Me ya faru tsakanin maiɗakin El-Rufai da jami'an hukumar ICPC?

Iyalan El-Rufai

Asalin hoton, IG Wala/FB

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai sun koka game da yadda ake tafiyar da shari'arsa da ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya.

Kamar yadda maiɗakinsa Hajiya Asiya El-Rufai ta bayyana, "ana tauye haƙƙin mijin nasu da hana shi samun ƴancinsa" na ɗan'adam.

Ta ce ya kamata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar mijinta ya samu adalci kan yadda ake tafiyar da shari'arsa, domin acewarta El-Rufai bai cancanci hakan daga wajensa ba.

Hajiya Asiya ta yi waɗannan kalamai ne tare da matar El-Rufai ta biyu, Aichatou, a inda ta mayar da martani kan kama likitan da ke kula da lafiyar mijinta, Farfesa Bello Abubakar, abin da hukumar ta ICPC ta tabbatar a ranar Talata.

Saƙon da iyalan El-Rufai suka aika wa Tinubu

Da take ganawa da manema labarai a gidanta da ke Abuja, Hajiya Asiya ta ce iyalansu ba sa roƙon Shugaba Tinubu ya tsoma baki a shari'ar El-Rufai ko ya dakatar da gurfanar da shi a gaban kotu.

Sai dai ta ce abin da suke nema shi ne a tabbatar da tsohon gwamnan ya samu haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada ga kowane ɗan ƙasa, ciki har da samun kulawar likita, damar ganin 'yan uwansa da lauyoyinsa, da kuma beli bisa sharuɗɗan da suka dace.

Hajiya Asiya ta ce ta yi wa Tinubu kamfen a sassa daban-daban na jihar Kaduna domin ganin ya samu nasara zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma mijinta ma ya tsaya masa tsayin daka.

"Mai Girma Shugaban Ƙasa, na yi maka kamfen. Na zagaya lungu da saƙo na jihar Kaduna saboda kai. Mijina ya tsaya maka. Shin wannan ne abin da za a saka mana da shi?" in ji ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta ƙara da cewa, a ganinta, Shugaba Tinubu na da ikon tabbatar da an mutunta haƙƙoƙin mijinta.

"Kana iya dakatar da duk abin da ake yi idan ka furta kalma ɗaya. Mun yi imanin kai uba ne, kuma mun san za ka iya tausaya mana."

"Ba wai muna roƙon ka hana a gurfanar da shi ba ne. Muna so ne kawai a ba shi haƙƙoƙin ɗan'adam da kundin tsarin mulkin da ka rantse za ka kare ya tanada. A ba shi belin da zai iya cikawa. Idan yana da laifi, kotu ce za ta yanke hukunci, idan kuma ba shi da laifi, kotu ce za ta tabbatar da hakan."

Hajiya Asiya ta ƙara da cewa ci gaba da tsare El-Rufai tare da hana shi ganin likitocinsa da ƴan'uwansa ya jefa su cikin damuwa.

"Mu iyalansa muna cikin matsananciyar damuwa. Kullum muna rayuwa cikin fargabar mu wayi gari mu ji wani mummunan labari," in ji ta.

"A ganina, abin da ake yi ya fi kama da jefa damuwa ga Malam da kuma iyalansa domin an san abin yana taɓa tunaninmu. Suna ganin idan sun wulaƙanta mu, suka tauye mana mutunci, suka kuma sa mu cikin fargaba a ko da yaushe, hakan zai shafi Malam."

"Ba a barin El Rufa'i ya ga likitocinsa"

Hajiya Asiya ta yi zargin cewa ana hana El-Rufai samun kulawa daga likitocinsa na kashin kansa, inda ta ce an ƙara tsaurara ƙa'idojin ganin sa da ƴan'uwansa.

Ta kuma bayyana damuwa kan wani rahoton lafiya da ake zargin Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja ya fitar, inda ta ce ya kamata a binciki sahihancin rahoton da kuma yadda aka fitar da shi ta hannun ƙwararren likitan da sunansa ya bayyana a cikinsa.

Iyalan El-Rufai sun ce, tsauraran matakan da ake ƙaƙaba masa ya sa ba zai iya samun damar shirya wa fuskantar shari'ar da ake masa domin kara kansa ba.

