Mayakan Houthi sun kai hari a birnin Riyadh

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen sun ce sun kai hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami masu cin dogon zango a Riyadh babban birnin Saudiyya, da kuma wasu cibiyoyin makamashi da ke gabar Tekun Bahar Maliya ta ƙasar.

Mahukuntan Saudiyya sun ce sun kawarda wani makami mai linzami da aka harba zuwa Riyadh a farkon wannan rana, sai dai ba su tabbatar da wasu ƙarin hare-hare ko asarar rayuka ba.

Tun da farko, an ga wani baƙin hayaƙi na tashi daga tankunan man fetur da ke kusa da filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na babban birnin Saudiyyar, inda aka ɗan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na wani ɗan lokaci a ranar Asabar.

An ji ƙararrawar da ke ankarar da mutane kan hare-haren sama a babban birnin ƙasar karo na farko tun bayan da 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran suka ƙara yawan hare-harensu kan Saudiyya a watan Yuli.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ta ce naurar kharno makamai daga sararin samaniya ta dakile "ƙoƙarin kai wa fararen hula hare hare" a garuruwan Bish, Taif, Farasan da Yanbu.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafukan intanet, kakakin rundunar sojin Houthi, Yahya al-Sarea, ya ce an yi amfani da "adadi mai yawa na makamai masu linzami , da kuma jiragen sama marasa matuƙa" wajen kai hare-hare kan "wurare masu matuƙar muhimmanci" a Riyadh, da kuma cibiyoyin kamfanin mai da iskar gas na gwamnati, Aramco, a birnin Yanbu da ke gabar teku.

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a intanet, kakakin rundunar sojin Houthi, Yahya al-Sarea, ya ce an yi amfani da "adadi mai yawa na makamai masu linzami na ballistic da cruise, da kuma jiragen sama marasa matuƙa" wajen kai hari kan "wurare masu matuƙar muhimmanci" a Riyadh da kuma cibiyoyin kamfanin mai da iskar gas na gwamnati, Aramco, da ke Yanbu a gabar teku.

Ya ƙara da cewa hare-haren " martini ne ga munanan hare-haren da abokan gaba ke kaiwa" kan Sana'a babban birnin Yemen, wanda a halin yanzu ke ƙarƙashin ikon 'yan tawayen Houthi.

Tun da farko, Al-Sarea ya zargi Saudiyya da kai hare-hare ta sama har sau 300 a sassa daban-daban na Yemen cikin makon da ya gabata.

Yan tawayen Houthi na Yemen suna cikin yaƙin basasa da gwamnatin ƙasar da duniya ta amince da ita, wadda ke samun goyon bayan Saudiyya.

A cikin watannin baya-bayan nan, sun kai hare-hare kan wurare da dama a cikin Saudiyya, sannan a wannan makon sun ce su ne suka harbo wani jirgin yaƙin Saudiyya a sararin samaniyar Yemen.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, bisa wasu rahotanni da har yanzu ba a tabbatar da su ba daga majiyoyin soji na bangarorin biyu da ke yakin basasar Yemen, cewa fada tsakanin mayakan Houthi da dakarun gwamnati masu samun goyon bayan Saudiyya ya yi sanadin mutuwar mutane 48 a ranar Asabar.

A cewar kungiyar Houthi, an kashe mayakanta 31, yayin da majiyoyin gwamnati suka ce sojojinsu 17 ne suka rasa rayukansu, kamar yadda AFP ta ruwaito.

A ranar Juma'a, Hukumar Kula da kaura ta Duniya (IOM), wata hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon sabbin rikice-rikicen ya haura 104,796.