KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 5/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 5 ga watan Agustan 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Muslim Muhammad Yusuf

  1. An kama wani mutum da bindiga a wurin da Trump zai kai ziyara a California

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an tsaro a jihar California sun kama wani mutum ɗauke da bindiga a filin wasan golf mallakin shugaban Amurka Donald Trump gabanin ziyarar da shugaban zai kai wurin domin halartar wani taron tara kuɗaɗe na Jam'iyyar Republican.

    Masu bincike sun ce an kama mutumin, mai suna Jeanine John Tael da shekaru 38 ne a filin wasan da ke Rancho Palos Verdes tare da bindiga da kuma haramtattun alburusai.

    'Yansanda sun bayyana cewa an ga mutumin yana yawo a wurare daban-daban na filin wasan, yana ɗaukar hotuna da bidiyo tare da lura da shirye-shiryen tsaro da ake yi gabanin zuwan Trump.

    An kama shi ne ranar Lahadi, kuma a yanzu yana tsare yayin da yake fuskantar zargin ɗauke da bindiga a ɓoye da kuma mallakar haramtattun alburusai.

  2. 'Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu linzami sakamakon yaƙin Iran'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka CBS sun nuna cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin wasu muhimman makamai masu linzami bayan yawan amfani da su a yaƙin da aka yi da Iran.

    Wasu majiyoyi sun shaida cewa sojojin Amurka sun yi amfani da kusan dukkan makaman ATACMS a hare-haren da suka kai wa Iran lamarin da ya jawo damuwa kan adadin makaman da suka rage a ma'ajiyarsu.

    Rahoton ya kuma ce ana ƙara nuna damuwa kan raguwar makaman kariya na Patriot da THAAD.

    Sai dai jami'an Pentagon sun musanta cewa lamarin ya kai matakin barazana, suna cewa har yanzu Amurka na da isassun makamai da ƙarfin soja da za su ba ta damar kare muradunta da gudanar da ayyukanta a duk inda ake buƙata.

    Batun ya sake tayar da muhawara a Washington kan ko masana'antun tsaron Amurka za su iya ci gaba da samar da makamai cikin sauri idan aka shiga wani yaƙi mai ɗaukar dogon lokaci.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.