ga ƴan kasuwa, manya da matsakaita da ƙanana.

Matan arewacin Najeriya na amfani da shafukan sada zumunta, irinsu TikoTok, Facebook, Instagram da Youtube domin gudanar da harkokin yau da kullum.

Za mu duba wasu daga cikin fitattun mata a arewacin Najeriya da sukai shuhura a shafukan sada zumunta, masu tarin mabiya da kuma suke tallafa fannonin da suka kware na rayuwa.

Aisha Falke

An fi sanin ta da sunan Malamar Aji kamar yadda masu bibiyar shafinta suka yi ma ta laƙabi a shafinta na Instagram mai mabiya 605k.

Shafin ya zama wani dandali da mata musamman na aure ke baje kolin matsalolinsu na zamantakewar aure, ko dai na dangin miji ko ƴan uwa ko abokan arziki.

Wasu na cewa a dandalin aka yankewa kalamar 'Malama hide my ID' a shafukan sada zumunta, sakamakon yadda masu aiko da sakon ke buƙatar a sakaya sunansu.

Ta na amfani da shafin domin nishaɗantarwa da ilaman tarwa da kuma neman kudi, a shekarar 2024 ta kaddamar da wata kasuwa ta intanet, mai sunan NH02.

Wanda ya yi rigista zai dinga sabuntawa a kowacce shekara bayan biyan wasu ƙudade, aƙwai damar tallata hajar shi da samun sabbin abokan ciniki.

Hadiza Ibrahim Ango (Chefamors)

Hadiza na da mabiya 1,200,000 a shafin sada zumunta na Instagram, ta yi fice wajen girke-girke nau'o'i daban-daban.

Tun daga na gargajiyar Bahaushe, da na turawa da larabawa har da sauran kasashe, ta na amfani da shafin na ta wajen koyar da girke-girken inda mabiya a ciki da wajen Najeriya ke shiga domin kallo, bayan biyan ƙuɗaɗe.

Hadiza na yi wa kamfanoni tallace-tallace musamman dangin abinci, da kayan kyale-kyalen gida da sauransu kuma ba wai a wuri daya ta ke yin hakan ba, a'a har balaguro ta ke yi a arewaci da kudancin Najeriya.

Murjanatu Umar (Voice of Bazawara)

Murjanatu Umar da aka fi sa ni da Voice of Bazawara ko muryar Bazawara da Hausa, na da mabiya 1,55000 a shafin sada zumunta na Instagram.

Ta yi fice wajen tallafawa matan da auren su ya mutu kuma suke cikin matsin rayuwa, ko wadanda aka rasu aka bar musu marayu.

Da tallafin kula da lafiyar mata da yara da tsofaffi, sai kuma ciyar da mabukata musamman ranakun Juma'a.

Murjanatu na samun kudaden tafiyar da wannan aikin daga asusun da jama'a ke ba da gudummawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ta kuma yi shela a shafukanta na sada zumunta.

Fauziyya D Sulaiman

An fi sanin Fauziyya D Sulaiman a fannin adabi, fitacciyar marubuciyar littafan Hausa na soyayya da nishadantarwa wadda littafanta suka karade kasuwannin arewacin Najeriya.

Daga bisani Fauziyya ta fantsama masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, bata sauka daga layin da aka san ta da shi ba.

Ta ci gaba da rubuta labarai da suka rikide fina-finai misali shiri mai dogon zango na Garwashi da tashar Arewa24 ke haskawa, kuma ta na gabatar da wani shiri duk dai a tashar.

A shekarar 2019 Fauziyya ta kafa gidauniyar Creative Helping Needy, domin tallafawa marayu da marassa lafiya mata da maza ba 'yan asalin jihar Kano kadai ba, har da jihohi makofta.

Yawan wallafa hotuna da bidiyon marassa lafiya da ta ke yi ya sa kamfanin Meta mamallakin Instagram ya sauke shafinta mai mabiya sama da 100,000, amma daga bsiani ta sake bude wani mai mabiya 25000.

Fatima Fu'ad Hamshim

Fatima Fu'ad Hashim ma mallakiyar shafin Open Diaries Foundation ta fara da tallafin rabon abinci a lokacin Azumin watan Ramadan, a hankali dandalin ya zama wurin da mata kan zo su bayyana damuwarsu ko dai akan matsalolin da suka shafi aure, da zaman takewa.

A hankali dandalin mai mabiya 22.5K a zama wata cibiya ta taimakon mabukata musamman mata da kanan yara, ta na samun kudaden tafiyar da gidauniyar ta daga gudummawar da al'umma ke badawa, ciki har da kamfanonin da suke samar da kayan abinci da na tsaftar gida da sauran.

na kuma koyawa mata sana'o'in hannu na dogaro ga kai, da taimakon asibiti da sauransu.

Ta na amfani da shafinta na sada zumunta wajen tallata hajarta, har ta kai da kafa masana'antar yin kunun larabawa wato Sabaya da sauran kayan abinci na gargajiya.

