'Yadda muka haɗu da juna har muka shiga auren gata a Kano'

Wasu ma'aurata da suka shiga auren gata da aka gudanar a Kano sun bayyana yadda ska ji da cikar burinsu a yau.
A ranar juma'a ne gwamnatin jihar Kano da ɗaura wa ƴanmata da zawarawa - kimanin 1,500 da angwayensu 1,500 - aure, ƙarƙashin shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa a kowace shekara.
An zaɓo ma'auratan ne daga duka ƙananan hukumomin jihar 44.
Gwamnatin na gudanar da shirin ne a wani yunƙuri na tallafa wa marasa ƙarfi da ke son yin auren amma sun gagara.
An ɗaura auren ne a fadar mai martaba sarkin Kano, yayin da Gwammnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kasance waliyyin amaren, sai kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya zama wakilin angwayen.
Babban kwamandan hukumar Hisba, wadda ita ce ta shirya auren ,Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya ɗaura auren.

Asalin hoton, Kano state Govt
'Yadda muka ji da wannan aure'
Wasu ma'aurata da BBC ta zanta da su a wurin ɗaurin auren sun bayyana irin farin cikin da suka shiga sakamakon cikar burin nasu.
Aliyu Ibrahim Beli, wanda ya kasance angon Amina Aminu Beli, ya ce gode wa Allah da ya tabbatar musu da aure tsakaninsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce sun jima suna soyayya da amaryar tasa, amma Allah bai ƙaddara za su yi aure ba, sai ta dalilin auren gata.
''Mun kai Allah shekara uku muna shan soyayya takanina da Amina, amma yanayin matsin rayuwa ya hana mu cika burinmu sai a yau ta dalilin auren gata da gwamnati ta shirya mana'', in ji Ango, wanda ke cike da zumuɗi da murna.
Ita ta amaryar tasa, Amina Aminu Beli ta ce babu abin da za ta ce a wannan rana sai gidaya ga Allah da ya cika mata burinta.
"Mun jima da burin aure tsakanina da Aliyu, amma hakan bai samu ba, sai a yau'', in ji amaryar.
Ta kuma bayyana irin soyayyar da take yi wa angon nata da fatan da take yi game da zaman auren nasu.
''Gaskiya ba zan iya bayyana irin siyayar da nake yi wa Aliyu ba, ina tsananin sonsa ta yadda ba zan iya misalta shi ba''.
Ta ƙara da cewa tana fatan za su rayu cikin kwanciyar hankali da amainci da juna.
''Ina fatan mu yi zaman aure irin wadda na baya ma za su yi koyi da zamanmu'', kamar yadda ta bayyana wa BBC.
Mutumin da aka kashe wa iyalai ya samu amarya

Asalin hoton, Kano state Govt
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankali a cikin auren gatar na bana shi ne sanya Haruna Bashir, mutumin nan da a shekarar da ta gabata aka kashe masa iyalai a unguwar Ɗarayi da ke birnin Kano.
An sanya Haruna Bashir cikin ɗaurin auren gatar, inda aka ɗaura masa aure da ... sabuwar amaryarsa.
A farkon shekarar nan ne labarin Haruna Bashir ya ɗauki hankali, bayan da wasu matasa ɗauke da makamai suka shiga gidansa da rana tsaka tare da kashe matarsa da ƴaƴansa shida, a wani al'amari mai sosa zuciya.
Tun bayan faruwar al'amarin gwmanatin Kano ta alƙawarta saya masa sabon gida tare da ɗaukar nauyin aurensa.
'Tun rasuwar matata ban samu damar aure ba'
Shi ma wani mutum da ya rasa shekaru da suka gabata, da a yanzu ya samu shiga auren gatar ya bayyana yadda ya ji.
Mutumin mai suna, Muhammad Tahiru, wanda mai lalurar bukata ta musamman ne ya ce ya ji daɗin wannan dama da ya samu na samun mata.
''Tun bayan rasuwar matata ban samu sukunin yin uare ba sai a yanzu, domn haka in aickin farin ciki'', in ji shi.
Manufar Auren gata

Asalin hoton, Kano State Govt.
Baya ga tallafin kayan aure da sauran abubuwan da suka shafi shirin, manufar Auren gata ita ce samar da wata dama ga waɗanda ke da niyyar yin aure, amma matsalolin tattalin arziki suka hana su cimma wannan buri cikin sauƙi.
Gwamnatin jihar na cewa shirin na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kan al'umma tare da gina iyali da tarbiyya domin makomar al'umma.
A duk lokacin gudanar da shirin gwamnati kan ware miliyoyin kuɗaɗe domin gudanar da shi, kama daga biyan sadaki da yi wa amaren kayan ɗaki da kayan gara, da ma ba su jari a wasu lokuta.
A wannan biki na bana gwamnatin jihar ta ce ta ware naira miliyan 300 domin biyan sadakin maraen da ba su kuɗin jarin sana'ar da za su fara bayan auren.
Ko manufar na wanzuwa?
Sai dai hukumar Hisba da ke shirya auren gatan ta ce kwalliya na biya kuɗin sabulu dangane da wannan shiri.
Cikin wani jawabi da ya yi a lokacin bitar da hukumarsa ta shirya wa ma'auratan a gidan gwamnatin jihar, gabanin ɗaura auren, shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce shirin na taimakawa wajen yawan zawarawa a jihar.
Haka kuma Sheikh Daurawa ya ce Hisba ta kafa kwasu kwamitocin sasanto tsakanin ma'auratan idan aka samu saɓani.
''Shi dama auren da Hisba ta ɗaura ba ya mutuwa, idan ya yi miki laifi ba gidanku za ki tafi ba, Hisba za ki zo akwai kwamitin karɓar ƙorafi, haka kai ma idan ta yi maka laifi Hisba za ka zo domin shigar da ƙorafinka'', in ji shi.
Sheikh Daurawa ya ce manufar hakan ita ce tabbatar da ɗorewar auren na har abada.











