'Yan tawayen Houthin Yemen sun ɗauki alhakin harin sansanin soji Marib
'Yan tawayen Houthi na Yemen sun ɗauki alhakin harin da aka kai kan wani sansanin soji a lardin Marib a ranar Juma'a. Yankin dai na ƙarƙashin ikon gwamnatin Yemen da Saudiyya ke marawa baya ne.
A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, wata majiya daga rundunar sojin Yemen ta bayyana cewa sojoji takwas sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai a lardin.
Kakakin Houthi, Yahya Saree, ta cikin wata sanarwa ya ce: "Abokan gabarmu na Saudiyya sun ci gaba da tara dakarunsu tare da ɗaukar matakan tsokana. A sakamakon haka, an kai hari kan waɗannan rundunoni tare da runbunan ajiyar makamansu, motocinsu da kayan aikinsu na soja a sansanin 'Sahn al-Jin' ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da dama."
A kwanakin baya-bayan nan, rikici da tashin hankali tsakanin Houthi da Saudiyya ya ƙara tsananta.
Houthi, waɗanda Iran ke marawa baya, suna iko da wasu sassan arewacin Yemen, kuma sun daɗe suna gwabza yaƙi da dakarun gwamnatin Yemen da kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ke goyon baya.



