"Ba wai muna tsoron kare kanmu a gaban shari'a ba ne, amma muna son a yi mana shari'a cikin adalci. Muna son a ba mu dama a saurare mu. Malam ba zai iya shiryawa yadda ya kamata domin kare kansa ba muddin yana tsare kuma an ƙaƙaba masa takunkumi kan damar ganawa da lauyoyinsa."

Jam'iyyar ADC ta ɓara

Jam'iyyar adawa ta ADC da tsohon gwamnan Malam Nasir El-Rufai ke cikinta ta bayyana damuwarta kan yadda ake tafiyar da shari'arsa.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na X, ADC ta zargi Hukumar ICPC da take doka ta hanyar ci gaba da tsare El-Rufai, tare da hana shi ganin likitansa duk da matsalar lafiyar da take fama da ita da kuma hukuncin kotu kan belinsa.

Jam'iyyar ta kuma yi zargin cewa hukumar ta kama likitan da ke kula da lafiyar El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, tare da cewa an ci zarafin ɗaya daga cikin matansa a Abuja.

Bolaji Abdullahi ya ce an shirya kai El-Rufai Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin a duba lafiyarsa a ranar Talata, amma daga baya jami'an ICPC suka mayar da shi inda ake tsare da shi.

"Jami'an ICPC suka dage sai sun maida shi inda ake tsare shi. Kuma likitansa da matarsa suka ce ba su yarda ba, wanda hakan ya jawo sa-in-sa har aka doke matarsa," in ji sanarwar ADCn.

Jam'iyyar ta ce abin da ke faruwa da El-Rufai tauye haƙƙi ne, inda ta yi zargin gwamnatin Shugaba Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa masa lamba saboda saɓanin siyasa.

"Babu gwamnatin dimokuraɗiyya da ke iƙirarin bin doka da za ta hana wanda ake tsare damar zuwa asibiti ko kuma a hana shi ganin iyalansa na kusa. "Wannan ya saɓa wa umarnin kotu, domin kotu ta ba shi damar ganin lauyoyinsa, likitocinsa da iyalansa ba tare da wani shamaki ba."

Kakakin ADC ya ce irin wannan mataki ya fi kama da abin da ake gani a gwamnatin kama-karya, kuma wannan batun na bai shi kaɗai ya hafa ba.

"Yau El-Rufai ne, gobe kuma zai iya faruwa kan kowane ɗan Najeriya wanda laifinsa kawai shi ne saɓanin ra'ayin masu riƙe da madafun iko."

Jam'iyyar ta buƙaci a bayyana wa duniya wanda ya bayar da umarnin hana El-Rufai ganin likitansa, a ba shi damar ganin iyalansa, da sake duba sharuɗɗan belinsa, sannan ICPC ta gudanar da aikinta bisa doka ba tare da nuna son rai ba.

Abin da ya sa muka kama likitan El-Rufai - ICPC

El-Rufai

Asalin hoton, El-Rufai/FB

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya ta tabbatar da kama likitan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke tsare a wajenta saboda saɓa ƙa'idojin duba lafiyarsa da kotu ta bayar.

Hukumar ta ce ta kama Farfesa Bello Abubakar, bisa zarginsa ba da bayanan ƙarya a yayin da ake bincike.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar, ICPC El-Rufai ya ƙi amincewa ya halarci zaman kotun da ya kamata a gudanar a Kaduna a ranar 6 da 7 da 8 ga watan Yuni, inda ya nace sai an haɗa shi da likitansa.

Sakamakon hakan ne hukumar ta ce ta ce ta amince da duba lafiyar tsohon gwamnan kamar yadda kotu ta yi umarni.

Hukumar ta ƙara da cewa kamar yadda iyalansa suka buƙata, jami'anta sun fita daga ɗakin a lokacin duba shi a babban asibitin ƙasa domin mutunta sirrinsa.

Sai dai ICPC ta ce daga bisani ta gano wasu hotuna da wani abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a shafinsa na Facebook, waɗanda ke nuna tsohon gwamnan tare da wasu baƙi, ciki har da likitansa, a lokacin da aka ware domin duba lafiyarsa.

Hukumar ta ce hakan ya nuna cewa an yi amfani da damar ziyarar jinya wajen yin wasu abubuwan da ba su cikin abin da kotu ta amince da shi.

ICPC ta kuma ce za ta sanar da kotu abin da ta kira saɓa wa umarninta da aka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da tsare Farfesa Bello Abubakar domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa.