Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashe biyar da likitocinsu suka mamaye Birtaniya
Yayin da ƙasashen duniya musamman na Afirka ke kokawa dangane da matsalolin lafiya masu alaƙa da ƙarancin likitoci, su kuwa ƙasashe musamman na Turai bakinsu har kunne saboda yadda likitocin ƙasashe matalauta ke tururuwa neman aiki a can.
Wata ƙididdiga da NHS Million, wata ƙungiya mai fafutuka ta fitar bayan nazari a game da likitocin da ke aiki a hukumar lafiya ta Birtaniya NHS ta ce aƙalla akwai dubban likitocin ƙasashen waje waɗanda ke aiki a Birtaniyan.
Masana na ganin cewa girman ya kai yadda idan aka wayi gari likitocin ƙasashe masu tasowa sun bar Birtaniya, to ƙasar za ta fuskanci matsalar kiwon lafiya irin wadda ƙasashe masu tasowa ke fuskanta a fannin kiwon lafiya yanzu haka.
A bisa ƙididdigar NHS Million, Najeriya tana a matsayi na shida a jerin ƙasashen da suka fi yawan likitoci da ke aiki a Birtaniya, inda ta ke bin bayan ita kanta Birtaniya(1) da India (2) da Philippines (3) da Ireland (4) da kuma Poland (5), yayin da hakan ke nufin cewa daga nahiyar Afirka Najeriya ce kan gaba a yawan likitoci masu aiki a Birtaniya.
Ƙididdigar na nuni da gagarumar gudunmuwar da ƙwararrun Najeriya ke bayar wa a fannin kiwon lafiya a Birtaniya, amma hakan na faruwa ne a yayin da ake ƙara nuna damuwa kan ƙarancin ma'aikatan lafiya a Najeriya.
Jerin ƙasashen Afirika masu yawan likitoci a Birtaniya
A bisa ƙididdigar ta NHS Million waɗannan ƙasashen Afirika 5 ne kan gama wajen yawan likitoci da suka koma Birtaniya suna aiki, duk da buƙatar su da ake yi a ƙasashen su na asali:
- Najeriya - 10,494
- Zimbabwe - 4,780
- Ghana - 3,395
- Masar - 2,895
- Afirika ta Kudu - 1,829.
Martanin ƙwararrun likitoci a Najeriya
Wannan batu dai ya ja hankalin masana a ciki da wajen nahiyar Afirika, inda da dama ke bayyana damuwa kan matsalar da ficewar likitocin Afirika ke janyo wa a fannin kiwon lafiyar nahiyar.
Farfesa Bala Audu, shugaban jami'ar kimiyya ta Azare ya shaidawa BBC cewa ''kashi ɗaya bisa uku na likitocin Najeriya suna Birtaniya, kuma idan aka haɗa da waɗanda ke aiki a Amurka da ƙasashen Larabawa to kusan rabin likitocin Najeriya ba su a cikin ƙasar.''
Ya ce wannan barazana ce sosai ga tsarin kiwon lafiyar ƴan Najeriya saboda ya zo ne a daidai lokacin da ''yawan mutanenmu ke ƙaruwa, amma sai ga shi ma'aikatan kiown lafiya ke raguwa.''
Ya yi bayanin cewa mafi yawa abin da ke jan su ciwo can sun haɗa da ''neman ƙarin karatu da sani sabbin hanyoyin kimiyya da kuma yadda ake daraja su a Turai, abubuwan da ke masu wuyar samu a ƙasashen su na asali.''
Masanin ya kuma bayar da matakan da ya kamata a ɗauka domin shawo kan matsalar. Matakan sun haɗa da:
- Inganta albashi
- Samar da kayan aiki
- Inganta asibitoci
- Gaggauta aiwatar da yarjejeniya tsakanin gwamnati da likitoci