KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya 06/07/2026

Wannan shafin ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya na ranar Litinin 6 ga watan Yulin, 2026

Skip Bidiyo and continue reading
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida

  1. Jami'an Afirka ta Kudu na binciken kisan 'yan Najeriya biyu a ƙasar

    ....

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar sa ido kan ayyukan 'yansanda ta Afirka ta Kudu IPID ta tabbatar da cewa tana binciken wani ƙorafi da aka shigar kan jami'an 'yan sanda a birnin Pretoria bayan mutuwar wasu ƴan Najeriya.

    Hukumar ta ce an shigar da ƙorafin ne a makon da ya gabata, amma ta ce har yanzu ba za ta iya bayyana cikakkun bayanai kan lamarin ba yayin da bincike ke gudana.

    Rahotanni sun nuna cewa ɗaya ya mutu ne yayin wata takaddama da ta shiga tsakaninsa da jami'an 'yansanda.

    A ranar 28 ga Yuni a lardin Mpumalanga kuma 'yansanda sun tabbatar da cewa suna binciken kisan ɗayan, wanda shi mai gidan gyaran gashi ne da aka harbe a wajen shagonsa da ke garin eMalahleni, tsohon Witbank.

    A cewar 'yansanda, wani mutum dauke da makami ne ya tare shi sannan ya harbe shi har lahira kafin ya tsere cikin wata farar mota.

    Har yanzu ba a kama kowa ba, kuma ba a san dalilin kashe ƴn Najeriya ɗin ba.

    'Yansandan suna kira ga duk wanda ke da bayanin da zai taimaka wajen cafke wanda ake zargi da ya tuntuɓe su.

  2. Za a kafa gwamnatin farar hula a Gaza bayan Hamas ta miƙa ragamar mulki

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Hamas ta sanar da rushe kwamitin da ke kula da harkokin gwamnatin Gaza, wanda ya jagoranci gudanar da mulkin yankin kusan tsawon shekara 20.

    A cewar sanarwar, shugaban kwamitin gaggawa na gwamnatin Hamas, Mohammed Fara, ya mika takardar murabus ɗinsa, yayin da aka amince da rusa kwamitin gaba ɗaya domin sauƙaƙa miƙa alhakin tafiyar da harkokin yau da kullum ga Kwamitin Kula da Gudanar da Gaza.

    Hamas ta karɓi ikon Gaza ne a shekarar 2007 bayan rikici da ƙungiyar Fatah, shekara guda bayan nasarar da ta samu a zaɓen majalisar dokokin Falasɗinawa na 2006.

    Tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila a watan Oktoban bara, Hamas ta bayyana a lokuta da dama cewa tana shirin janyewa daga tafiyar da harkokin yau da kullum na Gaza. sai dai har yanzu ba a warware batun kwance ɗamarar mayaƙanta.

    Mai magana da yawun Hamas ya ce matakin rushe kwamitin wani yunkuri ne na kawar da duk wata hujja da Isra’ila ke amfani da ita wajen ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

    Ana kallon wannan mataki a matsayin wani yunkuri na buɗe ƙofa ga kafa gwamnatin farar hula da za ta tafiyar da harkokin yankin a nan gaba.

  3. Matatar Dangote ta fitar da man biliyan 757 zuwa Turai

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Matatar man Dangote ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757 zuwa Turai a watan Yuni.

    Jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5.

    Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne mafi yawan man da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun lokacin da matatar Dangote ta fara samar da irin wannan mai a shekarar 2024.

    Haka kuma, Najeriya ta zarce Amurka wajen samar wa Turai man jirgin sama a watan Yunin inda ta fitar da tan 466,000, yayin da Amurka ta fitar da tan 399,000 kacal.

    Masana sun ce wannan nasara na nuna yadda matatar Dangote ke ƙara bunƙasa fitar da kayayyakin mai daga Najeriya tare da ƙarfafa matsayin ƙasar a kasuwannin makamashi na duniya.

  4. MDD ta ba da umarnin gaggauta bincike kan rikicin El-Obeid

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare haƙƙin ɗanadam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama a El-Obeid na Sudan, yayin da ta yi allawadai da ƙaruwar hare-haren RSF a yankin.

    Babban Kwamishinan MDD mai kula da haƙƙin ɗanadam, Volker Türk, ya yi gargaɗin cewa yankin na fuskantar wani sabon bala’in jin-ƙai, inda fararen hula suka shafe watanni 18 cikin mawuyacin hali sakamakon rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF.

    Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan RSF na ƙara taruwa a kewayen El-Obeid, lamarin da ya ƙara tsoron yiwuwar sabon hari, yayin da hukumomin jin ƙai ke gargadin ƙarancin man fetur, magunguna da ruwa mai tsafta a birnin.

  5. Tanzaniya ta tura sojoji da ƴansanda gabanin zanga-zangar ƙasa da aka shirya yi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Tanzaniya ta tura sojoji da ‘yansanda zuwa manyan biranen ƙasar gabanin wata zanga-zangar da aka shirya gudanarwa ranar Talata domin neman sauye-sauyen dimokuraɗiyya da kuma adalci kan zaɓen 2025 da ake takaddama a kansa.

    Mahukunta sun dakatar da duk wasu tarukan siyasa tun ranar 26 ga Yuni, suna masu cewa matakin na da nufin kare tsaro, yayin da ‘yan adawa ke ganin hakan tauye ‘yancin jama’a ne.

    Jami’an tsaro sun ce suna da bayanan sirri da ke nuna cewa wasu na shirin amfani da zanga-zangar wajen tayar da hankali da aikata ta’adi.

    Rundunar sojin ƙasar ma ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya ba.

    Tashin hankalin na da alaƙa da rikicin siyasa da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2025, wanda ya jawo zanga-zanga da asarar rayuka fiye da 500, a cewar wani kwamitin bincike na gwamnati.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ‘yan adawa suna zargin gwamnati da ƙuntata fagen siyasa, yayin da gwamnati ke cewa matakan tsaron da take ɗauka na wucin gadi ne kuma domin kare lafiyar ƙasa da al’ummarta.

  6. Pezeshkian, Qalibaf da babban ɗan Ali Khamenei za su halarci jana’izarsa a Iraq

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa za a kai gawar marigayi Ali Khamenei zuwa birnin Najaf gobe, Talata bayan an gudanar da jana’izarsa a birnin Qom.

    Rahoton ya ce Mustafa Khamenei, wanda shi ne babban ɗansa tare da shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian da kuma kakakin majalisar dokokin ƙasar Mohammad Baqer Qalibaf, za su tafi Najaf a gobe domin halartar jana’izar da za a gudanar a Iraq.

    An shirya gudanar da jana’izar Ali Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na ƙasar Iraq.

    Bayan haka, za a binne Khamenei ta Iran a ranar Alhamis a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.

  7. Cutar Ebola ta kashe mutum fiye da 500 a Gabashin DR Congo

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukuntan lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓullar cutar Ebola nau'in Bundibugyo ya kai 506.

    Tun bayan ayyana ɓarkewar cutar a ranar 15 ga Mayun 2026, an tabbatar da kamuwar mutum 1,561, yayin da mutum 628 ke killace ko kwance a asibiti a larduna uku na gabashin ƙasar.

    Lardin Ituri ne har yanzu ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda yake da fiye da kashi 90 cikin 100 na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu.

    Haka kuma jami'an lafiya sun nuna damuwa kan yawaitar zirga-zirgar jama'a a yankunan da ke cikin haɗari, musamman sakamakon rikice-rikice da ayyukan haƙar ma'adinai.

    Barkewar cutar ta kuma shafi ma'aikatan lafiya, inda mutum 96 daga cikinsu suka kamu da cutar, yayin da 19 suka mutu. Duk da ƙarancin kayan kariya da matsalolin da ake fuskanta, jami'an lafiya sun ce ana samun ci gaba wajen bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, kuma adadin waɗanda suka warke ya kai 254.

  8. Hatsarin mota a Ogun ya yi sanadin mutuwar mutum 10

    Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu shida suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a gadar Saapade da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

    Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Afolabi Odunsin, ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da kuma wata motar bas.

    Ya ce mutum 18 ne ke cikin motocin biyu a lokacin da hatsarin ya faru.

    A cewarsa, mutum 10 sun mutu nan take, ciki har da maza tara da yaro ɗaya, yayin da mutum shida suka samu raunuka daban-daban.

    Binciken farko ya nuna cewa saurin da ya wuce kima da kuma tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin.

    Ma'aikatan ceto na FRSC sun garzaya wurin da hatsarin ya faru inda suka kai waɗanda suka ji rauni Asibitin Victory da ke Ogere domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin mamatan ɗakin ajiye gawa na FOS da ke Ipara.

