'Na yi hijira zuwa Amurka don samun kwanciyar hankali, amma abu ya gagara'

Maryam Ahmed Said zaune a kan kujera cike da jimami
    • Marubuci, Bushra Mohamed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, London
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Maryam mai shekara 57, tana zaune a falon gidanta da ke Minneapolis, inda ta ke riƙe da wasu takardu masu ɗauke da sunan ɗanta, yayin da ta ke jimamin badaƙalar ƙwaya a Minnesota.

A kan cinyarta, takardu ne da ta ce ba za ta iya zubarwa ba, ciki har da na harajin ɗanta da rahoton bincike kan gawarsa, da sauran takardun da hukumomi suka bayar kan rayuwarsa a Amurka.

Kusan shekara 8 kenan, amma har yanzu tana cikin makoki kuma tana ci gaba da tunawa da ɗan autanta mai shekara 21, wanda ya rasu a 2019.

Maryam Said wacce ta tserewa yaƙin basasar Somalia sama da shekara 30 da suka wuce ta ce ta gudarwa rikici amma sai ta gamu wani tashin hankalin a Amurka.

"Na zo Amurka ne domin samun kwanciyar hankali, amma ban same shi," in ji Maryam.

Ma'aikatar Lafiya ta Minnesota ta ce mutum 678 ne suka rasu sakamakon shan ƙwayoyi da ya zarce ƙa'ida a shekarar 2024. Duk da cewa mace-macen sun ragu daga fiye da 1,000 da aka samu a 2022, wanda shi ne mafi yawa, jami'an lafiya sun ce matsalar ta na ci gaba da shafar iyalai a faɗin jihar.

Al'ummar ƴan asalin Somaliya a jihar Minnesota ta Amurka ta kasance cikin waɗanda abin ya fi shafa.

Kuma ga Maryam, waɗannan alƙalumma abu ne da zai tsaya mata a rai har abada.

Rahoton bincike da aka yi kan gawar ɗanta ya nuna cewa ya rasu ne saboda shan wuce ƙa'ida da ya yiwa ƙwayar fentanyl, wata ƙwaya da ake yawan sha a sassan Amurka.

"A lokacin da ya rasu, sai na yanke shawarar yin gwaji kan gawarsa, " in ji Maryam. "Mutane sun ce kada in yi, amma ina son yi, ko domin in gane hakƙiƙanin abin da ya faru."

Maryam ta ce rashin ɗan nata ya dawo mata da tunanin da ta shafe shekaru tana ƙoƙarin kauce ma.

Ta ce"Ina matashiya lokacin da aka fara yaƙi a ƙasata, an kashe makusanta na a kan ido na."

Ta kasance mai fatan cewa rayuwa a Amurka za ta zamo cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

A mamadin hakan sai ta samu wani abin na matuƙar damuwa.

"Mutuwa na da ciwo sosai, kuma har yanzu tana dau na. Ina rayuwa cikin tsananin damuwa.''

Jagororin al'umma sun ce illar fentanyl ta na matuƙar tasiri kan baƙi mazauna Minnesota.

Maryam Ahmed riƙe da wayarta mai nuna hoton ɗanta, wanda aka alaƙanta mutuwarsa da shan fentanyl, a Minneapolis.

Asalin hoton, Maryam Ahmed Said

Bayanan hoto, Maryam Ahmed riƙe da wayarta mai nuna hoton ɗanta, wanda aka alaƙanta mutuwarsa da shan fentanyl, a Minneapolis.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙwararru sun ce ana samun lokutan da iyaye da sauran ƴan uwa ke fama da wasu ƙalubalen na daban, kuma a lokaci guda suna ƙoƙarin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi.

Julie Bauch, babbar jami'ar tsare-tsare ta shirin yaƙi da shan ƙwaya a Hennepin County, ta ce ƴaƴan baƙi da dama suna tsintar kansu cikin ƙoƙarin koyon sabuwar rayuwar da al'ada, da kuma dimbin fatan da ke kansu ta gudanar da sauran harkokin rayuwa.

