Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce haɗakar siyasa ta "Rainbow Coalition" da Wike ya kafa?
A daidai lokacin da rikici ke ƙara rincaɓewa tsakanin gwamnonin APC da ministan Abuja, Nyesom Wike, hankali ya fara komawa kan ƙungiyar 'Rainbow Coalition" wadda ministan ke jagoranta.
Tun da farko dai haɗakar ta ƙara fitowa fili ne bayan gwamnonin APC sun zargi Wike da musu kutse duk da cewa shi ɗan jam'iyyar PDP ne.
Gwamnonin sun nuna cewa ba za su lamunci yadda a cewarsu Wiken yake amfani da ƙungiyar wajen goyon bayan ƴan takara a jihohinsu ba, suna masu cewa da farko ya yi alƙawarin cewa zai taimaka wa APC ne daga sama har ƙasa.
Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Nyesom Wike dai ya sake jaddada goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya nanata cewa bai taɓa yin alƙawarin cewa jam'iyyar PDP ba za ta tsayar da ƴan takara a zaɓen gwamna da majalisun dokoki ba.
Wike dai har yanzu yana jam'iyyar PDP ne, amma yake ta hanƙoron tabbatar da sake samun nasarar Bola Tinubu a babban zaɓe.
Ministan ya dai taka rawa wajen nasarar zaɓen Tinubu a 2023, inda ya jagoranci wasu gwamnoni biyar wajen yi wa jam'iyyarsu ta PDP tustsu wajen ƙin goya wa ɗan takararta a zaɓen wato Atiku Abubakar baya.
Mece ce ƙungiyar?
Rainbow Coalition wata sabuwar ƙawancen siyasa ce da ake dangantawa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadda ke ƙoƙarin haɗa ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A wata hira da BBC, Lere Olayinka, mai ba ministan Abuja shawara kan kafofin sadarwa da wayar da kan al'umma, ya ce ba lallai ne ƴan siyasar da ke cikin ƙawancen su bar jam'iyyunsu ba.
Ya ce kowace jam'iyya za ta iya tsayar da ƴan takararta a sauran zaɓuka, yayin da a zaɓen shugaban ƙasa za su mara wa Bola Tinubu baya ne domin ya sake samun nasarar lashe zaɓensa domin yi wa'adi na biyu.
A cewarsa, "akwai mambobin haɗakar da za su shiga wasu zaɓuka su fafata, amma a zaɓen shugaban ƙasa ta goyi bayan Tinubu. Haka kuma, ya ce akwai wasu ƴan siyasa da ba su da jam'iyya amma suke mara wa shugaban ƙasa baya da suka haɗu a haɗakar."
Ya bayar da misalin jihar Kwara, inda ya ce akwai wasu ƴan majalisar tarayya da ba su samu tikitin jam'iyyunsu ba, amma aka ba su damar tsayawa takara a PDP, "amma da tsarin cewa za su goyi bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa ne."
Olayinka ya kuma yi magana kan Rivers, inda ya ce a baya ana samun rikici wajen zaɓen ƴan takara a wasu jam'iyyu, amma a wannan karon, a cewarsa, an samu sauƙin gudanar da tsarin cikin lumana saboda haɗakar ta Rainbow.
Ya ce manufar ƙawancen ita ce a tsara tsarin siyasa ta yadda jam'iyyu daban-daban za su iya yin aiki tare ba tare da tilasta wa ƴan siyasar da ke cikinsu barin jam'iyyunsu ba.
Ya kuma kawo misalin Ekiti, inda ya ce ɓangaren PDP da yake cikinsa ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamna Ayo Fayose ya goyi bayan gwamnan da ke kan mulki na APC a zaɓen da ya gabata, abin da ya ce ya taimaka wajen samun nasararsa.
A Rivers kuwa, Olayinka ya ce shugabannin ƙawancen ne za su yi ƙoƙarin tsara yadda za a raba kujeru ga ƴan takara a ƙananan hukumomin.
"Hakan zai sa su yi la'akari da ɗan takara da ya fi fice a kowace takara sai a ce a zaɓe shi. Wannan zai sa APC ta samu, PDP ta samu kowa ma ya samu," in ji Mr Olayinka.
