Sabbin dabaru 5 da ƴanbindiga ke amfani da su wajen kai hare-hare

Sabbin dabaru 5 da ƴanbindiga ke amfani da su wajen kai hare-hare

Asalin hoton, Social Media

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da jami'an tsaro a Najeriya ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile hare-haren ƴanbindiga, su ma maharan na ci gaba da sauya salo tare da ƙirƙiro sabbin dabarun kai farmaki.

A baya-bayan nan, an ga yadda hare-haren nasu ba su tsaya kan al'umma kaɗai ba, har ma a kan sansanonin sojoji da sauran jami'an tsaro.

Ko da yake a wasu lokuta jami'an tsaro kan yi nasarar fatattakar maharan, yadda suke sauya dabarun na ƙara jefa fargaba, tare da ƙalubalantar ƙoƙarin hukumomin tsaro.

Hakan ya sa al'ummomi da dama ke rayuwa cikin ɗar-ɗar, saboda rashin sanin irin salon da ƴanbindiga za su yi amfani da shi a farmaki na gaba.

Wannan lamari dai na neman hana gudanar da ayyukan gona a daminar bana, sakamakon yadda matsalar tsaron ta yi ƙamari a sassa daban-daban na ƙasar.

BBC ta yi nazari kan wasu daga cikin sabbin dabarun da ƴanbindiga suka fara amfani da su a baya-bayan nan wajen kai hare-hare.

Yi wa jami'an tsaro ƙawanya kafin kai hari

Ɗaya daga cikin sabbin dabarun da ƴanbindigar suka ɓullo da shi a yanzu shi ne fara yi wa jami'an tsaro ƙawanya ko kuma cin ƙarfin su kafin su kai hari kan al'umma.

A maimakon su afka wa ƙauye kai tsaye, sukan fara kewaye sansanin jami'an tsaro ko wurin da suke, domin hana su fita ko kai ɗauki lokacin da harin ya fara.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Misali shi ne hari na baya-bayan na da aka kai Kasuwar Daji a ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, inda maharan suka fara kai farmaki kan sojojin da ke yankin, har ma suka kashe sojoji huɗu.

Bayan sun tabbatar jami'an tsaron sun maida hankali kan kare sansaninsu, sai sauran maharan suka shiga cikin garin, suka kashe mutane tare da yin garkuwa da fiye da mutum 50.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce jami'inta da ɗansanda ɗaya ne suka rasa rayukansu yayin da suke daƙile harin, kamar yadda rundunar Operation FANSAN YAMMA ta bayyana.

A watan Yuli ma, lokacin da ƴanbindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, mazauna yankin sun ce maharan sun fara kewaye jami'an tsaro da ke cikin ƙauyen tare da buɗe musu wuta, lamarin da ya hana jami'an fitowa domin kare mazauna.

Daga nan ne maharan suka riƙa bi gida-gida suna kashe mutane, satar dukiyoyi da kuma yin garkuwa da jama'a.

Masana tsaro na cewa wannan salo na bai wa ƴanbindiga damar cin karensu ba babbaka na sa'o'i ba tare da daƙile su cikin sauri ba.

Ƙona mutane da ransu a cikin gidajensu

Wani sabon salo da ƴanbindiga suka fara amfani da shi shi ne ƙulle mutane a cikin ɗakuna ko gidajensu sannan su banka musu wuta.

Masana tsaro na cewa wannan dabara ba wai don kashe mutane kaɗai suke amfani da ita ba, sukan yi ne domin razana al'umma da kuma tilasta musu barin ƙauyukansu.

A baya-bayan nan, a wani hari da aka kai wani ƙauye a jihar Sokoto, ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 12 tare da yin garkuwa da mata da yara. Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutum shida daga cikin iyali ɗaya sun ƙone ƙurmus bayan maharan sun rufe su a cikin gidansu suka banka masa wuta.

Bayan haka, maharan sun sace dabbobi da wasu mazauna ƙauyen kafin su tsere.

An samu makamancin irin waɗannan hare-hare a wasu sassan jihohin Zamfara, Katsina da Kebbi, inda maharan ke ƙona gidaje da rumbunan abinci bayan sun kwashe dukiyar da suke so ko kuma sun yi garkuwa da mutane.

