KAI TSAYE, Wasanni da sharhi da kuma bayanan da suka shafi gasar cin kofin duniya 2026 da wasu batutuwan da suka shafi wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran wasannin da ake fafatwa, da sharhi da kuma bayanan da suka shafi gasar cin kofin duniya 2026 da wasu batutuwan da suka shafi wasanni

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Glasner ya zama kocin Nottingham Forest na biyar cikin shekara guda.

    Glasner

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Nottingham Forest ta naɗa tsohon kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner, a matsayin kociyanta na biyar cikin ƙasa da shekara guda.

    Ɗan kasar Austriyan ya iso filin wasa na City Ground ne domin maye gurbin Vitor Pereira, wanda aka kora a ranar Talata - mintuna biyu kacal kafin wa'adin wani sharaɗi na musamman a cikin kwantiraginsa ya ƙare.

    "Oliver mutum ne mai son nasara," in ji mamallakin ƙungiyar Forest, Evangelos Marinakis. "A bayyane yake cewa muna da manufa ɗaya, buri ɗaya, da kuma kishin ganin mun samu nasara ba tare da gajiyawa ba."

    An fara tattaunawa da Glasner, mai shekaru 51 - wanda ya bar Palace a ƙarshen kakar wasan da ta gabata - tun farkon wannan bazarar.

    Nuno Espirito Santo ne ya fara kakar wasan bara a matsayin kocin Forest, yayin da Ange Postecoglou da Sean Dyche da Pereira suka yi aiki tun daga watan Satumba.

    Glasner ya zama kocin Palace ne 2024 kuma ya jagorance su zuwa lashe babbar gasarsu ta farko a kakarsa ta farko - Kofin FA - kafin su lashe gasar Europa Conference League a kakar wasa ta bara.

    Sun lashe Community Shield a watan Agusta, inda suka doke Liverpool da bugun fanareti. A watan janairu ne Glasner ya ce zai bar Palace saboda yana son ya fuskanci wani sabon ƙalubale, duk da cewa an miƙa masa sabon kwantiragi.

    Glasner yana daya daga cikin kociyoyi uku kacal da suka taɓa lashe gasar Europa League da Conference League, bayan ya jagoranci Eintracht Frankfurt zuwa nasara a gasa Europa League a kakar wasa ta 2021-22.

  2. Tottenham ta kammala yarjejeniyar sayen Tonali kan fam miliyan 100 daga Newcastle

    Tonali

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Newcastle, Sandro Tonali, kan kuɗin da ya karya tarihin cinikin ƙungiyar, wanda zai iya kai wa fam miliyan 100.

    Ɗan wasan mai shekaru 26 ya koma ƙungiyar ta Landan ne bayan ya shafe kaka uku tare da ƙungiyar ta Magpies.

    Da farko Newcastle ta yi watsi da tayin fam miliyan 80 da Spurs ta yi, amma daga bisani suka cimma yarjejeniyar da za ta sa su biya fam miliyan 92.5 kai-tsaye, tare da ƙarin fam miliyan 7.5 idan har aka cimma wasu sharuɗɗa na musamman. "Ina matuƙar farin cikin kasancewa a nan," in ji Tonali. "Mutane sun yi ta cewa akwai ƙungiyoyi huɗu ko biyar da ke zawarcina, amma a zahiri ƙungiya daya ce kawai.''

    Tonali ya zama ɗan wasa na biyu da spirs ta saya da maƙudan kuɗaɗe bayan ta ɗauki Mateus Fernandes daga West Ham kan farashin fam miliyan 85.

  3. Neymar ya yi ritaya daga taka leda a tawagar Brazil

    Neymar

    Asalin hoton, Getty Images

    Neymar ya ce lokacinsa na laka leda a tawagar Brazil ya 'zo ƙarshe' bayan da tawagarsa ta sha kashi a hannun Norway a gasar cin kofin duniya ta 2026.

    Ɗan wasan mai shekaru 34 ya shigon wasan ne a minti na 67, a daidai lokacin da Norway ke doke Brazil da ci 2-0 , amma bai iya hana a yi waje da Selecao daga gasar ba.

    Neymar ya zura ƙwallo da gubun febariti a cikin ƙarin lokaci a wasan da aka buga a filin wasan MetLife da ke New Jersey, amma ƙwallon da ya ci bai sauya sakamakon wasan ba, wanda shi ne ya zama wasan ƙarshe da Neymar zai bugawa ƙasarsa.

    "Na yi ƙoƙari, na yi ƙoƙari. Yanzu ya ƙare. Na fara a nan, na gama a nan," in ji Neymar a wata hira da ya yi da TV Globo bayan wasan.

    Neymar ya guga wasansa na farko a tawgar Brazil a wannan filin wasa ne a watan Agusta na 2010, lokacin da ya zura ƙwallo a wasan sada zumunta a wasan da Brazil ta yi nasara kan Amurka da ci 2-0.

    Ya ci gaba da zama fitaccen ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin Brazil da ƙwallaye 80, yayin da wasanni 130 da ya buga wa ƙasarsa suka sanya shi a matsayi na biyu a jerin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallaye a tarihi bayan Cafu wanda ya buga wasanni 142.

    Neymar bai buga wa Brazil wasa ba tun shekarar 2023 sakamakon matsalolin raunuka dsa ya yi fama da su, kafin daga bisani a saka shi cikin tawagar ƙasarsa ta gasar cin kofin duniya ta 2026.

    Yana buga gasar cin kofin duniya ta huɗu - inda ya wakilci Brazil a gasannin shekarun 2014, 2018 da 2022.