"Waɗannan yaran da aka haifa a Amurka ba su da masaniya kan rayuwa a Afirka,'' in ji ta.

"Sun tashi cikin tarbyyar iyaye ƴan Somaliya masu tsanani, kuma a lokaci guda suna tashi a cikin al'ada irin ta Amurkawa. Sun tashi cikin rayuwar da akwai ƙwaya da giya da waƙe-waƙe da banbancin tufafi da kuma sauran abubuwa da dama da iyayen su ba su yi a baya ba.''

Bauch ta ce sau tari, irin wannan banbanci na sanya ƴaƴan cikin mawuyacin halin da ba za su iya fitowa fili su tattauna da iayayensu kan irin ƙwayar da suke sha da kuma hatsarin da take da ita ba.

Ta ce irin yanayin da wata uwa a Minneapolis mai suna Deka ta tsinta kanta kenan.

Ta shafe shekaru tana fargabar za ta iya rasa ɗanta.

Ya fara shan ƙwaya da shiga rikici a cikin unguwa tun yana matashi.

"Wasu lokutan yana dawowa gida a firgice, wasu sun biyo shi da bindiga," in ji ta.

"Yana cewa in saki labule in kashe wuta kuma duk mu kwanta a kasa tare da yara. Ba mu san abin da ke faruwa ko waɗanda ke kawo mana hari ba.''

Ta bayar da labarin yadda ta kasance tana rayuwa cikin tsananin fargaba, dominkoanne lokaci ana iya kai masu hari.

Ta ƙara da cewa "Akwai lokacin da aka biyo shi har aka harbe shi a hannu,''

Deka zaune a falon ta a Minneapolis, inda ta bayar da labarin yadda ɗanta ya yi fama da matsalar shan ƙwaya.
Bayanan hoto, Deka zaune a falon ta a Minneapolis, inda ta bayar da labarin yadda ɗanta ya yi fama da matsalar shan ƙwaya.

Ba kamar ɗan Maryam ba, ita Deka ta yi sa'a ɗan nata ya tsira da rayuwar sa.

Ta ce wani abu da ya taimaka wajen sauya rayuwar sa shi ne sanarwar mutuwar abokinsa Samatar, wanda kuma shi ne ɗan Maryam.

Mutuwar ta tilasta mashi nazari kan shaye-shaye da kuma mayar da hankali wajen saita rayuwarsa.

A yanzu yana aiki tare da wasu matasa da suke fama da irin waɗannan ƙalubalen, yana ƙarfafa masu gwiwa domin su kaucewa irin kuskuren da ya kusa kaishi ga rasa rai.

Ita kuwa Deka, sauya halin nashi wani abu ne da ya zo da buƙatar dole ita ma ta sauya rayuwar gidanta.

"A ƙarshen na yanke shawarar canza abubuwa da dama game da rayuwa ta,'' in ji ta.

Ta sauya tsarin mu'amular su, inda ta canza daga yadda ta saba yi yun lokacin suna Somalia, ta koma tana huɗɗa da shi yadda zamani ke tafiya.

Yayin da rana ke faɗuwa a gidanta na Minneapolis, Maryam ta tattara takardun da ke gabanta, ta mayar da su a cikin jaka.

Ta ɗora rahoton gwajin da aka yiwa ɗanta bayan mutuwar sa, wani rahoto da ke tuna mata zafin rashin da ta yi.

Deka ta samu kwanciyar hankali cewa ɗanta ya tuba kuma ya fara sabuwar rayuwa.

Amma Maryam ta gaza mancewa da damuwar tambayoyin da take neman amsar su game da ɗan nata.

Labarinta ya fara ne da tserewa yaƙi a Somalia.

Gomman shekara bayan ta yi hijira, a yanzu Maryam mai shekara 57 a duniya ta tsinci kanta a cikin ƙuncin rayuwa a Amurka, saboda shaye-shayen ƙwaya da ta jefa iyalin ta a cikin tashin hankali.

Ba ta dai samu kwanciyar hankalin da ta fito nema ba.