A wasu lokuta kuma, sukan ƙone gidajen idan mutanen da suka ƙi biyan kuɗin fansa ko kuma waɗanda suka yi yunƙurin tserewa.

Wannan wata hanya ce da ƴanbindiga amfani da ita domin manufarsa ita ce haifar da firgici da kuma tilasta mazauna ƙauyuka yin hijira saboda tsoron kada su kasance waɗanda za su biyo baya.

Dasa nakiyoyi

Ƴanbindiga na ƙara amfani da salon dasa nakiyoyi ko wasu abubuwan fashewa a kan hanyoyin shiga da fita daga ƙauyuka. Hakan na nufin duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa ko kuma jami'an tsaro da za su kai ɗauki na iya faɗawa tarkonsu.

Wannan dabara na iya hana jama'a guduwa cikin gaggawa idan aka kai hari, saboda tsoron taka abin fashewa. Haka kuma tana jinkirta isowar jami'an tsaro ba tare da sun yi nazari kan lamarin ba.

Ƴanbindiga sun yi amfani da irin wannan salo a ranar 25 ga Yulin 2024, inda aƙalla sojojin Najeriya bakwai sun mutu bayan motarsu ta taka nakiyar IED a kan hanyar Monguno zuwa Baga a jihar Borno.

Nakiyar ta tashi ne lokacin da tawagar sojojin ke sintiri, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

A watan Yunin 2026 ma, rahotanni sun ce sojoji huɗu sun mutu bayan motar sintirinsu ta taka IED da aka dasa a kan hanyar Bargaja a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto. Rahoton ya ce fashewar ta lalata motar sojojin gaba ɗaya.

Kai wa alƙalai hari

A cikin ƙasa da mako guda, ƴan bindiga sun kai wa alƙalai biyu hari a arewacin Najeriya. Ɗaya an yi garkuwa da shi, yayin da ɗayan ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu masu ɗauke da makamai suka kutsa cikin kotun da ya ke shari'a.

A ranar 26 ga watan Yuli, wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Faruku Hassan, a ƙaramar hukumar Bunza. Rahotanni sun ce masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 200.

Bayan 'yan kwanaki kaɗan, wasu ƴan bindiga ne suka mamaye kotun Shari'a da ke ƙauyen Gwarjo a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina, inda suka riƙa harbe-harbe tare da tambayar "ina Alƙali Mohammed Muktar yake".

Masana harkokin tsaro na ganin hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa alƙalai ba wai don neman kuɗin fansa kaɗai ake yi ba.

A cewarsu, irin waɗannan hare-hare na iya kasancewa wata dabara ta razana masu gudanar da shari'a, tare da isar musu da saƙon tsoro domin su kasa gudanar da aikinsu cikin 'yanci.

Masanin harkokin tsaro, Dakta Kabiru Adamu, ya ce akwai yiwuwar ƴan bindiga na ƙoƙarin hana alƙalai gudanar da shari'o'in da suka shafe su ko kuma gurfanar da mambobinsu idan jami'an tsaro suka kama su.

"Akwai yiwuwar ƴan bindiga na ƙoƙarin isar da saƙo ga alƙalai domin su ji tsoro. Kai hari kan alƙalai na iya kasancewa wata hanya ta ɗaukar fansa kan hukunce-hukuncen shari'a.," in Kabiru Adamu

Kwantan ɓauna domin kashe masu tserewa

Ƴanbindiga sukan yi kwantan ɓauna ta hanyar rarrabuwa zuwa ayar-ayari kafin kai hari. Abin nufi shi ne yayin da wata tawaga ke kai farmaki a cikin ƙauye, wasu kuma sukan laɓe a hanyoyin fita ko cikin dazuka da ke kewaye da ƙauyen.

Da zarar mutane sun firgita suka fito daga gidajensu suna neman hanyar tsira, sai waɗanda ke fake su buɗe musu wuta ko kuma su yi garkuwa da su.

Hakan na rage wa mutane ƙwarin gwiwar tserewa.

A hare-hare da dama a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina, mazauna ƙauyuka sun ce maharan sun kewaye hanyoyin fita kafin su shiga cikin gari. Wasu da suka yi ƙoƙarin guduwa sun faɗa tarkon maharan, yayin da wasu kuma aka yi garkuwa da su.