    Kwamandan FRSC na jihar Ogun, Oludare Ogunjobi, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da gargadin direbobi musamman na motocin haya da manyan motoci da su guji yin tuƙin ganganci da gudun da wuce kima da sauran laifukan tuki da ke jefa rayuka cikin haɗari.

  9. Tsohon shugaban Iran Ahmadinejad ya halarci jana'izar Ali Khamenei a Tehran

    ....

    Asalin hoton, MORE

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun wallafa hotunan da ke nuna tsohon shugaban ƙasar, Mahmoud Ahmadinejad, yana cikin mahalarta jana'izar tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, da ake gudanarwa a birnin Tehran.

    Bayyanar Ahmadinejad a wajen jana'izar ta janyo hankali, kasancewar ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan fara yaƙin Iran.

    A lokacin yaƙin, rahotanni sun ce yankin da gidansa yake ya fuskanci hare-hare.

    Ahmadinejad ya shugabanci Iran daga shekarar 2005 zuwa 2013, kuma ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2009 mai cike da cece-kuce.

    Bayan zaɓen ne aka tsare manyan jagororin adawa, ciki har da Mir Hossein Mousavi, Zahra Rahnavard da Mehdi Karroubi, lamarin da ya haifar da zanga-zangar Green Movement a fadin ƙasar.

  10. Yadda ake zagayawa da gawar Khamenei a tsakiyar miliyoyin mutane a Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hotunan da kafafen yaɗa labarai suka wallafa sun nuna ɗimbin jama'a da suka mamaye tituna da manyan filayen taro a birnin Tehran domin yi wa tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, bankwana na ƙarshe.

    Maza da mata sanye da baƙaƙen kaya sun hallara tun daga safiyar ranar jana'izar, inda wasu ke ɗauke da hotunansa da tutocin Iran.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    A wasu daga cikin hotunan, ana iya ganin yadda gawar Khamenei ke tafiya a cikin wata mota ta musamman yayin da dubban masu makoki ke rakiyar ta a kan titunan birnin.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahalarta taron sun nuna alhini da jimami, inda wasu ke yin addu'o'i tare da bayyana girmamawarsu ga mutumin da ya shafe shekaru yana jagorantar ƙasar.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar ta zama ɗaya daga cikin manyan tarukan da aka gani a Iran cikin 'yan shekarun nan, lamarin da ya sa hukumomi suka ɗauki matakan tsaro da na zirga-zirga na musamman.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran bukukuwan za su ci gaba kafin daga bisani a kai gawar marigayin zuwa birnin Mashhad, inda za a yi masa jana'iza ta ƙarshe da kuma binne shi.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Ana ci gaba da gudanar da jana'izar Ali Khamenei a Tehran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei, a babban birnin ƙasar, Tehran.

    Rahotannin sun nuna cewa miliyoyin mutane ne suka fito domin halartar taron jana'izar, yayin da aka wallafa hotuna da ke nuna dimbin mahalarta taron.

    Masu shirya jana'izar sun ce za a yi tattaki da gawar ta amfani da wata mota ta musamman da aka tanada domin ɗaukar gawar marigayin, kuma ana sa ran tattakin zai ɗauki tsakanin sa'o'i 10 zuwa 12.

    Saboda yawan mahalarta da kuma buƙatar tabbatar da tsaro, hukumomin Iran sun sanar da sabbin matakan zirga-zirga a biranen Tehran da Qom, inda aka yi gyare-gyare na musamman domin sauƙaƙa gudanar da bukukuwan jana'izar.

    A ranar Lahadi, sabon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei, bai halarci sallar jana'izar mahaifinsa ba. Sai dai daga baya an fitar da wata sanarwa da aka danganta da shi, wadda ta sake tabbatar da naɗin Gholamhossein Mohseni Ejei a matsayin shugaban ɓangaren shari'ar ƙasar.

    Ana sa ran bukukuwan jana'izar za su ci gaba cikin kwanaki masu zuwa, kafin daga bisani a kai gawar Ali Khamenei zuwa birnin Mashhad domin yi masa jana'iza ta ƙarshe da kuma binne shi.

  12. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar.

    A yau zamu kawo muku labarai da hotunan ci gaban tarukan jana'izar jagoran addinin Iran, da sauran labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.