Ya ce ba su da matsala da kowa, kawai su dai burinsu shi ne a zaɓi Tinubu, sai kowa ya koma jiharsa ya fafata a jam'iyyar da yake a sauran zaɓuka.
Daga cikin ƴan siyasar da ake dangantawa da Rainbow Coalition akwai Nyesom Wike, Gwamnan Osun Ademola Adeleke, Gwamnan Anambra Charles Soludo, wanda ke da alaƙa da APGA, da Gwamnan Abia Alex Otti na Labour Party,kamar yadda Olayinka ya bayyana.
Tinubu na sane da "Rainbow Coalition" - Wike
A wani saƙon martani da ɗaya daga cikin masu magana yawun ministan, Lere Olayinka ya fitar, Wike ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana sane da haɗakar siyasarsa ɗin ta "Rainbow Coalition" da kuma dukkan ayyukansa na siyasa.
Wike ya bayyana hakan ne a daren Talata yayin wata hira da ya yi a shirin Prime Time na tashar Arise News.
Ya ce: "Babu wani abu da nake yi da ban sanar da shugaban ƙasa ba."
Ministan FCT ya bayyana cewa yana tattara goyon baya daga jam'iyyu daban-daban domin sake zaɓen shugaba Tinubu a shekarar 2027 ta hanyar abin da ya kira "Rainbow Coalition".
Ya kuma jaddada cewa goyon bayan da yake bayarwa ga Shugaba Tinubu ne kaɗai, ba ga jam'iyyar APC gaba ɗaya ba.
Wike, wanda jigo ne a jam'iyyar PDP, ya ce ba ya yin ayyukansa a ɓoye, domin kuwa shugaban ƙasa yana da cikakken bayani game da dukkan matakansa na siyasa.
Haka kuma, ya ce ba shi da alhakin bayyana kansa ga gwamnonin APC.
Ya ce: "Ba ni ne zan ba gwamnonin APC bayani ba."
Ya ƙara da cewa: "Idan mutane ba sa koya daga sauran mutane, ba za su ci gaba ba. Na ɗauki kwana 31 ina ƙaddamar da ayyuka a FCT, kuma hakan bai yi musu daɗi ba."
Da yake magana kan Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, Wike ya ce:
"Ya kamata Hope Uzodimma ya gode wa Allah cewa ba ni cikin APC. Hope yana tsoron komai ba komai."
Dangane da Jihar Rivers kuwa, Wike ya ce: "Saboda wannan haɗakar siyasa ta Rainbow Coalition, yanzu ba mu da fargabar zubar da jini a Rivers. Babu kuma shari'o'in da suka shafi ƴan takarar jam'iyya a Rivers kamar yadda ake gani a jihar Imo."
Da aka tambaye shi a ina kuma Shugaba Tinubu zai iya samun nasara a yankin Kudu maso Kudu, Wike ya amsa cewa:
"Hakan na iya faruwa a Jihar Bayelsa. Kusan dukkan PDP a can suna aiki ne domin shugaban ƙasa. Wanda ya kafa NDC ba shi ne ya kafa Bayelsa ba."
Me "Rainbow Coalition" ke nufi?
Ga lauya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Liborous Oshoma, Rainbow Coalition wata haɗaka ce ta siyasa da za ta yi amfani domin cimma muradun waɗanda suke cikinta.
Ya ce hakan ya nuna irin tasirin da Ministan Abuja ke da shi a cikin jam'iyyun PDP da APC, yana mai cewa irin wannan abu ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya.
"A baya mun ga jam'iyyun siyasa suna amincewa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a lokacin zaɓe. Abin da ke faruwa yanzu ma irin wannan ne, don haka ba wani abu ne da ya sha bamban sosai ba.
"A siyasar Najeriya, ba a cika amfani da aƙida ko manufar jam'iyya ba a mafi yawan lokuta. An fi amfani da muradun ƴan siyasa, shi ya sa ake cewa ƴan siyasa ba su da abokai ko maƙiya na dindindin."
Ya ce masu muradi iri ɗaya su ne ke haɗuwa suna jagorantar tafiya, "kuma shi ne ya sa ake ganin irin waɗannan haɗaka da sauye-sauye a alaƙar siyasa."