Shugaba Tinubu ya nemi a gudanar da sahihin bincike kan mutuwar matasa 37 a jihar Neja

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakke kuma sahihin bincike, game da mutuwar mutanen da ake zargin suna hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, wadanda hukumar Sibil Defens ta tsare a birnin Minna na jihar Neja.

Umarnin na shugaban Najeriyar yana zuwa ne yayin da dangin mamatan ke ci gaba da bayyana damuwa game da rasuwar masu hakar ma'adinan

Wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana alhini da ta'aziyyarsa game da rasuwar masu hakar ma'adinan a jihar Neja.

Ya kuma umarci hukumomin duk da suka kamata a kan lallai ilalla su gaggauta gudanar da cikakken binciken da ya dace, ba tare da wata balulluba ko coge ko kuma son zuciya ba.

Domin a gano yadda aka yi kamen, da halin da suke ciki yayin da aka kama su a kai su kurkuku, da adadin mutanen da aka tsare a ciki, da kula da lafiyarsu da kuma abin da ya yi sanadin mutuwar tasu.

Kuma binciken ya kasance bisa doka da girmama hakkin dan Adam.

''Ran duk wani dan Najeriya yana da muhimmanci, kuma bai kamata wani dan kasar ya rasa ransa yayin da yake tsare a kurkukun gwamnati ba, sakamakon sakaci da cin zarafi, da ketta hakkin bil'Adama, da kuma wasarere da aiki da gangan'' in ji shi.

Wannan sanarwa na zuwa ne yayin da 'yan uwan mutanen da suka rasa rayukansu a tsare, suke ci gaba da bayyana jimami da kakabin abin da ya auku

A dayan bangaren Gwamanan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ce ana gudanar da bincike kan gawarwwakin matasan su kusan arbain da suka mutu .

Gwamnan ya shaidawa BBC cewa sakamakon binciken zai fito nan da kwanaki biyar zuwa makonni uku masu zuwa .

Ya ce suna son su gano abinda ya janyo mace macen bayan zarge- zargen da ake yi akan cewa mutuwar matasan ta nada alaka da rashin samun iska da kuma feshin wani sinadari da aka yi mu su a dakin da ake tsare da su.

''Wadanda suka rayu sun ce an sa su a kurkuku kuma suna da yawa a cikin dakin, kuma isa ya gagaresu, akwai kuma wasu dake cikin wani daki, maza da mata , ba abinda ya samesu, ba bu wanda ya mutu a ciki''

''Da mu ka ga gawarwwakin wasu daga cikinsu, fatarsu ta ɗaye,wasu suna da kumfa a bakinsu da jini a hancinsu kuma wannan ya nuna cewa ko guba na ci ko guba na sha ko guba na tonon kasa da suke yi ko akwai wani sinadarin da suka hadu da shi yayin da suke hakar ma'adinan'' in ji shi.

Gwamnan ya ce kwamitin binciken da suka kafa shi ne zai gano abinda ya janyo mutuwar matasan yayin da ake tsare da su.