Ƴantakarar shugaban Najeriya 5 mafi ƙanƙantar shekaru a zaɓen 2027

Ƴan takarar shugaban Najeriya 5 mafi ƙanƙantar shekaru a zaɓen 2027

Asalin hoton, Multiple/Social Media

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Jerin ƴantakarar shugaban ƙasa a zaɓen Najeriya na 2027 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa ya nuna cewa shekarun ƴantakarar 18 da za su fafata a zaɓen sun kasance tsakanin 35 zuwa 79.

Cikin ƴantakarar 18, akwai mata biyu, yayin da sauran 16 maza ne. Duka matan biyu kuma suna cikin ƴantakarar biyar mafi ƙanƙanta shekaru.

A dokokin Najeriya, dole ne mutum ya kai aƙalla shekaru 35 kafin ya cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Ga jerin ƴantakarar biyar da bayanan INEC suka nuna su ne waɗanda ba su kai shekaru 50 ba a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Janairun 2027.

1. Moses Olusoji Adebisi — DLA

Adebisi Moses Adesoji

Asalin hoton, Adebisi Moses Adesoji

Moses Olusoji Adebisi ne mafi ƙanƙantar shekaru cikin ƴantakarar shugaban ƙasa 18 da INEC ta fitar a zaɓen 2027.

Shekarunsa 35, kuma yana neman shugabancin Najeriya ne ƙarƙashin jam'iyyar Democratic Leadership Alliance (DLA). Adebisi yana da shaidar kammala Firamare, sakandare da digiri, kamar yadda bayanan INEC suka nuna.

DLA ba ta taɓa shiga zaɓe ba somin sabuwar jam'iyya ce da INEC ta yi wa rajista a ranar 5 ga Fabrairun 2025. Saboda haka, zaɓen 2027 shi ne karon farko da DLA za ta shiga zaɓen shugaban ƙasa tun bayan samun rajistar jam'iyyar.

Adebisi ya zaɓi Nafisat Usaku Abubakar a matsayin mataimakiyarsa, wadda ita ma shekarunta 35, kuma tana da shaidar Firamare, sakandare da digiri.

2. Sunday Chibuzo Okereke — Labour Party

Okereke Sunday Chibuzo

Asalin hoton, Okereke Sunday Chibuzo/FB

Sunday Chibuzo Okereke yana da shekaru 43, kuma shi ne ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2027. INEC ta kuma bayyana cewa yana da takardun karatu da suka haɗa da NABTEB, BSc, MSc da PhD, baya ga MLS mai matakin distinction.

Labour Party ba sabuwar jam'iyya ba ce. An kafa ta a shekarar 2002, kuma a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ta taka rawar gani sosai inda ta samu gagarumin sauyi a sakamakon komawar tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, jam'iyyar daga PDP ya yi mata takarar shugaban ƙasa.

Obi ya samu kuri'u 6,101,533, lamarin da ya sanya LP ta samu babban matsayi a zaɓen shugaban ƙasar na wancan lokacin kuma ta lashe wasu kujerun ƴan majalisar dattawa da wakilai na tarayya da jihohi da kuma gwamna ɗaya.

A 2027, Okereke zai tsaya takara tare da mataimakiyarsa Hajja Bintu Konto, wadda INEC ta bayyana cewa tana da shekaru 54. Tana da digiri a fannin ilimin lafiya da Satifiket a fannin jinya.

3. Nkem Esther Okereke — NRM

Esther Nkem Okereke

Asalin hoton, Esther Nkem Okereke/FB

Nkem Esther Okereke mai shekaru 43, ita ce ƴar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyyar National Rescue Movement (NRM). Tana cikin mata biyu kacal da INEC ta saka cikin jerin ƴantakarar shugaban ƙasa 18 na zaɓen 2027. Tana da digiri, MSc da PhD, baya ga shaidun karatun Firamare da sakandare.

NRM ba sabuwar jam'iyya ba ce a zaɓen shugaban ƙasa. Ta shiga zaɓen 2023, inda Felix Johnson Osakwe ya yi mata takara inda ya samu kuri'u 24,869.

Jam'iyyar ta kuma shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2019, inda ɗan takararta a lokacin Ibrahim Usman Alhaji ya samu kuri'u 6,229.

A wannan karon, Nkem Esther Okereke za ta yi takara tare da mataimakinta Sulaiman Nasir Muhammed, mai shekaru 35. Hukumar ba ta nuna wata babbar takardar karatu ta jami'a a bayanan da ta wallafa a kansa ba, inda ta wallafa yana da shaidar kammala firamare da sakandire.

4. Aliyu-Bin-Abbas — ADP

Abbas-Bin Aliyu

Asalin hoton, Abbas-Bin Aliyu

Aliyu-Bin-Abbas shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na Action Democratic Party (ADP) kuma yana da shekaru 44. INEC ta bayyana cewa yana da takardar kammala firamare da sakandare ta SSCE da kuma digiri BSc.

Mataimakinsa shi ne Chinazam Ike, wanda ke da shekaru 50, bisa bayanan da hukumar ta wallafa.

ADP ma ba sabuwar jam'iyya ba ce. INEC ta yi mata rajista a ranar 7 ga Yunin 2017, kuma jam'iyyar ta shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2019. A wancan zaɓen, Yabagi Yusuf Sani ne ɗan takararta, inda ya samu kuri'u kusan 19,000.

A zaɓen 2023 kuma, Sani ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin ADP. Ya samu kuri'u 43,924.

A watan Yulin 2026, Abbas-Bin Aliyu ya bayyana cewa ya zaɓi Chinazam Ike a matsayin mataimakinsa.

5. Ada Elizabeth Fredrick Okwori — NDP

Okwori Ada

Asalin hoton, Okwori Ada

Ada Elizabeth Fredrick Okwori mai shekaru 48, kma ita ce ƴar takarar shugaban ƙasa ta jam'iyyar National Democratic Party (NDP). Ita ce za a iya cewa ta kai kusan shekara 50 cikin wannan rukuni na ƴantakarar biyar mafi ƙanƙanta shekaru.

NDP sabuwar jam'iyya ce a zaɓen Najeriya. Tana cikin sabbin jam'iyyun da aka yi wa rajista a wannan zagayen, inda aka ba ta takardar rajista a ranar 16 ga Maris 2026, bayan wata kotun tarayya ta bayar da umarnin a yi mata rajista.

NDP ba ta cikin jam'iyyun da suka fafata a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Don haka, zaɓen 2027 zai kasance karon farko da NDP za ta shiga zaɓen shugaban ƙasa.

Mataimakinta shi ne Chukwuemeka Uchenna Anthony, wanda shi ma ke da shekaru 48. Yana da shaidar kammala firamare da sakandare da LLB.