Fitattun Sha'irai 5 da suka fi tashe a TikTok

.

Asalin hoton, Facebook/Multiple

    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Idan kai mai amfani da TikTok ne, akwai yiwuwar ka taɓa cin karo da ɗaya daga cikin waƙoƙin yabon da wasu fitattun sha'irai ke wallafawa a dandalin.

Mafi yawansu matasa ne da shekarunsu ke tsakanin 20 zuwa 30, kuma sun samu karɓuwa a tsakanin jama'a a sassa daban-daban na duniya, ciki har da arewaci da kudancin Najeriya.

A wasu lokutan ma, ana ganin har waɗanda ba Musulmi ba suna amfani da ƙasidunsu a bidiyoyi ko kuma suna rerawa, duk da cewa ba lallai su fahimci ma'anar kalmomin gaba ɗaya ba.

Ko da yake akwai fitattun mawaka da sha'irai da suka yi suna tun kafin bayyanar TikTok, BBC ta mayar da hankali ne kan waɗanda suka yi fice a wannan dandali.

Bayan nazarin yawan mabiyansu, yawan masu kallon bidiyoyinsu da kuma yadda ake amfani da waƙoƙinsu a TikTok, BBC ta gano sha'irai biyar da suka fi yin fice a dandalin.

1 - Zaki Dan Yaya

.

Asalin hoton, ZAKI DAN YAYA FACEBOOK

Bayanan hoto, ZAKI DAN YAYA

Zaki Dan Yaya na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan yabon da suka yi fice a TikTok, bayan wani gajeren bidiyonsa da ya yi tare da abokansa ya bazu a shekarar 2023.

Daga cikin waƙoƙinsa da suka fi jan hankali akwai "Ya Fadima", wadda dubban mutane suka yi amfani da ita a TikTok, yayin da bidiyon waƙar ya samu fiye da kallo miliyan ɗaya a YouTube.

Ya kuma yi wasu waƙoƙin yabo da suka samu karɓuwa kamar Mai Gida Ɗan Gata, Ahmad Ali da Fauqal Muqamati, lamarin da ya taimaka masa tara kusan mabiyan miliyan biyu a TikTok.

A wata hira da Dandal Kura, Zaki Dan Yaya, wanda sunansa na ainihi Salisu Alhaji Uba (UMT), ya ce an haife shi ne a unguwar Gomari Costin da ke Maiduguri a jihar Borno, kuma ya yi karatu har matakin Diploma.

2 - Sirrin Fatahi

.

Asalin hoton, SIRRIN FATAHI FACEBOOK

Bayanan hoto, SIRRIN FATAHI

Sirrin Fatahi na ɗaya daga cikin fitattun mawakan yabon Annabi (S.A.W) da suka yi suna a TikTok, inda yake da sama da mabiyan miliyan 1.4. Karɓuwar waƙoƙinsa ta sa dubban mutane ke amfani da su a bidiyoyinsu a dandalin.

Daga cikin waƙoƙin da suka fi ba shi suna akwai Annabi Ya Fi Nan, Haka Muka So, da kuma Barhama, wadda yake yabon Sheikh Ibrahim Inyass a cikinta.

Sirrin Fatahi ya yi fice ne da waƙoƙin yabo masu motsa sha'awa da ɗaukar hankalin masoya, inda wasu ke kwatanta salon waƙarsa da na marigayi Fadar Bege.

Mawakin ɗan asalin jihar Kano ne, kuma sunansa ya bazu a sassa daban-daban na duniya ta hanyar kafafen sada zumunta.

3. Babangida Mafaka da tawagarsa

BABANGIDA MAFAKA FACEBOOK

Asalin hoton, BABANGIDA MAFAKA FACEBOOK

Bayanan hoto, BABANGIDA MAFAKA FACEBOOK

Babangida Mafaka, shugaban tawagar Sha'irai ta Mafaka, ya yi suna a TikTok tare da ɗalibansa sakamakon salon waƙoƙinsu na karɓa-karɓa da ya samu karɓuwa a wurare da dama na duniya.

Tawagar ta ja hankalin jama'a har ma a yankunan da ba a jin Hausa, inda wasu ke haddace waƙoƙinsu suna rerawa duk da rashin fahimtar ma'anar kalmomin.

Bidiyoyinsu na samun miliyoyin masu kallo a TikTok, kuma suna da sama da mabiyan miliyan 1.3 a shafinsu.

Ɗaya daga cikin ƙasidunsu ma ya samu fiye da kallo miliyan 18, lamarin da ya ƙara tabbatar da farin jinin tawagar a kafafen sada zumunta.

4 - Musaddiq M Sadiq

.

Asalin hoton, MUSADDIQ M SADIQ FACEBOOK

Bayanan hoto, MUSADDIQ M SADIQ

Musaddiq M. Sadiq na ɗaya daga cikin matasan mawakan yabo da suka yi fice a TikTok, musamman da waƙarsa ta Ya Nana, wadda dubban mutane suka yi amfani da ita a bidiyoyinsu.

Sauran waƙoƙinsa da suka samu karɓuwa sun haɗa da Madina, Garin Masoyi da Muradin Zuciya. Wani abin da ya bambanta shi da wasu mawaka shi ne yadda yake amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) wajen samar da waƙoƙinsa.

Waƙarsa ta Ya Nana ce ta fi ba shi suna a wannan lokaci, inda matasa maza da mata ke amfani da ita wajen ƙirƙirar bidiyoyin yabo. Musaddiq na da sama da mabiya dubu 800 a TikTok, kuma ana kallon waƙoƙinsa da yawa a dandalin.

A halin yanzu, ana ɗaukar Musaddiq a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mawakan yabo da suka fi tashe a kafafen sada zumunta.

5 - Zakin Ma'aiki

ZAKIN MA'AIKI

Asalin hoton, ZAKIN MA'AIKI FACEBOK

Bayanan hoto, ZAKIN MA'AIKI

Zakin Ma'aiki na ɗaya daga cikin matasan mawakan yabo da suka yi fice a TikTok, inda ya shahara da ƙwarewarsa wajen rerawa da kuma salon kalaman da ke jan hankalin masoya.

Mawakin, wanda ɗan asalin jihar Kano ne, ya samu karɓuwa musamman a tsakanin matasa. Daga cikin waƙoƙinsa da suka yi tashe akwai Umma Fatima, wadda dubban mutane suka yi amfani da ita a bidiyoyinsu a TikTok.

Zakin Ma'aiki ya kuma yi suna wajen amfani da kalamai masu kare mazahabar Tijjaniyya a wasu waƙoƙinsa, lamarin da ya sa waƙoƙinsa ke yawan jawo muhawara da martani daga masu sauraro.

Duk da haka, farin jininsa na ci gaba da ƙaruwa a kafafen sada zumunta, inda yake da gagarumin goyon baya daga matasa masu sha'awar waƙoƙin yabo.