Jihohin Najeriya mafiya sauƙi da kuma mafiya tsadar kayan abinci

Kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci, hukumar tattara alƙaluma ta Najeriya, NBS a wannan karon ma ta saki wani rahoto da ke nuna jihohin da suka fi sauƙi da waɗanda suka fi tsadar abinci a fadin ƙasar.

Rahoton wanda NBS ta saki a ranar 24 ga watan Yunin da ya gabata ya tattaro alƙaluma ne na watan Mayu daga ƙananan hukumomin Najeriya 774.

Rahoton ya kasa abin gida biyu - jihar da aka fi samun arahar nau'in abinci da kuma wadda aka fi samu tsadar kayan abincin.

Tumatur

Tumatur

Asalin hoton, Getty Images

Alƙaluman na NBS sun nuna cewa farashin tumatir mai nauyin kilogiram ɗaya a watan Mayu ya kai naira 1,392.71.

Sai dai kuma hukumar ta ce farashin na tumatur ya fi sauƙi a jihar Ekiti inda aka sayar da shi a kan naira 1,017.

Farashin tumaturin kuma ya fi tsada a jihar Legas inda aka rinƙa sayar da shi naira 1,974.81.

Shinkafa

Shinkafa

Asalin hoton, Getty Images

Dangane kuma da shinkafa, jihar Bauchi ce ta fi kowacce jihar Najeriya arahar ta inda alƙaluman hukumar suka nuna an saye ta kan naira 1,570.72 a kan kowane kilogiram a watan na Mayu.

Ita kuma jihar Ekiti ita ce ta fi kowacce tsadar shinkafar a watan na Mayu inda mutanen jihar suka saye ta a kan nairan 2,189.76.

Wake

Wake

Asalin hoton, Getty Images

Shi kuma wake ya fi araha a jihar Taraba inda aka sayar da shi a kan naira 760 kowane kilogiram ɗaya.

Jihar Oyo ita ce wadda ta fi kowacce tsadar waken inda aka sayar da shi a kan naira 1,941.78

Doya

Doya

Asalin hoton, Getty Images

Ita kuma doya kamar yadda alƙaluman hukumar NBS suka nuna a watan na Mayu ta fi sauƙi a jihar Jigawa inda aka rinƙa sayar da guda ɗaya mai nauyin kilogiram ɗaya a kan naira 1,998.82.

Amma a jihar Delta, doyar ta fi ko'ina tsada inda aka rinƙa sayar da ita a kan naira 2,750.50.

Albasa

Albasa

Asalin hoton, Getty Images

Dangane kuma da kayan gwari, albasa ta fi araha a jihar Nassarawa da ke tsakiyar Najeriya, inda aka rinƙa sayar da ita a kan naira 850 a kan kowace albasa mai nauyin kilogiram ɗaya.

A Abia kuma inda nan ne jihar da albasar ta fi tsada a Najeriya, an rinƙa sayar da ita a kan naira 2,199.07

Nama

Nama

Asalin hoton, Getty Images

A jihar Anambra an rinƙa sayar da naman a kan naira 8,856.65 a watan Mayun 2026 abin da ya sa jihar ta fi kowacce tsadar nama a watan na Mayu.

Burodi

Burodi

Asalin hoton, Getty Images

Burodi ya fi sauƙi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya inda aka rinƙa sayar da burodun mai nauyin giram 450 a kan naira 1,026.7.

A jihar Adamawa kuwa wanda ita ma ta kasance a arewa maso gabashin ƙasar, burodin ya fi tsada fiye da kowacce jiha inda ake sayar da shi akan naira 1,970.

Man ja

Manja

Asalin hoton, Getty Images

Da yake shi man ja a kudancin najeriya ake yin sa, a yankin ne aka samu jihohin da man ya fi tsada da ma araha.

Jihar Abia da ke kudu maso gabashi ce ta ciri tuta wajen sauƙin farashin man jan inda ake sayar da kwalbar man a kan naira 2,025. 75

Jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya ta zamo wurin da manjan ya fi ko'ina tsada, inda ake sayar da shi akan naira 2,812.07.

Fulawa

Fulawa

Asalin hoton, Getty Images

Alƙaluman na NBS sun nuna cewa ana sayar da kilo biyu na fulawa a kan naira 3,090.1 a wasu jihohin Najeriya inda nan ne farashin fulawar ya fi sauƙi.

Amma fulawar ta fi tsada a jihar Kwara inda aka sayar da ita akan naira 4,663.25.

Gari

Gari

Asalin hoton, Getty Images

Gari wanda yake cikin manyan cimakar mutanen Najeriya musamman kudanci ya fi araha a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya inda aka sayar da kilo ɗaya kan naira 521,1.

Abia da ke kudu maso gabashin Najeriyar ta zama wurin da garin ya fi ko'ina tsada a watan Mayun da ya gabata, inda aka sayar da kowane kilo ɗaya na garin a kan naira 1,075.71.