Aisha Abba Girema (Aishan Borno)

Wadda aka fi sani da Aishan Borno a shafukan sada zumunta musamman Instagram da ta ke da mabiya 79.9K, 'yar asalin jihar Borno mazauniyar yankin Scotland a Birtaniya.

Shafinta ya yi fice wajen koyawa mata nau'ukan abincin kabilar Kanuri daban-daban, da na turawa da larabawa har da shayi mai kayan kamshi.

Sannu a hankali ta sake rikiɗe wa mai koyar da harshen Kanuri, musamman kalmomi irin na gaisuwa da sauransu.

Ta kan yi ayyukan taimako da suka shafi tallafawa marayu, sai kuma lokacin da mummunar ambaliyar ruwa ta fadawa jihar Borno, inda ma ayukanta suka kara fadada.

Aisha Girema, ta ƙara daukar hankalin masu bibiyar shafinta lokacin da ta fara koyar da yadda ake hada turaren wuta da na jiki waɗanda mutanen Borno sukai fice a kai. Duk da nisan da ke tsakanin Birtaniya da Najeriya amma ta kafar sada zumunta ta ke koyarwa.

Baya fa wannan ta na koyawa mata yadda za su yi amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI ta hanyar da ta dace da kuma samun kudade, ajin na ta ya na da dalibai sama da 800.

Hyda Ahmad Ghaddar (Coach Hyda)

Ana yi wa Hyda Ahmad Ghaddar kirarin Mace mai kamar maza..... Haifaffiyar jihar Kano amma tushen kasar Lebanun.

Mai horas da ƴan wasan wallon ƙafa ce, ta kafa makarantar Breakthrough Football Academy a jihar Kano.

Tun ta na ƴar shekara 5 Hyda ta fara nuna sha'awar wasan ƙwallon kafa, inda suke yi da ƴan uwanta maza.

Daga bisani ta koma gida Lebanun inda ta hadu da sauran taƙwarorinta mata ma su buga ƙwallon, wani lamari da ya kai ta da buga wasa da kungiyoyi a Najeriya da Ingila da Labanun.

Hyda ta yi fice ne kasancewarta mace kuma ta zabi horas da ƴan wasa a Najeriya kuma jihar Kano.

Ta ce burin ta shi ne wata rana ƴan wasan da ta ke horas wa ta a jihar Kano su taka matsayin bugawa ƙasarsu wasa a matakin ƙasa da ƙasa, ta na da mabiya 12.5 a Instagram.

Layla Ali Othman

Da farko an fi sanin Layla da harkar gyaran gida da ƙawata shi, ta na da kamfanin yin gadaje da kujeru da duk wani abu da ake amfani da katako domin yi a kuma ƙawata gida ko ofis da sauransu.

Layla Ali Othman ta na amfani da shafukan sada zumunta musamman Instagram mai mabiya 1,000,000 wajen wallafa bidiyon kalaman karfafawa mata gwiwa a fannoni daban-daban na rayuwa, ta kasance wadda ke bai wa mata shawara kan neman na kai da tsayawa kan gaskiya.

Sai kuma ta tsunduma harkar girke-girke da buɗe wurin saida abinci, musamman na gargajiya, kuma ta shafukan sada zumunta ake yin rabin cinikin da hulda da abokan kasuwanci ke yi.

Turaren Wuta ByRay

Sunanta Rahanatu Ahmad Aliyu, amma an fi sanin ta da sunan Turarenwuta By Ray kasancewar shi ne kamfanin ta na haɗa turarukan wuta na gida har da na shafawa.

Ta fara tambari a shekarar 2018, lokacin da ta ƙaddamar da kamfanin Turarenwuta a shafukan sada zumunta, kusan rabin abokan hulɗar Rahanatu ta shafin Instagram su ke haduwa, da a yanzu haka ta na da mabiya 198K.

A shekarar 2023 ta yi amfani da wannan kafa wajen shirya bai wa mata horo kan kasuwanci, inda mata sama da 300 suka halarta ta kafar sada zumunta da zuwa da kai.

Ta kara fice lokacin da ta yi gangamin bikin kalankuwar Turarenwuta a jihar Kano, ta yi amfani da damar na yin rangwamen hajarta.

Yawancin mahalarta taronn sun fito daga wajen jihar Kano, amma haka tas tikitin shiga ya kare cikin ƙanƙanin lokaci.

Maryam Adam

Ta na kiran kan ta da sunan ministar Sharholiya ta Najeriya, to amma anan sharholiyar kwarewa a fannin girke-girke ake nufi.

Koyar da girki ta shafin Telegram da Whatsapp na daga cikin ayyukan da ta kware akai. Kusan a kowanne azumin watan Ramadan ta na gudanar da ajin koyar da girki domin sauƙaƙawa mata tunanin abin da za su yi wa iyali a lokacin buda baki.

Ta na yi wa kamfanoni da 'yan kasuwa tallan hajarsu a sassa daban-daban na Najeriya, ta amfani da shafukanta na sada zumunta domin janyo abokan hulɗa ta hanyar wallafa wa ashafinta na Instagram da mutum 695K.