Tasirin kudu maso gabashin Najeriya a siyasar ƙasar

    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A daidai lokacin da aka soma yaƙin neman zaɓe a Najeriya, yankuna shida da ke ƙasar kan taka rawa wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar shugaban ƙasa, inda hakan ya ta'allaƙa da yawan 'yan takarar da yankunan ke da ƙarfin tattalin arzikinsa da ma 'yan siysar da kan fito daga waɗannan yankuna, da kusan a kowane zaɓe ake kallon irin rawar da suke takawa.

Kudu maso Gabashin Najeriya dai na ɗaya daga cikin yankunan da ke da muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar, duk da cewa shi ne yanki mafi ƙarancin jihohi a cikin shiyyoyin siyasar Najeriya shida da suka haɗa da Abia da Anambra da Ebonyi da Enugu da kuma Imo.

A tsarin siyasar Najeriya, jihohi suna da muhimmiyar rawa wajen rabon wakilci a Majalisar Tarayya, rabon albarkatu da kuma samun damar shiga manyan mukaman siyasa.

A halin yanzu, Kudu maso Gabas na da jihohi biyar ne kawai, yayin da Arewa maso Yamma ke da bakwai. Wannan bambanci yana da tasiri kai tsaye kan adadin kujerun Sanata da na Majalisar Wakilai da yankin zai iya samu.

A Majalisar Dattawa, kowace jiha tana da Sanatoci uku, yayin da kujerun Majalisar Wakilai ake rarrabawa bisa tsarin mazaɓu da yawan jama'a.

Wannan ya sa batun wakilci ya kasance muhimmin batu a siyasar Kudu maso Gabas.

Ƙuri'un yankin da tasirinsu

Bari mu duba wasu daga dalilan da suka sa ake ganin yankin Kudu maso gabashin Najeriya ya zama daban wajen bayyana inda nasarar zaɓuka ta nufa ko akasin haka.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Kudu maso Gabas ya nuna yadda zaɓen yankin zai iya samar da gagarumin sakamakon siyasa a Najeriya.

Peter Obi na Labour Party a wancan lokaci, ya lashe dukkan jihohin biyar na Kudu maso Gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu kusan ƙuri'a miliyan biyu a yankin, sama da kashi 87 cikin 100 na ƙuri'un da aka samu a yankin.

Wannan ya kasance gagarumin sauyi daga tsarin da aka saba gani a baya, inda jam'iyyar PDP, ta daɗe tana da ƙarfi a yawancin jihohin yankin a shekaraun baya.

Kuma hakan na nuna yadda 'yan siyasar yankin ke da tasiri ga al'ummarsu.

A zaɓen 2023 ma, jam'iyyar samu gagarumin ci gaba a Majalisar Tarayya, inda rahotannin bayan zaɓen sun nuna cewa wannan sauyi ya karya tsarin da PDP ta dade tana da shi a yankin tun bayan komawar mulkin farar hula a 1999.

Saboda haka, zaɓen 2023 ya nuna cewa siyasar Kudu maso Gabas ba ta kasance a kan tsarin jam'iyya guda ɗaya kawai ba, kuma masu zaɓe a yankin na iya sauya alkiblar goyon bayansu idan yanayin siyasa ya sauya.

Dakta Kabiru Sufi ma;ami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar jihar Bayero da ke Kano, " yanki ne da ke taka rawa idan aka zo harkar zaɓe sai su mazauna yankin suna ganin ba a ba su irin muhimmancin da suke gain ya kamata a ce ana ba su musamman idan an zo matakin siyasar ƙasa, shi ya sa duk lokacin da aka yi juyin siysa suke ƙoƙarin ganin nasu ya shigo a tsarin siysa kuma sukan yi ƙoƙarin ganin sun dunƙule gaba ɗaya su ba shi ƙuri'u kamar yadda aka gani a zaɓen da ya gabata."

Baya ga haka kuma yankin na da wani tsari na goyon bayan ɗan takarar da ya yi

Muhimmancin jihohin yankin

Masana kimiyyar siyasa dai sun danganta yankin na Kudu maso gabashin Najeriya a matsayin mai wata ɗabi'a ta daban, inda al'ummarsa ke dunƙulewa su zaɓi ɗan takarar da ya yi musu, kuma hakan ya sa kowane ɗan takarar shugaban ƙasa ke son samun karɓuwa a yankin, abin da Dakta Kabiru Sufi, ya bayyana da cewa, "wannan shi ne kusan abin da zai iya faruwa a zaɓen da ake tunkara, kowane a cikin 'yan takara, in dai har zai so a yi irin abin da ya faru a baya to shi ne zai so a ce ya ribaci tagomashin da yankin ya yi ƙoƙarin bayar wa a zaɓen da ya gabata," in ji shi.

Kazalika, yankin na daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da masana'antu na Najeriya. Garuruwan Onitsha da Aba da Nnewi musamman suna taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwanci, sarrafa kayayyaki da masana'antu.

A Abia kuma, Aba ta kasance muhimmiyar cibiyar ƙananan masana'antu, musamman na samar da tufafi, takalma, kayan fata da sauran kayayyaki.

Wannan harkar kasuwanci ta sa tasirin yankin ya wuce iyakokin jihohinsa biyar. 'Yan kasuwa daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen Afirka na hulɗa da cibiyoyin kasuwanci na yankin.

Saboda haka, duk wata manufar gwamnatin tarayya da ta shafi haraji, kudin waje, shigo da kaya, fitar da kaya, hanyoyi, wutar lantarki da masana'antu na iya yin tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin Kudu maso Gabas.

