Waɗanne ƙasashe ne za su tsallake kwata-fainal a Gasar Kofin Duniya?

Lionel Messi, Kylian Mbappe, Harry Kane da Romelu Lukaku
    • Marubuci, Joe Bradshaw
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport senior journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gasar cin kofin duniya ta bana da aka faɗaɗa ta riga ta haifar da wasu manyan wasanni - kuma labari mai daɗi shi ne jerin ƴanwasan da za su fafata a zagayen kwata-fainal wanda idan aka duba ba ƙaramin abin sha'awa ba ne ga masu bibiyar ƙwallon ƙafa.

Ƙasashe shida na Turai da ɗaya-ɗaya daga Afirka da kuma Kudancin Amurka za su yi ƙoƙarin shiga cikin wasan daf da na ƙarshe a wasanni huɗu masu ban sha'awa da za fara fafatawa daga ranar Alhamis.

Duk wasannin huɗu suna da ban sha'awa sosai - kuma kusan duka wasannin za a fara su ne a lokacin da magoya baya daga ƙasashen Turai za su iya kallo saboda ba su yi dare ba sosai.

To me za mu iya sa ran gani a wasannin zagayen kwata-fainal guda huɗu?

Mamaicin wasan kusa da na ƙarshe na gasar 2022

xxx

Asalin hoton, Getty Images

Faransa da Moroko, filin wasan Atlanta, Ranar Alhamis 09/07/2026

Yayin da nasarar da Moroko ta samu na kaiwa zagayen kusa da na ƙarshe a Qatar abin mamaki ne, wannan tawagar da ke fafatawa a Amurka ta fi ƙarfin a yi mata kallon ta ƴan wasa marasa ƙarfi.

A ranar Asabar da ta gabata, zakarun gasar ƙasashen Afirka (wanda Senegal ke jiran ɗaukaka ƙara bayan wasan ƙarshe mai cike da ce-ce-ku-ce a watan Janairu), sun sanya ƴan wasa huɗu ne kacal daga cikin waɗanda suka sha kashi a wasan kusa da na ƙarshe da suka kara da Faransa shekaru huɗu da suka gabata.

Suna wasa da kuzari da kuma ƙarfin hali, kuma za su zama ƙalubale mafi tsanani da Faransa ta fuskanta zuwa yanzu a gasar bana.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ɓangaren ƙasar da ta zo ta biyu a gasar 2022, uku ne kawai daga cikin ƴan wasan da suka buga wasan kusa da na ƙarshe suka fara wasan da Faransar ta yi nasara kan Paraguay a ranar Asabar. Fitowar William Saliba, ɗan wasan tsakiya kuma gwarzon ɗan wasa Michael Olise, suna daga cikin sabbin abubuwan da Didier Deschamps ya yi tun daga lokacin.

Kylian Mbappe har yanzu shi ne gwarzon ɗan wasa kuma zai ci gaba da ƙoƙarinsa na doke Lionel Messi na Argentina wajen samun kyautar takalmin zinare da kuma lambar gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya.

Muhimman alkaluma: Rabin adadin rashin nasarar da Faransa ta yi a gasar cin kofin duniya a cikin wannan ƙarnin sun zo ne a hannun ƙasashen Afrika (Uku daga cikin shida).

Moroko ba ta yi rashin nasara ba cikin wasanni 34 a jere da ta fafata a baya, amma ba ta taɓa nasara kan Faransa ba wadda ta lashe wasannin bakwai a jere, yayin da ta yi nasara a wasanni 11 cikin 12 da ta buga.

Yadda za a iya bibiya: Ku bibiyi shafin labaran wasanni na kai-tsaye a babban shafin mu na intanet bbc.com/hausa.

Ko ƴan wasan gaban Belgium za su iya galaba kan ƴan wasan bayan Spain?

Belgium ta ragargaji Amurka domin zuwa matakin kwata-fainal inda za ta kara da Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Belgium ta ragargaji Amurka domin zuwa matakin kwata-fainal inda za ta kara da Spain

Spain da Belgium, Filin wasan Los Angeles Stadium, Ranar Juma'a 10/07/2026

Ƙwallaye 13 da Belgium ta ci su ne na uku mafi yawa a wannan gasar (bayan Argentina da Faransa da suka ci 14), kuma sun yi nasara a kan New Zealand, Senegal da Amurka a wasanni uku da suka gabata.

Romelu Lukaku ya zura ƙwallaye uku yayin da ya ke shigowa daga kan benci, yayin da Leandro Trossard na Arsenal ya zura ƙwallaye biyu ya kuma taimaka aka ci biyu.

Babu shakka Spain za ta kasance ƙalubale mafi wahala daga wasannin da ta yi a baya. Har yanzu ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya ba a wannan gasar, kuma wasa shida da ta yi ba tare da an zura mata ƙawallo ba - ciki har da wasansu na ƙarshe a gasar 2022 - shi ne jerin wasanni mafi tsayi da kowace tawaga ta taɓa yi a tarihin gasar cin kofin duniya.

Muhimman alƙaluma: A ƙarƙashin jagorancin Luis de la Fuente, Spain ta samu tsallakawa daga duka wasannin shida da ta buga a zagayen kifa-ɗaya-ƙwala a gasar kofin duniya da kuma ta cin kofin nahiyar Turai. Wannan shi ne wasanta na farko a zagayen kwata-fainal tun bayan da ta lashe gasar a Afrika ta kudu a shekarar 2010.

