Ko shan lemun kwalba mai sa kuzari na da illa ga matasa?

Asalin hoton, Getty Images
A yau, shan lemun da ke sa kuzari da ake kira da 'energy drinks' ya zama ruwan dare a birane da ƙauyuka da dama na Najeriya da ƙasashen yammacin Afirka.
Ana ganin nau'ukan lemun a makarantu da wuraren aiki da tashoshin mota da wuraren shakatawa da kantunan sayar da abinci, inda mutane musamman matasa, ɗalibai, yara har da ma manya ke shan su domin samun ƙarin ƙarfi da kuzari da rage gajiya ko kuma hana su bacci musamman lokacin karatu da dai sauransu.
Sai dai masana lafiya na ganin cewa mutane da dama na dogaro da waɗannan kayan sha ba tare da cikakken sani ba game da tasirinsu ga lafiya.
Dalilin hakane BBC ta tuntuɓi wani likitan abinci, Dr. Bello Adamu domin bayani kan gaskiyar abin da ke cikin kayan sha masu ƙara kuzari da yadda suke shafar lafiyar bil'adama.
Mene ne a cikin ababen sha masu ƙara kuzari?
Likitan abincin ya bayyana cewa akwai wasu sinadaran da ke cikin kayan sha masu ƙara kuzari waɗanda ke iya yin illa ga lafiyar mutum, kamar haka:
Sinadarin 'Caffeine'
Samun wannan sinadari (Caffeine) mai yawa fiye da abin da jiki ke buƙata a lokaci ɗaya - inda ya ce a wasu lokuta, kwalba ɗaya na iya kai wa adadin caffeine da ya wuce kofi biyu zuwa uku na shayi mai ƙarfi. Wannan shi ne mafi tasiri a cikinsu kuma yana iya haifar da matsala ga zuciya da bacci," in ji shi.
Sinadarin 'taurine'
Wannan sinadari ne na 'amino acid' a turance, da ke taimaka wa aikin zuciya da jijiyoyi. Ana saka shi a cikin ababen sha masu ƙara kuzari domin taimaka wa jiki ya jure gajiya, ko da yake ba shi kaɗai ne ke bayar da kuzari ba.
Sinadarin 'Guarana'
Wannan sinadarin na ƙunshe da 'caffeine' mai ƙarfi. Idan aka haɗa shi da 'caffeine' na ainihi, zai iya sa yawan 'caffeine' ya wuce kima, wanda ke ƙara haɗarin bugun zuciya da rashin natsuwa.
Sukari mai yawa
Wannan yana ƙara nauyi, yana tayar da haɗarin ciwon suga, tare da gajiyar da jiki bayan "kuzarin farko da mutum ya ji."
Illolin shan lemu mai ƙara kuzari
A cewar Dr. Bello, illolin shan waɗannan lemuka ba sa bayyana nan take. Suna taruwa ne a hankali.
Ya lissafo illolin shan lemun ƙara kuzari kamar haka;
- Yana iya jawo bugawar zuciya fiye da kima
- Yana lalata tsarin bacci (rashin barci)
- Yana iya haifar da tashin hankali da rashin natsuwa
- Yawan shan lemon kwalba mai ƙara kuzari na ƙara haɗarin hawan jini
- Yana iya jawo ciwon kai da jiri
- Yana iya sa mutum ya dogara da sinadarin 'caffeine' sosai (addiction)
- Yawan sukari na iya ƙara nauyi da haɗarin ciwon suga
- Yana iya shafar aikin ƙwaƙwalwa, musamman ga matasa
- Yana iya jawo matsala ga hanta da ƙoda idan aka sha da yawa
Likitan abinci ya ƙara da cewa: "A matasa musamman, ƙwaƙwalwa tana ci gaba da girma, don haka yawan sinadarin 'caffeine' na iya shafar yadda suke mayar da hankali kan abubuwa."
Ko shan lemun ƙara kuzari na da alfanu?
Dr Bello ya kuma lissafo amfanin lemon ƙara kuzari kamar haka:
- Ƙara kuzari na ɗan lokaci
- Taimakawa wajen tsayawa da ido a buɗe (alertness)
- Yana rage jin gajiya na gaggawa
- Taimakawa direbobi ko masu aiki na dare ci gaba da aiki amma na ɗan lokaci
- Yana iya ƙara ƙarfin mayar da hankali na ɗan lokaci saboda sinadarin 'caffeine'
Waɗanne gabobi ne suka fi shan wahala?
Likitan abincin ya bayyana cewa zuciya na ɗaya daga cikin gaɓoɓin da suka fi fuskantar matsala, domin sinadarin 'caffeine' na iya hanzarta bugunta fiye da yadda ya kamata.
Sauran gaɓoɓin da suka fi shan wahala sun haɗa da:
- Ƙwaƙwalwa na fuskantar matsalar rashin bacci da rage natsuwa, wanda ke shafar karatu da tunani.
- Hanta da ƙoda sukan yi aiki fiye da kima wajen tace sinadarai, musamman idan ana yawan sha.
- Ciki da tsarin narkar da abinci kuma na iya samun matsala kamar kumburi ko rashin jin daɗi.
Yadda ya kamata a sha lemu mai ƙara kuzari
Dr. Bello ya ce ba wai masana kiwon lafiya na hana shan lemun kwalba mai ƙara kuzari gaba ɗaya ba ne amma su kiyaye yadda suke sha.
Likitan abincin ya bayar da wasu shawarwari game da yadda ya kamata a sha lemun waɗanda suka haɗa da:
- Kada a sha fiye da kofi ɗaya zuwa biyu a rana
- Kada a haɗa shi da giya ko wasu abubuwan da ke motsa jiki
- A guji sha kafin barci
- A guji amfani da shi a matsayin maye gurbin bacci ko abinci
- Matasa ƙasa da shekara 18 su guji shan waɗannan lemukan
- A rika shan ruwa sosai domin rage tasirin sinadarin 'caffeine' a jiki
Amma likitan ya ce "gaskiya mafi kyau ita ce a rage ko a guje ma shan su. Matasa ba su da cikakken jiki da zai iya jure yawan caffeine. Abin da ake kira kuzari na ɗan lokaci, yawanci yana zuwa da gajiya mai tsanani daga baya ne kawai."









