Salva Kiir ya rusa gwamnatinsa

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya rusa gwamnati tare da naɗa gwamnatin riƙon ƙwarya, matakin da ya ce zai share fagen gudanar da zaɓen ƙasar na farko a tarihi wanda ake sa ran yi a watan Disamba.
Masu sukar matakin dai sun yi gargadin cewa hakan zai bai wa shugaban cikakken iko ba tare da wata takura ba.
A bangare guda kuma, Mista Kiir ya cire dukkan mataimakan shugaban ƙasa da aka naɗa ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar.
Haka kuma an sallami ministoci, da shugabannin ƙananan hukumomi da kuma jami'an majalisun dokoki na ƙasa da na jihohi.
'Yan adawa a kasar dai sun yi Allah-wadai da wadannan sauye-sauyen, waɗanda suka soke muhimman tanade-tanaden yarjejeniyar zaman lafiyar, ciki har da haɗa rundunonin sojojin da suka yi gaba da juna da kuma kammala rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.


