Spain ba ta yi rashin nasara ba a wasanni 11 da ta ƙara da Belgium (ta ci guda tara an kuma yi canjaras biyu) Belgium za ta yi fatan cewa tarihi zai maimaita kansa shekara 40 bayan lokacin da ta doke Spain a bugun fenariti a zagayen kwata-fainal ɗin gasar Mexico '86.

Yadda za a iya bibiya: Ku bibiyi shafin labaran wasanni na kai-tsaye a babban shafin mu na intanet bbc.com/hausa.

Kane v Haaland - fafatawar ƴan wasan gaba mai matuƙar jan hankali

Haaland ya taimaka wa Norway ta doke Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haaland ya taimaka wa Norway ta doke Brazil

Norway da Ingila, filin wasan Miami, Ranar Asabar 11/07/2026

Gawurtaccen mai zura ƙwallaye a raga na Norway, Erling Haaland, ya zura ƙwallaye bakwai a wasanni huɗu a gasar bana, kuma ya nuna ƙwarewarsa inda ya ci ƙwallaye biyu, a wasan da suka yi waje da Brazil daga gasar, wadda ta lashe gasar har sau biyar.

Ɗan wasan gaban na Manchester City, yana da ƙwallaye 62 a wasanni 54 da ya buga wa ƙasarsa- wanda ke nufin yana zura ƙwallo ɗaya cikin kowane minti 71. Haka kuma ya zura aƙalla ƙwallo ɗaya a wasanni 14 da ya buga wa ƙasarsa a jere, inda ya ci ƙwallaye 27 a wannan lokacin.

Duk da haka, kyaftin ɗin Ingila Harry Kane, yana bin bayan Haaland da ƙwallo ɗaya a fafatawar neman wanda ya fi zura ƙwallo a gasar, wanda fenaritin da ya ci a wasansu da Mexico ya tabbatar da cewa sun yi waje da masu masaukin baƙin.

Ɗan wasan gaba na Bayern Munich mai shekara 32 ya zura ƙwallaye (73) a ƙungiyarsa da ƙasarsa, adadin da ya zarce na kowane ɗan wasa a ƙwallon kafar Turai a kakar 2025-26, kuma ya ci gaba da nuna wannan bajinta a gasar kofin duniya ta bana.

Da ƙwallaye 14, ya zama ɗan wasan Ingila da ya fi kowa zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya, kuma yana da kyakkyawan fata na ƙara yawan ƙwallayen a wannan matakin na kwata-fainal.

Muhimman alƙaluma: Ingila za ta buga wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya karo na 11 — adadi na uku mafi yawa bayan Brazil da Jamus (waɗanda kowaccensu ta kai sau 14). Sai dai, Ingila ta samu nasara a wasanni uku kacal a wannan matakin.

A nata ɓangaren kuma, Norway ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya sau huɗu ne kacal, kuma wannan shi ne karo na farko da ta kai zagayen kwata-fainal a babbar gasar. Ta yi hakan ne ta hanya mai wahala inda ta zura ƙwallaye aka kuma jefa mata ƙwallaye a dukkan wasanninta zuwa yanzu. Jamus ce kawai a shekarar 1954 ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da irin wannan salon wasan.

Yadda za a iya bibiya: Ku bibiyi shafin labaran wasanni na kai-tsaye a babban shafin mu na intanet bbc.com/hausa

Ko Argentina za ta kai bantenta?

Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Argentina ta sha da ƙyar a wasan da ta doke Masar

Argentina da Switzerland, filin wasan Kansas City, Ranar lahadi 12/07/2026

Wannan zai zama wasa na uku a jere da ake yi wa Argentina kyakkawar zato - amma har yanzu nasara ba ta zo da sauƙi ga masu riƙe da kambun gasar ba.

Cape Verde ta kai ta har zuwa bango inda har sai da aka kai ƙarin lokaci a wasansu na zagayen ƴan 32, sannan ta farfaɗo bayan an zura mata ƙwallo biyu a raga a zagayen da ya biyo, inda abokiyar hamayyarta Masar da ta sha kashi ta yi iƙirarin cewa an yi mata "rashin adalci".

A ƙarƙashin jagorancin koci Murat Yakin, Switzerland ta nuna cewa ita ba kanwar lasa ba ce kuma tana da nata ƙasaitaccen ɗan wasan Johan Manzambi mai shekara 20, duk da cewa bai buga wasan da suka yi nasara a bugun fenariti da Colombia ba saboda raunin da ya samu. Wannan shi ne karo na farko da suka kai matakin zagayen kwata-fainal na gasar cin kofin duniya tun 1954 kuma da alama wannan tawagar ta Argentina mai ƴan wasa da ke ya yawan shekaru ba za ta tayar musu da hankali ba.

Muhimman alƙaluma: Duk da yawan alkaluma masu ban sha'awa da yake da su, Messi ya ƙara wani mara kyau guda ɗaya a ranar Talata lokacin da ya zama ɗan wasa na farko da ya ɓarar da bugun fenariti biyu a gasar cin kofin duniya.

Duk da haka, kwallon da ya ci daga baya ta sa ya wuce Mbappe a fafutukar neman lashe takalmin zinare inda ya ke da ƙwallaye takwas.

Yadda za a iya bibiya: Ku bibiyi shafin labaran wasanni na kai-tsaye a babban shafin mu na intanet bbc.com/hausa