NLC ta nemi gwamnati ta sassautawa ƴan Najeriya kan tsadar mai

Asalin hoton, NLC/Serap/X
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, NLC ta buƙaci gwamnati da ta gaggauta bijiro da matakan sassautawa al'umma da ma ƴan kasuwa sakamakon ƙarin farashin man fetur.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar samar da albashin da ya dace ga ma'aikata wanda zai yi daidai da yanayin da ake ciki sannan ta riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida ta hanyar amfani da naira, ta kuma faɗaɗa ma'ajiyar man fetur ta ƙasa don buƙatun gaggawa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a wasu jihohin, mai ya tashi zuwa kusa N1,500 ka kowace lita.
Ajaero ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnati ta riƙa bayar da tallafi a lokutan da ake da buƙata ganin yadda Najeriya ta kasance mai yawan albarkatun ƙasa.
NLC ta kuma ce gwamnati ta ci gajiyar tashin da ɗanyen mai yake yi a duniya ina kuma ya yi zargin cewa ana sayar da ɗanyen mai ne kan kamar dala 35 zuwa dala 40 kowace ganga, wanda hakan ya zarce yadda aka ɗora kuɗin man a kasafin kuɗin Najeriya.

















