BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Tasirin Kudu maso kudu a siyasar Najeriya
Daga tarihin gwagwarmayar neman 'yanci a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ya zuwa muhimmiyar rawar da yake takawa a tattalin arzikin ƙasa, yankin ya kasance muhimmin ɓangare na tsarin siyasar Najeriya tun ba a yau ba
Arsenal na zawarcin Rodrygo, Shaw zai iya barin Man United
Arsenal na sanya ido kan Rodrygo, Luke Shaw na shirin raba gari da Manchester United
Fitattun matan da ke takarar majalisar dattawan Najeriya a zaɓen 2027
Yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar hankali a Najeriya, wasu fitattun mata sun shiga fafatawar neman kujerun Majalisar Dattawa a sassa daban-daban na ƙasar.
Yadda Amurka ta girke makamanta a sararin samaniya
Sakataren rundunar sojin sama ta Amurka, Troy Meink, ya ce makaman, wanda ke kewaya duniya a sararin samaniya, suna da muhimmanci wajen bayar da tsaro ga dakarun Amurka, daga barazanar hare-haren abokan gaba.
'Ɓarnar da Iran ta yi wa sansannonin sojin Amurka'
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Laraba 16/09/2026
Me ya bambanta farashin man fetur a Najeriya da wasu ƙasashen Afrika?
Najeriya ta cire tallafin man fetur a 2023, lamarin da ya sa farashin man fetur ya tashi sosai, kuma hakan ya shafi sufuri da shafar kusan kowane fanni da jefa da dama na ƴan ƙasar cikin matsin tattalin arziki.
Yadda aka kama mutumin da ya nemi shawarar ChatGPT don kashe ɗansa
Shari'ar ta haifar da tambayoyi game da abin da ya kamata ya faru idan AI ya gano wata barazana kafin a aikata laifi.
Wane ne Olu Jacobs, tauraron finan-finan Nollywood da ya rasu?
Fitaccen jarumin Najeriya kuma tauraron masana'antar fina-finan Nollywood, Olu Jacobs, wanda ya tashi a birnin Kano, ya rasu yana da shekaru 84. Iyalansa ne suka sanar da rasuwarsa a shafukan s
Me ya janyo rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin APC?
Wani kwantaccen rikicin siyasa tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnonin jam'iyyar APC ya fito fili a ranar Litinin bayan da ike ya bayyana damuwarsa dangane da abin da ya bayyana da ƙoƙarin taɗe shi da gwamnonin ke yi.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Hantsi, 06:30, 17 Satumba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurara Kai Tsaye, Shirin Safe, 05:29, 17 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 16 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 16 Satumba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Joao Pedro na son sabon laƙabi ga ƴan gaban Chelsea uku
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 14 zuwa 19 ga watan Satumbar 2026.
Barcelona na sa ido kan Kane da Haaland, United na harin Branthwaite
Barcelona na sa ido kan Harry Kane da Erling Haaland, yayin da ɗan wasan gaban Jamus Nick Woltemade na iya maye gurbin Kane a Bayern Munich, yayin da Manchester United ke harin Jarrad Branthwaite, da ƙarin wasu labaran
Kuskuren VAR: Me ya sa ba a soke ƙwallon Haaland ba?
Manchester United ta yi rashin nasara a wasan hamayya da Manchester City, amma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne ƙwallon da Haaland ya ci da cewar an yi satar gida.
Atletico da Juventus na harin Madueke, Liverpool na son Wanner
Atletico Madrid da Juventus na harin Noni Madueke, Liverpool ta shiga sahun ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗan wasan PSV Paul Wanner, sai Lazio na nazari ɗaukar dan wasa mai zaman kansa Mauro Icardi, da ƙarin wasu labaran.
Bayern na son Wirtz, Dortmund ta fasa sayen Sancho
BBayern Munich na sa ido kan Florian Wirtz, yayin da ɗan wasan gaban Bournemouth da Brazil Rayan zai iya komawa Liverpool, sai Borussia Dortmund ta fasa sayen Jadon Sancho.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Gwamnonin da ba za su je majalisar dattawa ba bayan kammala mulki a 2027
A yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙara matsowa, siyasar Najeriya na shiga wani sabon salo, musamman a jihohin da gwamnoni masu ci ke kammala wa'adinsu na biyu.
Ina makaman da ake safara zuwa Najeriya ke shigewa?
A cikin watanni shida na farkon shekarar 2026, an shiga da da makamai da alburusai da darajarsu ta kai naira biliyan 55.06 cikin Najeriya.
Waɗanne makaman uranium ne Rasha ke amfani da su?
An ce akwai kusan lokuta 10 da aka tabbatar da amfani da irin waɗannan jirage. Dukkansu jiragen leƙen asiri ne na Rasha da aka gano bayan sun fāɗi a ƙasar Ukraine.
Ko yawan kallon bidiyo na illa ga ƙwaƙwalwar matasa?
Wannan ɗabi'a ta zama dalilin da ya sa mutane da dama ke amfani da gajerun bidiyoyi a kafafen sada zumunta kamar TikTok, Instagram, YouTube Shorts da Facebook.
Wane mataki Najeriya ke ciki wajen aiwatar da kasafin kuɗin 2026?
Wata Cibiyar da ke Neman Tabbatar da Adalcin Ga Jama'a (CSJ) ta buƙaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da kasafin kuɗin manyan ayyuka na shekarar 2026 nan take, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da jinkirta hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da dokar kula da kuɗaɗen Jama'a da kuma dokar kasafin kuɗi.
Abin da malaman jami'a suka faɗa wa masu neman su goyi bayan Tinubu
Ganawa da malaman jami'o'in ta haifar da ce-ce-ku-ce a fadin ƙasar, inda aka ruwaito cewa sun yi mubaya'ar ne da sunan Lakcarori a arewacin Najeriya.
Fitattun Sanatoci 10 da ba za su koma majalisar dattawan Najeriya a 2027 ba
Aƙalla ƴan majalisar dattawan Najeriya 35 ne suka rasa damar sake tsayawa takara a zaɓen 2027 da ke tafe a ƙasar.
Za mu mayar da martani kan hare-haren Houthi - Saudiyya
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Talata 15/09/2026
Wane ne zai gaji Trump? Ɓoyayyiyar fargabar da Republican ke ciki
Idan jam'iyyar Republican ta yi nasara a zaɓen shugaban Amurka na 2028, wanda zai gaji Trump zai zama shugaban Amurka na 48.
Mayaƙan Houthi sun sake kai hare-hare kan cibiyoyin soji a Saudiyya
Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Litinin 14/09/2026
Yadda za ku gane warin jikinku na damun na kusa da ku
Warin jiki matsala ce da aka sani wadda ke iya shafar jin daɗin rayuwar mutum. Masana sun bayyana cewa abin ba zufar kanta ba ne, sai dai yawan ƙwayoyin cuta da suke girma a cikin zufar.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































