Abu 5 kan sabuwar dokar hana bara a Najeriya

Hoton shugaban Najeriya Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Najeriya ta fara shirin inganta ilimin almajirci da tsangayu da makarantun allo, tare da rarraba kundin da ya kunshi tsare-tsaren wannan shiri a jihoh, musamman ma a jihohin arewacin kasar.

Shirin dai ya kunshi koyar da almajirai karatun alkur'ani da sauran fannonin ilimin addini da harsunan Larabci da Turanci, lissafi da ilimin kwamfuta da sauran sana'o'in dogaro da kai.

Bayan kaddamar da shirin inganta ilimin almajirci da tsangayu da makarantun allo a cikin watan Nuwamban bara a Najeriya, a yanzu an rungumi gabarar ganin wannan shiri ya yadu a jihohi da kananan hukumomi, musamman a arewacin kasar.

Dokta Muhammad Sani Idris, shugaban hukumar kula da al'amuran almajirai da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta, ya ce wannan shiri ne na gyara kayanka, ba wai sauke mu raba ba.

"Almajiri ɗa ne kamar kowa, kuma ya kama ayi masa gata, saboda haka yakamata aduba al'amarinsa da wanda ya kamata su taimake shi domin inganta rayuwarsa."

Dr Muhammad ya ce sun duba me ya kamata gwamnati a matakin tarayya da jihohi su yi kamar yadda kowane karatu yake samun taimakon gwamnati.

"Zamu kewaya jihohi domin tattaunawa da malaman tsangaya da kuma gwamnonin jihohi."

Dokta Balarabe Shehu Kakale, mai ba ministan ilimi na Najeriya shawara kan inganta ilimin almajirci da tsangayu da makarantun allo, wasu daga cikin fa'idoji biyar da wannan shiri ya zayyana

  • An shigar da tsarin ilimin almajiranci a hukumance
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hakan na nufin an sanya makarantun allo cikin tsarin ilimin Najeriya da zai basu damar amfana da dukkan wasu shirye-shirye na gwamnati.

  • Malamin makarantar allo zai amfana da duk wani shiri na gwamnati

Hakan na nufin za a ba malaman tsangaya damar cin gajiyar shirye-shirye gwamnati da ya shafi malamai na sauran makarantu.

  • An tabbatar da makarantun allo a matsayin makaranta kamar kowace makaranta ta gwamnati

Hakan na nufin almajirai dake karatu a makarantar suma sun zama dalibai a makarantar, saboda haka zai samu dukkan haƙƙoƙinsa da tsaro da walwala.

  • Almajirai ba za su riƙa bara ba

Za a kare haƙƙoƙinsa ta yadda ba zai je yayi bara ba, za a koya masu turanci da larabci da lissafi, sannan za a koya masu sana'o'i sama da ashirin da biyar da kayan aiki da masu koya masu.

  • Ilimin sanin ƴancin kai

Sannan za a koya wa almajirai ilimin sanin ƴancin kai, saboda duk inda almajiri ya je a Najeriya zai san ƴancinsa a matsayinsa na ɗan ƙasa.

Ana sa ran idan wannan shiri ya sami karbuwa da kafuwa, musamman a yankin arewacin Najeriya, zai kyautata tsarin ilimin almajirci da tsangayu da makarantun allo, kuma ya magance dimbin matsalolin da ake ta korafin suna tattare da shi.

A karshe ya samar da ingantattun dalibai, kuma kwararru, wadanda za su iya gogayya da dalibin wata cibiyar ilimi a duniya.

Shin akwai alaƙa tsakanin almajiranci da rashin tsaro?

Kabiru Adamu mai bincike ne kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited ya ce an yi bincike da dama kan matsalar a baya.

''Har gwamnatin Najeriya ta ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ta gudanar da bincike kan ko akwai alaƙa tsakanin almajiranci da matsalar tsaro. Sannan kamfanoni masu zaman kansu sun yi bincike," in ji shi.

Masanin harkokin tsaron ya ƙara da cewa dukkan binciken da aka yi sun gano abubuwa da dama.

"Amma ya kamata mu fara da tarihin tsarin. Ya kasance tsari ne don koyar da ilimin addini, amma yanzu abubuwa da yawa sun shiga ciki. Daga cikin abubuwan da suka shiga kamar yadda bincike ya nuna akwai:

Hatsarin shig cikin ƙungiyar: "Da farko shi ne hatsari ko kasada da yake ciki da ma yake jefa yara da suke ciki da al'umma dangane da yadda ƙungiyoyin da suke faɗa da gwamnati ke ɗaukarsu."

Sai Kabiru Adamu ya nanata cewa babu shaida tabbatacce da ke nuna cewa suna shiga ƙungiyoyi, "amma dai ana iya ɗaukarsu saboda ababe da yawa da suka shiga tsarin."

Masanin ya ce za a yi amfani da wa'azi a ja hankalinsu "saboda dama karatu suke yi. Idan aka yi rashin dace malaminsu ko na kusa da shi ko wuraren da suke zuwa akwai masu irin tunanin mayaƙan za su iya shiga. Na biyu amfani da kuɗi wajen jan hankalinsu su shiga."

Masanin ya kuma ƙara da cewa tsarin yakan taimaka wajen ta'azzarar aikata laifuka a cikin birane.

"Bincike ya nuna cewa yaran da aka jibge da ba sa samun kula, ƙungiyoyi na amfani da su wajen aikata laifuka musamma sace-sace a birane."

Ya ƙara da cewa tsarin na janyo safarar jama'a ko jefa su cikin hali na tagayyara. "A ƙarƙashin wannan bincike ya nuna cewa ana wahalar da su ta hanyoyi da yawa ciki har da saka su bara wanda ba na kansu ba, wasu sukan yi bara su kai wa na gaba da su, sannan akwai rhotannin cin zarafinsu."

"Akwai kuma cututtuka da suke iya ɗauka a sanadiyar yanayin wurin da suke zama, wanda sukan iya yaɗawa a cikin al'umma."