Tasirin Kudu maso kudu a siyasar Najeriya

Gwamnoni

Asalin hoton, Rt Hon Sheriff Oborevwori/Pastor Umo Eno/HE Sen Monday Okpebhol/Sir Siminalayi Fubara/Facebook

    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A siyasar Najeriya, akwai wasu yankuna da tasirinsu ya wuce adadin kujerun da suke da su a Majalisar Dokoki ko yawan al'ummarsu. Yankin Kudu maso Kudu na ɗaya daga cikin irin waɗannan yankuna.

Daga tarihin gwagwarmayar neman 'yanci a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ya zuwa muhimmiyar rawar da yake takawa a tattalin arzikin ƙasa, yankin ya kasance muhimmin ɓangare na tsarin siyasar Najeriya tun ba a yau ba.

Yanki ne da ba shi da tarin jihohi kamar saura, amma Kudu maso Kudu ya ƙunshi jihohin Akwa Ibom da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da kuma Rivers.

Duk da bambance-bambancen ƙabilu da harsuna da siyasar cikin gida, jihohin yankin suna da wani abu mai muhimmanci a haɗe, kasancewar suna da ɗinbin jama'a, kamar yadda Farfesa Abubakara Kari, na Jami'ar Abuja ya bayyana cewa, "jihohin shida na da ɗimbin jama'a kuma shi yankin na Kusu maso kudu shi ne na huɗu a yawan jama'a a Najeriya sannan shi ne na uku a jerin yankuna masu tarin ƙananan hukumomi".

Arzikin man fetur

Ba za a iya fahimtar siyasar Kudu maso Kudu ba tare da fahimtar rawar da man fetur ke takawa a Najeriya ba. Yawancin manyan wuraren samar da ɗanyen mai na ƙasar suna a yankin Neja Delta, wanda ya sa jihohin yankin suka kasance cikin muhimman cibiyoyin tattalin arziki a Najeriya.

Tsarin rabon kuɗin tarayya yana ba jihohin da ke samar da man fetur kaso na 13 cikin ɗari na daga rabon kuɗaɗen albarkatun da jiha ke samarwa. Kuma alƙalumman da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS, sun nuna cewa ana raba biliyoyin naira ga jihohin da ke samar da mai ta wannan tsarin. Misali, a watan Yunin 2024, an raba naira biliyan 106.50 ga jihohin da ke samar da mai.

Wannan ya sanya batun man fetur da rabon kuɗaɗen tarayya da muhalli da bunƙasa ci gaban yankin Neja Delta ba kawai batun tattalin arziki ba ne; har ma za a iya cewa ya zama batun siyasa mai girma.

Gwagwarmayar yankin Neja Delta

Tsawon shekaru, mazauna yankin Neja Delta sun yi ta nuna damuwa kan tasirin hakar man fetur da ke gurɓata muhalli da ma rashin isasshen ci gaba da kuma yadda ake raba arzikin yankin a lokaci ɗaya ana wofintar da al'ummar da ke rayuwa a cikin talauci da ƙarancin abubuwan more rayuwa.

Wannan rashin gamsuwa ya haifar da ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin matasa da kuma wasu ƙungiyoyin gwagwarmaya waɗanda suka sanya batun na Neja Delta cikin muhimman ajandar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Kamar yadda Farfesa Abubakar Kari ya ce, "daga bisani martabar yankin ta ƙara fitowa a fili, ta yadda kowace gwamnati na ƙoƙarin ganin ta cika muradun al'ummar yankin, domin kaucewa bore da da sauran ayukkan tayar da ƙayar baya."

Wanda haka ya sa a wasu lokuta ma, matsalolin tsaro da rikice-rikice a yankin suka shafi samar da mai da kuɗaɗen shiga na ƙasa. Rahotannin gwamnati sun nuna cewa hare-hare da lalata bututun mai sun taɓa yin mummunan tasiri kan kuɗaɗen shiga da fitar da mai daga Najeriya.

Saboda haka, siyasar yankin ba ta tsaya kan wanda zai zama gwamna ko Sanata kawai ba. Tana iya shafar muhimman batutuwan ƙasa kamar kasafin kuɗi da makomar kuɗaɗen tarayya da makamashi da kuma tsaron tattalin arziki.

Gudummawar yankin ga shugabancin Najeriya

Yankin na Kudu maso Kudu ya samar da manyan jiga-jigan siyasar Najeriya a matakin tarayya. Misali a tarihin baya-bayan nan shi ne tsohon shugaban ƙasar Goodluck Ebele Jonathan, wanda ɗan asalin Bayelsa ne, da a farko ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa sannan Shugaban Ƙasa.

A cewar Farfesa Kari "tasirin yankin bai taƙaita ga kasancewar ɗan yankin a fadar shugaban ƙasa ba kawai. A cikin tsarin siyasar Najeriya, goyon bayan jihohin yankin na iya zama muhimmi wajen gina manyan ƙawancen siyasa na ƙasa, musamman a zaɓukan shugaban ƙasa da na majalisun tarayya".

