Abin da muka sani kan zargin "kashe fiye da naira tiriliyan 8" da IMF ta ce gwamnatin Tinubu ta yi

Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan da Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya bayyana wasu kashe-kashen kudaɗe da gwamnatin Najeriya ta yi da suka kai kusan kashi 2 na tattalin arziƙin ƙasar da ba a fayyace su yadda ya kamata ba a cikin kasafin kuɗin ƙasar, ƴan Najeriyar kama daga ƴan siyasa da masana ke ta tofa albarkacin bakinsu.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai wani jami'in asusun ya bayyana haka a wani taro a birnin Legas.

IMF dai bai ce an kashe kuɗin ne da suka kai naira tirirliyan 8.83 ba bisa ƙa'ida ba, amma ya nuna cewa an kashe kuɗaɗen ne ba tare da fayyacewa ba a rahotannin kasafin kuɗin ƙasar ba.

Sai dai masana tattalin arziƙi da ƙungiyoyin sa ido kan kuɗaɗen gwamnati sun nuna damuwa cewa idan har akwai giɓin bayanai a rahotannin kuɗaɗen gwamnati, hakan na iya shafar amincewar masu zuba jari da kuma yadda ake tantance ainihin matsayin bashin da giɓin kasafin kuɗin ƙasar.

Me IMF ya ce?

IMF

Asalin hoton, Getty Images

Christian Ebeke, wakilin IMF a Najeriya, wanda ya yi wannan bayani a wani taro da ya gudana a Legas, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta fayyace wasu kashe-kashe kuɗaɗe musamman na ayyukan raya ƙasa ba a cikin takardun kasafin kuɗi, lamarin da ya sa giɓin kasafin kuɗin gwamnati ya yi ƙasa a rubuce fiye da yadda yake a zahiri.

A cewar Ebeke, IMF na ganin ya zama dole a rubuta da kuma bayyana waɗannan kashe-kashen domin a samu sahihan bayanai game da matsayin kuɗaɗen gwamnati da kuma a kawar da bambancin da ke tsakanin abin da ake kashewa da abin da rahotanni ke nunawa.

Sai dai kuma Ebeke ya yi gargaɗin cewa kashe kuɗaɗe ba tare da sanya su cikin kasafin kuɗi ba na haifar da ƙarin damuwa game da yin lissafi da gaskiya, hanyoyin bayar da kwangiloli, da kuma sa ido daga hukumomin da ke da alhakin kula da harkokin gwamnati.

Ya jaddada cewa inganta bayyana bayanan kuɗaɗen gwamnati a fili ya kamata ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnati za ta ba fifiko.

Sai dai wakilin na IMF ya amince cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara ɗaukar matakan magance matsalar ta hanyar wasu sauye-sauyen dokoki da ke da nufin shigar da kashe-kuɗaɗen da ba a riƙa bayyana su a baya ba cikin tsarin kasafin kuɗi na hukuma.

Martanin gwamnatin Najeriya

Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta zargin cewa ta kashe sama da naira tiriliyan 8 a wajen tsarin kasafin kuɗi.

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele ya ce gwamnati ba ta gudanar da wani "kasafin kuɗi a ɓoye" kuma duk wani kashe kuɗi yana gudana ne bisa tanadin kundin tsarin mulki da dokokin da Majalisar Tarayya ta amince da su.

Gwamnatin ta ƙara da cewa akwai nau'o'in kashe kuɗi da doka ta tanada, ciki har da ayyukan da ke gudana na tsawon shekaru da dama, bashin gwamnati, da wasu tsare-tsaren musamman da ke samun amincewar doka, wanda bai kamata a ɗauke su a matsayin kashe kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.

Martanin Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Team

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka dangane da rahoton da IMF, inda ya bayyana shi da wani mummunan al'amari da ya faru a baya-bayan nan.

"Wannan ne mafi girman rashin bin ƙa'idar tafiyar da kuɗaɗen gwamnati a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya na baya-bayan nan."

A cikin wata sanarwa, Atiku ya yi zargin cewa wannan kashe kuɗin da aka ruwaito na nuni da kasancewar wani tsarin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati na daban da ke aiki a wajen sa idon Majalisar Tarayya da kuma hukumomin da ke kula da harkokin sanya ido da tabbatar da gaskiya.

Atiku Abubakar ya ƙara da cewa "wannan ne babban dalilin da ya sa ƴan Najeriya za su hukunta gwamnati APC" a zaɓen 2027, kasancewarta mara kula da irin halin da ƴan aksar ke ciki.

Peter Obi ya nemi Tinubu ya yi "murabus"

Peter Obi

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, shi ma ya shiga cikin masu sukar lamarin, inda ya sake kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus daga muƙaminsa.

Obi ya ce abubuwan da IMF ta ruwaito sun ƙara tabbatar da damuwar da aka daɗe ana nunawa game da rashin bayyana gaskiya da ɗaukar alhakin ayyuka da kuma yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama'a a "ƙarƙashin gwamnatin yanzu."

Ya bayyana kashe kuɗin naira tiriliyan 8.83 da aka ruwaito a "matsayin abin matuƙar tayar da hankali" yana mai cewa adadin ya zarce kashi ɗaya bisa uku na duk kuɗin da aka ware wa ayyukan raya ƙasa a kasafin kuɗin Najeriya, sannan ya fi jimillar kuɗaɗen da aka ware wa bangaren ilimi da na lafiya.

A cewar Obi, al'amari ya ƙara ƙarfafa sukar da ya daɗe yana yi wa yadda gwamnatin ke tafiyar da tattalin arziƙi.

Ya kuma ce a koyaushe yana jaddada cewa gwamnatin ta gaza magance matsalolin da ke "ƙara ta'azzara na talauci da rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalar tsaro" yadda ya kamata.