Me mabiya mazhabar Shi'a ke yi a Karbala?

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
A ranar 20 ga watan Safar na kowane wata ne mabiya mazahabar Shi'a daga ko'ina a faɗin duniya ke tattaki na jimamin kisan jikan manzon Allah SAW, Imam Hussain, a birnin Karbala na ƙasar Iraki.
Taron wanda ake yi wa laƙabi da "Tattakin Arbaeen" kuma ake yin sa ranar 20 ga watan Safar ya kasance cikar kwana 40 tun bayan kisan Imam Hussain ranar 10 ga watan Muharram.
To sai dai tattakin na farawa ne da yammacin ranar 19 ga wata inda kowace tawaga kan shiga hubbare ko kuma "haramin" Imam Hussain da na ɗan uwansa Abul Abbas domin jaje da addu'o'i.
Taron na Arbaeen shi ne taro na biyu mafi girma a duniya bayan wani taron Maha Kumbh Mela na mabiya addinin Hindi.
Alƙaluma daga Karbala sun nuna cewa mutum miliyan 20 zuwa 30 ke halartar wannan alhini a duk ranar 20 ga watan Safar - wata na biyu a addinin Musulunci, a kowace shekara.
Duk da cewa alƙaluman na sauyawa a duk shekara amma alƙaluma sun nuna cewa mutum miliyan 21 ne suka halarci taron a 2022, inda kuma a 2017 aka samu halartar mutum miliyan 30, kamar yadda hukumomin Al-Abbas Holy Shrine da Imam Hussaini Holy Shrine suka fitar.
BBC ta tattauna da wasu ƴan Najeriya da suka halarci tattakin na Arbaeen a Karbala kuma ga bayanan da suka bayar.

Asalin hoton, Getty Images
Tattaki zuwa Karbala

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
A ranar Arbaeen, miliyoyin mabiya mazhabar Shi'a suna yin tattaki zuwa birnin Karbala na Iraq domin tunawa da cikar kwanaki 40 bayan shahadar Imam Hussain.
Mabiya Shi'a suna yin tattakin Arbaeen zuwa Karbala daga sassa daban-daban na Iraq da ma wasu ƙasashe, amma mafi shahararren tattakin shi ne daga Najaf zuwa Karbala.
Mafi shaharar tattakin shi ne wanda ake yi daga:
- Najaf zuwa Karbala: Kimanin kilomita 80, inda masu tattakin ke tafiya a ƙafa na tsawon kwanaki biyu zuwa uku.
- Wasu kuma suna zuwa Karbala daga Baghdad, Basra, da sauran biranen Iraq.
- Haka kuma, akwai masu tattakin daga ƙasashe daban-daban kamar Iran, Pakistan, Lebanon, Afghanistan, da sauran sassan duniya irin su Najeriya da Ghana suna shiga tattakin kafin su isa Karbala.

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
Me ya sa ake tattaki daga Najaf zuwa Karbala?

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
Duk da cewa akwai hanyoyi daban-daban na shiga Karbala, amma tattakin daga Najaf zuwa Karbala shi ne mafi girma kuma mafi shahara, domin Najaf na ɗauke da hubbaren Imam Ali, wanda Shi'a ke yi wa ziyara kafin su nufi Karbala.
Bisa al'adar Arbaeen, masu tattakin da dama kan fara ziyararsu a Najaf, inda suke yin addu'a a hubbaren Imam Ali, sannan su yi tattaki a ƙafa zuwa Karbala domin tunawa da sadaukarwar Imam Hussain da kuma nuna biyayya ga manufofinsa na adalci da tsayawa kan gaskiya.
Yadda mabiya Shi'a ke kallon tattakin Arbaeen

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
Mabiya Shi'a a faɗin duniya na ganin wannan tattaki a matsayin:
- Ibada da kusanci ga Allah.
- Nuna soyayya da girmamawa ga Imam Hussain.
- Tunawa da wahalhalun da Imam Hussain da iyalansa suka sha a Karbala.
- Hanyar haɗa kan mabiya Shi'a daga sassa daban-daban na duniya.
Me ya faru da Imam Hussain a Karbala?

Asalin hoton, Isma'eel Albabawee
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tarihi ya nuna cewa Husseini Ibn Ali Ibn Abi Talib ya tashi ne tare da tawagarsa daga Kufa a kan hanyarsu ta zuwa Hijaz domin karɓar ragamar halifancin Musulunci.
A wancan lokaci Yazid bin Mu'awiyah shi ne khalifa bayan rasuwar mahaifinsa Mu'awuya Ibn Abu Sufyan.
Sai dai wakilan Yazid a Basra da Kufa sun tura dakarunsu waɗanda suka tursasa wa Husseini da tawagarsa karkata akala zuwa Karbala.
A can ne kuma aka yi musu ƙawanya, aka hana shi tsallaka kogin Alfuraat, sannan aka kashe Hussaini da iyalansa da mabiyansa a ranar 10 ga watan Muharrama na shekara 61 bayan Hijira.
A lokacin yaƙin an kama mata da yara da yawa, ciki har da ƴar'uwarsa Zainab da ɗansa Ali Zayn al-Abidin, wanda ɗaya ne daga cikin imamai 12 na Shi'a.
A cikin ruwayoyin tarihi, an fi danganta jagorancin rundunar da ta yi yaƙi da Imam Hussain ga Umar bn Sa'ad, yayin da aka ambaci Shimr bn Dhil-Jawshan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a kashe shi.
Kisan da aka yi wa Husseini da tawagarsa da kuma kama iyalansa ya kawo sauyi sosai a cikin mabiya Shi'a. Wannan ne ya sanya ake tunawa da lamarin a duk shekara.
Darussan da wannan lamari ya koyar ya shafi sauran abubuwan da suka biyo baya a tarihin Musulunci a ɓangaren addini da kuma a siyasa.
Haramta bukukuwan tunawa da kisan Husseini

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin mulkin tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussain, hukumomin ƙasar sun ɗauki matakan dakushe al'umma mabiya mazhabar Shi'a, waɗanda su ne masu rinjaye a ƙasar daga gudanar da bukukuwan.
Sai dai wannan ba shi ne na farko ba a tarihi. A baya an sha haramta wa mabiya Shi'ar gudanar da taruka da bukukuwansu.
Masana tarihi sun ce an sha haramta tarukan Ashura a zaman mulkin Mulukiya na Iraqi.
Sai dai daga baya an dawo da tarukan a lokacin daular Ottoman, sa'ilin da daular wadda ke da cibiya a Istanbul na Turkiyya ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Iran bayan gushewar mulkin Mulukiya.
Amma an samu karo uku da aka yi yunƙurin haramta tarukan na Ashura.
Ra'ayi na siyasa na daga cikin manyan dalilan da suka sanya shugabanni ke ɗaukar matakin taƙaita tattakin, a yunƙurin hana yin amfani da su domin adawar siyasa.
A shekarar 2003 lokacin da aka kawar da gwamnatin Saddam Hussain sa'ilin da Amurka da ƙawayenta suka mamaye Iraqi, an samu sauyin lamurran siyasa.
Ƴan Shi'a sun samu muƙamai da yawa na gwamnati, wannan ya sanya aka kawar da manufofin da aka yi amfani da su a baya wajen mayar da su gefe.
Bayan zaɓukan majalisar dokokin Iraqi da aka gudanar, jam'iyyun ƴan Shi'a sun mamaye gwamnati, duk da cewa akwai na Sunni da kuma Kurdawa da su ma suka samu kujeru a gwamnatin.
Tun daga lokacin ne aka ci gaba da gudanar da bukukuwa ba tare da takurawa ba.