Masanin ya kuma ce a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu yankin na kudu maso kudancin Najeriya ya yi ƙawance da shiyar arewa ne, kuma a wancan lokaci jam'iyyar NPN ta yi matuƙar ƙarfi a yanki.

Gudummuwar jihohin yankin Kudu maso kudu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yankin Kudu maso kudancin Najeriya dai na da jihohi shida kamar yadda muka ambata da farko waɗanda kusan duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa ke neman ganin ta ya samu yawan ƙuri'u daga can.

Ga jerin jihohin da tasirinsu a siyasar Najeriya:

Rivers

Daga cikin jihohin Kudu maso Kudu, Rivers ta kasance ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin siyasar ƙasa.

Rivers tana da Port Harcourt, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin tattalin arziki da makamashi na yankin. Haka kuma tana da kananan hukumomi 23 da mazabu 13 na Majalisar Wakilai da mazabu 3 na Sanata. A bayanan INEC na 2023, jihar tana da sama da masu rajistar zaɓe har miliyan 3.5.

Wannan ya sa siyasar Rivers ta zama batun da zai iya wuce iyakokin jihar.

A wasu lokuta, abin da ke faruwa a Rivers yana zama wani ɓangare na babban rikicin siyasar ƙasa.

Delta

Jihar tana da kananan hukumomi 25, mazabu 10 na Majalisar Wakilai da mazabu 3 na Sanata, tare da sama da masu rajistar zaɓe miliyan 3.2 a bayanan INEC na 2023.

Amma muhimmancin Delta ya wuce lambobin masu zaɓe.

Tana cikin manyan jihohin da ake danganta su da samar da man fetur, kuma hakan ya sanya batun rabon arzikin ƙasa, ayyukan ci gaba da muhalli cikin muhimman batutuwan siyasarta.

A lokaci guda, Delta ta kasance muhimmiyar jihar wajen ƙawancen siyasa na ƙasa, musamman a tarihin PDP.

Bayelsa

Idan aka kwatanta yawan masu zaɓe da jihohi kamar Rivers ko Delta, Bayelsa ƙaramar jiha ce. Amma tasirinta a tarihin siyasar Najeriya ya fi abin da adadin masu zaɓe kaɗai zai nuna.

Daga mataimakin gwamna zuwa gwamna, daga mataimakin shugaban ƙasa zuwa shugaban ƙasa, tarihin Jonathan ya sanya Bayelsa cikin muhimman wuraren da ake magana a kai idan ana nazarin siyasar Najeriya.

Bugu da ƙari, Bayelsa tana da matsayi na musamman a cikin siyasar Neja Delta saboda muhimmancin yankin wajen samar da man fetur.

Akwa Ibom

A bayanan da Hukumar zaɓen Najeriya ta INEC ta fitar a 2023, jihar tana da masu rajistar zaɓe sama da miliyan 2.35, tare da ƙananan hukumomi 31 da mazaɓu 10 na Majalisar Wakilai da mazaɓu 3 na Sanata.

Wannan ya sa jihar ta zama muhimmiyar cibiyar siyasa a Kudu maso Kudu.

Tarihin siyasar jihar ya kuma nuna yadda tsarin jam'iyya ɗaya a matakin jiha zai iya taka rawa wajen tsara sakamakon zaɓukan ƙasa, musamman idan manyan 'yan siyasa daga jihar suka shiga ƙawancen siyasa na ƙasa.

Edo

Edo tana da wani matsayi na musamman saboda yanayin tarihinta da matsayinta na yanki.

Tana da alaƙa da siyasar Kudu maso kudu amma kuma tana da kusanci da siyasar Kudu maso Yamma.

Wannan matsayi ya sa siyasar Edo ta kasance filin da manyan jam'iyyun ƙasa ke neman samun ƙarfi.

A bayanan INEC na 2023, Edo tana da masu rajistar zaɓe sama da miliyan 2.5, tare da mazabu 9 na Majalisar Wakilai da mazabu 3 na Sanata.

Sakamakon haka, siyasar Edo na iya zama muhimmi wajen fahimtar yadda jam'iyyun ƙasa ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinsu daga wani yanki zuwa wani.

Cross River

Cross River ita ce ɗaya daga cikin jihohin Kudu maso Kudu da ke da nata yanayin siyasa.

Tana da kananan hukumomi 18, mazabu 8 na Majalisar Wakilai da mazabu 3 na Sanata, tare da kusan masu rajistar zaɓe miliyan 1.77 a bayanan INEC na 2023.

Tarihin siyasar jihar ya haɗa da sauye-sauyen jam'iyyu da manyan 'yan siyasa da suka taka rawa a matakin tarayya.

Wannan ya ƙara tabbatar da cewa tasirin Kudu maso kudu a siyasar Najeriya, ba wai daga tattalinarzikin yankin ne ba; siyasar cikin gida da shugabanci da ƙawancen jam'iyyu ma suna taka rawa.