Kotu ta buƙaci ƴansanda su tsare Dr Kurfi saboda zargin ɓata sunan gwamnatin Katsina

Asalin hoton, Amnesty International Nigeria
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kamawa da tsare Dr Bashir Kurfi, lamarin da ya biyo bayan jawabin da ya game da matsalolin tsaro.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin Trust, Dr Kurfi ya zargi gwamnatin jihar Katsinda da hannu a ɗaukar nauyin ƴanbindiga zuwa Hajji.
A ranar Laraba ne aka gabatar da malamin jami'ar a kotun Majistare a Katsina bayan rundunar ƴansandan jihar ta tuhume shi ƙazafi da ɓata suna.
Alƙalin kotun mai shari'a Zaharaddeen Kofar Soro ne ya buƙaci ƴansanda su cigaba da tsare wanda ake ƙara har zuwa lokacin da za a cigaba da sauraron shari'ar.
Da take jawabi kan batun, Amnesty ta ce Kurfi ya amsa gayyatar ƴansanda ne a ranar Talata 7 ga watan Yuliln 2026 domin amsa tambayoyi, amma a cewar ƙungiyar sai aka faɗa masa cewa za a tsare.
"Yanzu ana ƙoƙarin ganin an tsare shi na tsawon lokaci ta hanyar ƙirƙirar tuhume-tuhume," in ji ƙungiyar, wanda a cewarta karya ƴancin tofa albarkacin baki ne.
"Gwamnatin jihar Katsina na so ne ta hukunta kawai don ya yi tambayoyi game da yadda take kula da harkokin da suka shafi yaƙi da ƴanbindiga maimakon ta bincika abin da ya faɗa."
Amnesty ta ce an tsare Kurfi ne domin a tsoratar da mutane su daina tsokaci kan gwamnati. "Bai kamata a hukunta mutum ba domin ya soki gwamnti. Dr Kurfi bai aikata laifin komai ba, kuma tsare shi cin amanar aiki ne domin yana da ƴancin tambaya ko sukar yadda gwamnati take gudanar da aiki."































