Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasu mutane suka kashe ɗan'uwansu suka jefa gawar a masai
An kama wasu mutane a yankin Hadiyya da ke tsakiyar ƙasar Habasha (Ethiopia) da ake zargi da kashe ɗan'uwansu sannan suka jefa gawarsa cikin masai.
An ce lamarin ya faru ne shekara 11 da suka gabata, kuma ƴan sanda sun shaida wa BBC cewa sun kama wasu ƴan uwa bisa zargin hannu a kisan bayan samun bayanai game da lamarin.
An kashe Dettamoo Ergodoo Ali a shekarar 2007, sannan aka jefa gawarsa cikin ramin bayan gida.
Ƴansanda sun ce bayan shekara 11 da faruwar lamarin, sun kama mutum shida da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da mahaifiyar mamacin da kuma uku daga cikin ƴan'uwansa, baya ga wasu mutane.
Kwamandan ofishin ƴansanda na Homachoo a yankin Hadiyya, Sufeto Addisuu Zakkiyos, ya shaida wa BBC yadda aka ɓoye lamarin tsawon shekaru 11 da kuma abin da binciken ƴansanda ya gano.
Ya ce: "Wanda ake zargin ya bayyana a gaban kotu, inda ya amsa laifin ba tare da an tilasta masa ba, kuma ya faɗi gaskiya a kotu."
Ɗaya daga cikin ƴan'uwan mamacin ma ya amince cewa laifin ya faru ne a shekarar 2007.
Sun bayyana mutanen da suka shiga cikin aikata laifin da kuma rawar da kowane mutum ya taka.
Kodayake babu cikakken bayani kan abin da ya haddasa saɓanin da ya kai ga aikata laifin a lokacin, Sufeton ya ce: "Muna kyautata zaton cewa lamarin yana da alaƙa da wasu muradun kashin kai."
Ya ƙara da cewa mamacin da waɗanda ake zargi da kashe shi duk ƴangida ɗaya ne.
An tono gawar mamacin domin gudanar da binciken kimiyya na likitocin shari'a (forensic examination).
Ya ce za a fitar da ƙarin bayanai idan sakamakon binciken ya kammala, amma yana da zaton cewa an aikata kisan ne da dare.
Ya ce: "Akwai alamu da ke nuna cewa an kashe shi ne a inda yake kwance.
A matsayina na jami'in binciken manyan laifuffuka, abin da na fahimta shi ne lokacin da aka tono gawar, wandon da yake sanye da shi yana nan manne da ƙasusuwansa da kuma wurin da ya kwanta."
Ana zargin cewa ƴanuwansa ne suka aikata kisan. Wasu daga cikin waɗannan mutanen sun amsa laifin tare da bayyana waɗanda suka aikata shi da kuma yadda aka aiwatar da kisan.
"Mun kuma yi ƙoƙarin tattara shaidu daga al'umma. Akwai tsoratarwa da aka yi wa mutane domin hana bayanai fitowa fili. Misali, ɗaya daga cikin ƴan'uwan mamacin ta ce an gargaɗe ta kada ta yi magana kan lamarin," in ji jami'in ɗan sandan.
Saboda haka, jami'an bincike sun ce ɗaya daga cikin shaidun muhalli da suka yi amfani da su wajen binciken lamarin ita ce bayanin da ƴar'uwar mamacin ta bayar.
Jami'in ya kuma ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ya bayar da shaida kan yadda aka aikata laifin a kan mamacin.
A cewarsa, an yi wa mamacin duka sau da dama a kansa da ƙafafunsa har sai da ya mutu.
Lokacin da BBC ta tambayi yadda aka gano wannan laifi bayan an ɓoye shi tsawon shekara 11, Sufeto Addisuu Zakkiyos ya ce asirin kisan ya tonu ne bayan wasu daga cikin 'yan uwan da ake zargi da hannu a lamarin suka samu saɓani, kuma a yayin da suke musayar kalaman zagi ne bayanan suka fito fili.
Ya ce matar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi tana da masaniya kan abin da ya faru.
A wani lokaci, ta samu rashin jituwa da wasu daga cikin iyalan, lamarin da ya rikiɗe zuwa gardama.
A cewarsa, "A yayin gardamar, sun ce wa matar: 'Kun kashe ɗan'uwanku kuma kun ɓoye shi, amma za mu sa a tono gawarsa.' Wasu mutane da suka ji wannan tattaunawa ne suka kai rahoto ga ƴansanda."
Sufeton ya ce bayan samun wannan bayani, ƴansanda suka fara bincike, inda har mahaifiyar mamacin ta zama daga cikin waɗanda ake zargi.
Ya ce ana zargin cewa lokacin da ake kashe mamacin ta yi shiru, sannan kuma ta kasance tana da masaniya lokacin da aka jefa gawarsa cikin ramin masai.
Ya ƙara da cewa mutum bakwai ne ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da mahaifiyar mamacin, ƴayanta da wasu danginsu.
Sai dai ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin baya cikin ƙasar, domin bayanan da suke da su na nuna cewa ya tafi Afirka ta Kudu ne bayan aikata laifin.
Ya ce tuni sun kama mutum shida, ciki har da mahaifiyarsa, wasu daga cikin 'yan uwansa da kuma wasu danginsa.
Jami'in ya kuma ce an tono gawar mamacin bisa tanadin doka tare da taimakon ƙwararrun masu binciken kimiyyar shari'a.
Bayan an tono gawar, an fara tabbatar da cewa ƙasusuwan da aka samu na mutum ne, kafin daga bisani a gudanar da ƙarin bincike domin gano cikakkun bayanai kan yadda mutuwar ta faru.
Yadda aka ɓoye labarin kisan har tsawon shekara 11
Mamacin matashi ne a lokacin da aka kashe shi. Ƴansanda sun ce mutanen da ake zargi da hannu a kisan sun kasance suna muzguna masa tun kafin faruwar lamarin.
Sufeto Addisuu Zakkiyos ya ce: "Tun kafin in zo wannan gari na fara aiki da rundunar 'yan sanda ta gunduma, na san cewa a shekarar 2006 wasu daga cikin 'yan'uwansa sun sa aka kama wannan matashi."
Ya ce alamu na nuna cewa kusan dukkan iyalan suna gallaza wa matashin, lamarin da ka iya zama dalilin da ya sa suka haɗa kai wajen ɓoye bayanan da suka shafi kisan.
"Lokacin da lamarin ya faru, an kai rahoto ga wasu jami'an ƙaramar hukuma da ke aiki a yankin a lokacin. Mutumin da ya karɓi bayanin ya fara zargin akwai matsala, sai ya tambaya inda matashin yake. Daga nan sai aka ɓoye gaskiyar lamarin ta hanyar cewa ya shiga aikin soja ne kuma ya bar yankin," in ji shi.
Sufeto Addisuu ya ce daga ƙarshe asirin kisan ya tonu ne bayan saɓani da ya ɓarke tsakanin wasu daga cikin 'yan'uwan mamacin biyu da matansu, wanda ya sa bayanan da aka daɗe ana ɓoyewa suka fito fili.