Tasirin 'yan kasuwar Igbo da mazauna yankin a sauran Najeriya

Wani muhimmin abu wajen fahimtar tasirin Kudu maso Gabas shi ne yadda al'ummar yankin suka bazu zuwa kusan dukkan manyan biranen Najeriya.

Akwai manyan al'ummomin 'yan kasuwar ƙabilar Igbo a Lagos da Abuja da Kano da Kaduna da Jos, Fatakwal da ma sauran birane.

Saboda haka, tasirin siyasar yankin ba ya takaita ga masu rajistar zaɓe a jihohin biyar ba.

'Yan kasuwa, masu masana'antu, ƙungiyoyin kasuwanci da al'ummomin da suka fito daga Kudu maso Gabas suna da dangantaka da tattalin arzikin sauran yankuna. Wannan na iya ba yankin wata irin tasiri ta fuskar harkokin kasuwanci da hulɗar siyasa da ta wuce yawan kujerun da yake da su a Majalisar Tarayya.

Batun wakilci da tsarin jihohi biyar

Daya daga cikin manyan ƙalubalen siyasar Kudu maso Gabas shi ne tsarin rabon jihohi.

Yankin yana da jihohi biyar kacal, yayin da wasu shiyyoyin ke da jihohi shida ko bakwai. Wannan yana nufin akwai bambanci a yawan kujerun Sanata da kuma wasu matakan rabon wakilci da albarkatun tarayya.

Wasu masu ruwa da tsaki a yankin suna ganin wannan a matsayin wani babban dalilin da ya sa Kudu maso Gabas ke samun ƙarancin wakilci idan aka kwatanta da yankunan da ke da ƙarin jihohi.

Sai dai a cewar Dakta Kabiru Sufi, "duk da yankin ba shi da yawan jama'a, amma al'ummarsa fa sun ba zu a wasu sassan Najeriya, kuma ana ganin wannan ne ma ya sa sakamakon da aka samu a jihar Legas ya bada mamaki a zaɓen da ya gabata saboda al'ummarsu da ke zaune a can".

Masanin ya kuma ce wannan ya kan taimaka musu yin tasiri a duk zaɓukan da suka goya wa baya.

Sai dai wannan batu yana da sauran fannoni da ya kamata a duba, ciki har da yawan jama'a, yawan masu rajistar zaɓe, tsarin mazabu da kuma yadda 'yan siyasar yankin suke amfani da kujerun da suke da su.

Biafra da siyasar yankin

Ba za a iya tattauna siyasar Kudu maso Gabas ba tare da ambaton tarihin Yaƙin Biafra da tasirinsa kan dangantakar yankin da gwamnatin tarayya ba.

Shekaru da dama bayan ƙarshen yaƙin, batun Biafra ya ci gaba da kasancewa wani ɓangare na muhawarar siyasa da zamantakewa a yankin.

A 'yan shekarun nan, ayyukan ƙungiyoyin masu fafutukar kafa Biafra da matakan tsaro da gwamnatin tarayya ta ɗauka sun kuma zama wani muhimmin ɓangare na yanayin siyasar yankin. Masu sa ido kan zaɓen 2023 sun yi gargadin cewa hare-hare kan ofisoshin INEC da matsalolin tsaro a wasu sassan yankin na iya shafar gudanar da zaɓe da fitowar masu kaɗa ƙuri'a.

Wannan ya sa tsaro ya zama wani muhimmin batu a siyasar yankin, musamman wajen fahimtar dalilin da ya sa a wasu lokuta yawan fitowar masu zaɓe ke kasancewa ƙasa da abin da ake tsammani.

Tsarin goyon bayan ɗan takara ɗaya

Wani abu da yankin Kudu maso gabashin Najeriya ya bambanta da sauran takwarorinsa shi ne keɓance kansu ga zaɓen ɗan takara guda, wanda a acewar Dakta Kabiru Sufi, wani abu ne da su gare su ɗin ya ba su damar bin alƙibla ɗaya da kuma amincewa da junasu sai dai "yana da naƙasu wanda ya kan iya jawo musu tsangwama a wasu wuraren da za ga su mutane ne masu ƙabilanci, wanda wannan zai sa a ƙi yarda da su da ɗan takarar nasu".

To sai dai a tsarin zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya, ɗan takara ba ya buƙatar samun rinjaye a yanki guda kawai. Don haka, samun gagarumin goyon baya a Kudu maso Gabas na iya samar da muhimmiyar fa'ida, amma samun tasiri a matakin tarayya yana buƙatar dangantaka da masu zaɓe da ƙungiyoyin siyasa daga sauran sassan ƙasar.

Wannan shi ne babban abin da zai iya ayyana makomar siyasar Kudu maso Gabas. ko za ta mayar da ƙarfin tattalin arzikinta, yawan jama'a, ƙuri'un zaɓe da tasirin diaspora zuwa ƙawance mai faɗi a matakin ƙasa, ko kuma siyasar yankin za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi musamman a cikin iyakokinsa.

A sakamakon haka, Kudu maso Gabas na da muhimmiyar rawa a tsarin siyasar Najeriya, amma girman tasirinta na gaba zai dogara ba kawai kan yawan ƙuri'un da take da su ba, har ma da ikon gina alaƙa da sauran yankuna, samun wakilci a manyan cibiyoyin gwamnati da kuma haɗa ƙarfin siyasa da tattalin arzikin yankin.