Yadda jama'a ke tserewa gidajensu saboda rikicin ƙabilanci a jihar Kebbi

Asalin hoton, AFP
Al'ummar garin Lafagu, da ke karamar hukumar Bagudu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun fara tserewa suna barin gidajensu, bayan wani rikicin ƙabilanci da ya janyo mutuwar mutum 15, ciki har da hakimin garin.
Al'ummar garin sun yi ƙaura inda suka koma garin Bagudu don tsira da ransu.
Kisan da aka yi wa hakimin garin Alhaji Sa'idu Mujeli, ya haifar da fargaba a zukatan jama'a.
Ɗaya daga cikin iyalan hakimin ya shaida wa BBC cewa, a yankinsu ana fama da rikici ne tsakanin Fulani da kuma Kamburawa.
Ya yi iƙirarin cewa Kamburawan ne suka far wa Fulani inda suka riƙa kama su suna kashewa, sannan kuma suka shiga garin Lafagu inda suke riƙa bi gida-gida suna tambayar ko an ɓoye wani Bafullace.
"To a nan ne da suka shiga gidan sarkin, kuma dama shi Bafullatani ne, to ko da suka shiga sai suka fito da shi suka ƙona gidan sanann suka je can wani waje da shi suka harbe shi," in ji shi.
Abin da jami'an tsaro suka ce
Ya ƙara da a yanzu garin na Lafagu ba ya zaunuwa domin kowa ya gudu saboda ya tsira da ransa, duk da jami'an tsaro sun ce kowa su koma gidajensu, amma har yanzu ba wanda ya koma.
Tuni dai jami'an tsaro suka tabbatarwa da BBC afkuwar wannan lamari, inda kwamshinan 'yan sandan jihar, CP Umar Hadeja ya ce suna tsare da mutum shida da ake zargi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rikicin ƙabilanci dai ba sabon abu ba ne a Najeriya, kuma lamari ne da ya ki ci ya ƙi cinyewa a kasar.
A mafi yawancin lokuta akan danganta irin wannan rikici a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma.
Akwai dai jihohin Najeriya da ke fama da irin wadannan rikici na kabilanci ciki har da jihar Filato da Taraba da kuma Adamawa.
Kamar jihar Taraba, ta yi ƙaurin suna a kan rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, da na makiyaya da manoma abin da kan rura wutar zaman gaba da rashin yarda tsakanin ƙabilun da ke zargin juna.
Haka Filato ma ana kallon ƙabilanci da addini a matsayin ƙiraren da ke rura tashin hankalin na jihar Filato, inda a mafi akasarin lokuta duk wani rikici da kan tashi a yankin kan samo asali ko kuma ya rikiɗe zuwa na ƙabilanci ko na bambancin addini.
Masana dai na ganin duk da cewa a ko da yaushe aka samu ɓarkewar rikici a jihar Filato ana alaƙanta ta da bambancin addini tsakanin Musulmai da Kirista ko kuma ƙabilanci - tsakanin ƙabilun jihar Filato da kuma a ɓangare ɗaya Fulani makiyaya da Hausawa, amma sauyin yanayi da kuma tsukewar dazukan kiwo na daga cikin manyan dalilan da ke iza wutar rikicin.
Mene ne shirin gwamnonin arewa kan matsalar tsaro?
Tun a watan Yunin 2026 ne gwamnonin yankin arewa maso yammacin Najeriya suka fara yunƙurin aiwatar da wata manufar haɗin gwiwa da nufin shawo kan talauci mai fuskoki da dama ta hanyar shirye-shirye da dabarun tallafawa rayuwa a jihohin yankin bakwai.
Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne bayan kammala wani taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Kano, inda suka yi fatan za su samar da dabarun da za su magance matsalolin yankin ciki har da batun yaran da ba sa zuwa makaranta.
Mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo, da ya wakilci gwamnan jihar ya shaida wa BBC cewa, akwai abubuwan da suka ja hankalin gwamnonin yankin da har aka shirya taron aka kuma gudanar da shi.
Ya ce,"mun ga cewa gara a hadu gaba daya domin a fito da sabbin dabaru na yakar talauci, domini dan abu ya yi yawa to dole sai an samu shawarwari daga masana da al'umma ta yadda za a fito da sabbin dabaru na magance duk wata matsala."
"Akwai abubuwa da dama da ke janyo talauci kamar yawan mutane a yankinmu na arewa maso yamma da yawan yaran da basa zuwa makaranta da tabarbarewar tsaro da na noma da ma rashin sana'oin dogaro da kai." In ji shi.
Mataimakin gwamnan Kano, ya ce," A yayin taron an cimma matsaya akan yadda za a tallafawa bangaren ilimi sosai ta yadda kowanne yaro da ke yankin zai samu damar zuwa makatanta musammamma mata."
" Baya ga batun inganta ilimi a yankin na arewa maso yamma, an kuma cimma matsaya akan yadda za a inganta fannin lafiya da noma da ma tsaro, wanda yana daga cikin abin da yad amu gwamnoni da ma al'ummar yankin baki daya." In ji shi.










