'Fitsari da gumi muka riƙa sha a inda aka tsare mu a Neja'

Waɗanda suka tsira
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Mutane biyu da suka tsallake rijiya da baya bayan tsare su a jihar Neja da ke Najeriya sun shaida wa BBC cewa sun rika shan fitsarinsu da kuma zufarsu domin su rayu bayan ƙishirwa mai tsanani ta addabe su a wani ƙaramin ɗaki da aka tsare ɗimbin mutanen da ake zargin masu haƙar ma'adinai ne ba bisa ƙa'ida ba.

Matanen biyu, waɗanda duk suna shekarunsu na ashirin da haihuwa, na cikin mutanen da jami'an Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Najeriya (NSCDC) da aka fi sani da Sibil Difens, suka kama yayin wani samame da suka kai domin yaƙi da abin da suka bayyana a matsayin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

Daga baya, aƙalla mutum 37 da aka tsare sun mutu, kamar yadda gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bayyana, inda ya ce mafi yawansu matasa ne masu ƙarancin shekaru.

Har yanzu ba a tantance musabbabin mutuwar mutanen ba, yayin da ake gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan lamarin.

BBC ta samu damar kai ziyara ta musamman zuwa wurin da ake tsare mutanen a Minna, inda mutanen biyu da suka tsira suka koma ɗakin da suka ce su da sauran waɗanda aka tsare tare da su suka yi ta gwagwarmayar neman tsira.

A gare su, komawa wurin yana dawo musu da tunanin sa'o'i na fargaba da ƙishirwa da kuma matsananciyar damuwa da suka fuskanta.

Ɗakin ƙarami ne, kuma babu wadatacciyar iska. Har ila yau, akwai wani wari mai ƙarfi da ke ci tashi a cikin ɗakin.

'Matsanancin halin da muka shiga'

Matasan biyu sun ce an cunkusa mutane da dama a cikin ɗakin, lamarin da ya sa numfashi da motsi ya yi musu wahala.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sun ce waɗanda ake tsare da su sun riƙa neman agaji akai-akai yayin da halin da suke ciki ke ƙara tsananta, amma sun zargi cewa ba a saurari kokensu ba.

Yayin da tsananin zafi da rashin ruwa suka yi muni, mutanen sun ce wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su sun fara shan fitsarinsu da kuma tattara zufa daga jikinsu domin su samu abin da zai taimaka musu su ci gaba da rayuwa.

''Mun riƙa shan fitsarinmu da zufar da ke fita daga jikinmu saboda tsananin ƙishirwa," in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga lamarin.

Sun ce wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su sun fara galabaita sakamakon mummunan halin da suke ciki, inda wasu ke faɗuwa saboda rashin ƙarfi.

A cewarsu, wasu kuma sun rasa rayukansu ne a cikin wurin da ake tsare da su.

"Irin zafin da na ji a cikin wannan wuri ban taɓa jin irinsa ba a rayuwata. Idan muka taɓa jikin juna, sai ya zama kamar yana ƙonewa," in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga lamarin.

"Ɗaya daga cikinmu ya suma, sai muka fara bugun ƙofa muna neman taimako. Da ɗaya daga cikin masu gadin ya zo, muka roƙe shi ya ba mu ruwa saboda wani ya suma. Ya kalli mutumin da ya suma sannan ya rufe ƙofar ya tafi. Daga nan ne suka fara mutuwa ɗaya bayan ɗaya," in ji shi.

Sai dai BBC ba ta iya tantance iƙirarin waɗannan matasan ba.

Tun da farko da Hukumar NSCDC ta ce wataƙila ɓarkewar wata cuta na iya kasancewa cikin abubuwan da suka haifar da waɗannan mace-mace, amma ta ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

Yaushe aka kama mutanen?

An kama mutanen ne a yayin wani samame da aka kai domin yaƙi da ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Jihar Neja.

Hukumar NSCDC ta ce sama da mutum 50 ne aka kama a lokacin gudanar da samamen.

Sai dai waɗanda suka tsira daga lamarin sun ce an tsare adadi mai yawa daga cikin mutanen da aka kama a cikin ɗaki ɗaya.

Mutuwar mutanen ta harzuƙa jama'a Minna Neja, inda mazauna birnin suka fito zanga-zanga.

Daga bisani gwamnatin jihar ta ƙaƙaba dokar hana fita ta sa'o'i 24 domin daƙile rikice-rikice da kuma dawo da doka da oda.

Waɗanne matakai hukumomi suka ɗauka?

Gwamnan Neja

Gwamnan jihar, Umaru Bago, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku tare da kira da a ɗauki ƙarin matakai wajen magance matsalar haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da ke addabar jihar.

A hirarsa da BBC Gwamnan Bago ya ce dole ne a yi wa waɗanda suka mutu adalci.

"Mutanen da aka kashe ba ƙudaje ba ne. Ta yaya za a yi watsi da wannan lamari? Za mu yi bincike har sai mun gano ainihin abin da ya faru."

Sai dai gwamnan ya ce har yanzu ba za a iya yanke hukunci kan musabbabin mutuwar mutanen ba, har sai sakamakon gwajin gawawwakin mamatan ya fito.

Ya ƙara da cewa yana sa ran sakamakon gwajin zai kammala cikin tsakanin kwanaki biyar zuwa makonni uku.

Haka kuma ya buƙaci dakatar da ayyukan haƙar ma'adinai a wuraren da ake ganin suna haifar da matsaloli a faɗin Jihar Neja.

A nata ɓangare gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa da ya ƙunshi mutum 10 domin gano ainihin abin da ya faru.

An bai wa kwamitin wa'adin makonni biyu ya tantance sunayen mamatan, ya binciki yadda aka kama su da kuma yadda aka tsare su, tare da gano musabbabin mutuwar da kuma duk wani sakaci ko alhakin da zai iya kasancewa a lamarin.

Hukumar NSCDC ta ce jami'anta 24 na tsare dangane da lamarin, ciki har da dakatararren kwamandan hukumar na Jihar Neja, Suberu Aniviye.

Hukumar ta ƙara da cewa an mayar da jami'an da ake zargi da hannu a lamarin zuwa Abuja, inda ake yi musu tambayoyi tare da gudanar da matakan ladabtarwa na cikin gida.

A halin yanzu an fitar da sunayen duka mutum 37 da suka mutu a wurin tsarewar.

Ga iyalan mamatan kuwa, fitar da sunayen ya taimaka wajen gano ainihin waɗanda suka mutu, waɗanda tun da farko aka riƙa ambatonsu gaba ɗaya a matsayin "mutane 37" kawai.

Haka kuma iyalan waɗanda suka rasu sun fara kira ga gwamnati ta biya su diyya, inda wasu iyaye suka ce da yawa daga cikin matasan da suka mutu su ne ke ɗaukar nauyin iyalansu.