Barcelona na iya miƙa tayi kan Haaland, Liverpool ba ta da niyyar sallamar Wirtz

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Har yanzu Barcelona ba ta cire rai kan ɗan wasan gaban Manchester City, Erling Haaland ba, kuma za ta iya gabatar da tayi mai tsoka domin sayen ɗan wasan na Norway mai shekara 26 a shekara mai zuwa. (Football Insider)

Liverpool na sa ran samun tayin sayen ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Jamus, Florian Wirtz, a watan Janairu, amma ba su da niyyar barin ɗan wasan mai shekara 23 ya tafi. (Football Insider)

Arsenal na da matuƙar sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Brazil da Real Madrid, Endrick, a watan Janairu. Ana ta samun damuwa game da yawan lokacin wasa da matashin ɗan wasan mai shekara 20 ke samu a babban birnin ƙasar Spain. (Teamtalk)

Tottenham ta yi watsi da tayin da ƙungiyar Shabab Al Ahli ta Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi mata kan ɗan wasan gaban Brazil, Richarlison, mai shekara 29. (Ekrem Konur a shafin X)

Juventus da Atletico Madrid na sa ido kan Ɗan wasan gefe na Arsenal, Noni Madueke, mai shekarA 24, domin ganin yiwuwar ɗaukar sa a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu. (Football London)

Liverpool da Manchester City na zawarcin ɗan wasan baya na Real Sociedad da Venezuela, Jon Aramburu, mai shekara 24. (Teamtalk)

Ana tattaunawa kan sabbin kwantiragin ƴan wasan gaban Paris St-Germain, Ousmane Dembele (mai shekara 29), da Khvicha Kvaratskhelia (mai shekara 25), da Desire Doue (mai shekara 21). (L'Equipe)

Juventus na iya neman ɗaukar mai tsaron raga wanda ba shi da ƙungiya, bayan da ta rasa ɗan wasan Poland da ta ɗauka a matsayin aro, Kamil Grabara (mai shekara 27), sakamakon raunin tsokar gwiwa (ACL) da ya samu yayin atisaye a ranar Asabar. (Calciomercato)