Barcelona na sa ido kan Kane da Haaland, United na harin Branthwaite

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harry Kane
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona na harin ɗan wasan Bayern Munich Harry Kane, da takwaransa na Manchester City, Erling Haaland, a madadin ɗan wasan Atletico Madrid Julian Alvarez. (Talksport)

Anan alaƙanta Bayern Munich da ɗan wasan Newcastle United da Jamus Nick Woltemade da ke zaman ɗan wasan aro a Juventus - a matsayin wanda zai maye gurbin Kane.(Talksport)

Manchester United na hangen ɗan wasan Everton da Jarrad Branthwaite, bayan komawarsa ci gaba da taka leda sakamakon rauni da ya samu. (Football Insider)

Arsenal na harin ɗan wasan Ingila Rio Ngumoha, yayin da Liverpool ke son tsawaita masa kwantaraginsa. (Athletic - subscription required)

Har yanzu Tottenham na son ɗan wasan Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, da a baya suka so ɗaukar ɗan wasan a kakar wasanni ta 2025, sai dai Forest bata da niyar siyar da shi. (Teamtalk)

Ɗan wasan Real Madrid Endrick, zai iya zama mai zaman kansa, nan da watan Janairu, inda Manchester United ke harin ɗan wasan na Brazil. (AS via Teamtalk)

Ɗan wasan Sipaniya Rodri, ya tattauna da mai horar da Real Madrid Jose Mourinho, domin yi masa godiya kan yadda yake mu'amala da shi, bayan komawarsa Barcelona duk da ƙin zuwa Madrid din daga Manchester City a wannan kaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Darktan wasanni Barcelona Deco ya yi wata ganawa da ɗan wasan Brazil Raphinha, da kwanta. (Sport - in Spanish)

AC Milan na yunƙurin siayrwa da Nottinham Forest ɗan wasanta da ke zaman aro a ƙungiyar kan euro miliyan 50 kwatankwacin fam miliyan 42.8.(Calciomercato - in Italian).