Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai uku da suka sa jihar Kano ke da muhimmanci a zaɓen Najeriya
Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, jihar Kano na daga cikin wuraren da ake sa ran ƴan takara, musamman a matakin shugabancin ƙasa za su fi mayar da hankali.
Kano na da yawan masu rajistar zaɓe, tana da dogon tarihin siyasa, sannan ta samar da wasu daga cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya da suka taka rawar gani a lokuta da dama na siyasar ƙasar.
A zaɓen 2023, Kano na da sama da miliyan 5.9 na masu rajistar zaɓe, a cewar Hukumar INEC.
Amma yawan masu rajista ba shi kaɗai ne ke nuna muhimmancin jihar ba. Tarihin siyasar Kano da irin sauye-sauyen da aka samu a akalar ƙuri'un jihar daga wannan zaɓe zuwa wancan, na daga cikin abubuwan da ke sa 'yan siyasa ke kallon jihar da muhimmanci.
To, me ya sa Kano ke da wannan matsayi da har kusan kowane ɗan takara ke gogoriyon samun ƙuri'unta?
Dr Kabiru Sufi, masanin siyasa ne kuma malami a kwalejin sharen fagen shiga jami'a a Kano, ya ce akwai dalilai da suke sa Kano ke da wannan tasirin.
Yawan jama'a
Ɗaya daga cikin manyan dalilan shi ne yawan masu rajistar zaɓe da kuma yawan al'umma.
Bayanan INEC na zaɓen 2023 sun nuna cewa Kano na da masu rajistar zaɓe 5,921,370. Wannan ya sanya jihar cikin jihohin Najeriya masu yawan masu rajistar zaɓe.
Sai dai akwai bambanci tsakanin masu rajista da waɗanda suka fito suka kaɗa ƙuri'a. Haka kuma, ba duk ƙuri'un da aka kaɗa ba ne ake ƙirga su a matsayin ingantattun ƙuri'a.
A tsarin zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya, manyan jihohi masu yawan masu zaɓe na da muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun kamfen na jam'iyyu.
Dr Kabiru Sufi, masanin siyasa ya ce yawan jama'a da masu rajistar zaɓe na daga cikin abubuwan da suka sa jihar ke da muhimmanci.
"Dalilai da dama ne suka sa Kano take da muhimmanci. Na farko shi ne yawan ƙuri'a, saboda ita ce jihar da ta fi yawan al'umma, kuma ta haɗa al'umma daga kowane ɓangare na ƙasar. Haka zalika tana cikin jihohin da suka fi yawan waɗanda suka yi rajistar zaɓe."
Tarihin Kano a siyasar Najeriya
Tun kafin samun ƴancin kai, jihar ta kasance ɗaya daga cikin cibiyoyin siyasa da kasuwanci a Arewacin Najeriya.
A Jamhuriyya ta farko zuwa ta biyu, sunan Malam Aminu Kano ya yi fice a siyasar jihar da ma ta ƙasa baki ɗaya.
Aminu Kano ya kafa wata babbar tafiya da ta zama wata makaranta a siyasar Arewa, musamman kan batutuwan da suka shafi talakawa, ilimi da yadda ya kamata a tafiyar da mulki.
A shekarar 1979, jam'iyyar People's Redemption Party, PRP, ta lashe zaɓen gwamnan Kano, inda Muhammadu Abubakar Rimi ya zama gwamna.
Wannan ya nuna irin yadda zaɓin masu kaɗa kuri'a a Kano zai iya bambanta da na matakin tarayya.
Dr Sufi ya ce wannan tarihi na siyasa ya taimaka wajen samar da wani yanayi na fafatawar siyasa a jihar.
"Na biyu akwai batun cewa a baya jihar madubi ce ta siyasar ƙasar. Misali, a Jamhuriyya ta Biyu tana cikin jihohin da suke da gwamna da ba na shugaban ƙasa ba. Wannan ya sa jihar ke cikin jihohin da ake siyasa sosai."
A Jamhuriyya ta Hudu ma, Kano ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa.
Manyan 'yan siyasa da aka haifa a Kano
Wani abin da ya bambanta Kano shi ne yadda ta samar da manyan ƴan siyasa a lokuta daban-daban.
Aminu Kano ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar Jamhuriyya ta Farko da ta Biyu.
A Jamhuriyya ta Huɗu kuma, ƴan siyasa daga Kano sun samu manyan muƙamai a matakin jiha da tarayya.
Wannan ya sa siyasar jihar ta kasance tana da tasiri fiye da batun kujerar gwamna ko ƴan majalisar dokoki kawai.
Dr Sufi ya ce: "Na uku shi ne yanayin siyasar da ta fitar da manyan ƴan siyasa a baya. Jamhuriyya ta Ɗaya da ta Biyu an ga irin su Aminu Kano. Haka a Jamhuriyya ta Hudu ma akwai zaratan 'yan siyasa."
Me ya sa ƴan takara ke neman Kano?
A yayin da ake shirin zaɓen 2027, manyan jam'iyyu na ƙoƙarin ƙarfafa matsayinsu a Kano.
Amma har yanzu ba a iya cewa wace jam'iyya ko ɗan takara zai samu ƙuri'un Kano a 2027 ba.
Tarihin zaɓe ya nuna cewa masu kaɗa kuri'a a jihar sun sauya goyon baya daga jam'iyya zuwa wata a lokuta daban-daban.
Wannan ya sa ake ganin siyasar Kano ba ta da wani tsayayyen tsarin da za a iya amfani da shi wajen hasashen sakamakon zaɓe tun kafin ranar kaɗa ƙuri'a.
Tasirin Kwankwaso da NDC
Idan ana magana kan siyasar Kano a yau, ana yawan ambaton sunan Rabiu Musa Kwankwaso da Kwankwasiyya.
A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Kwankwaso ya tsaya takara ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, kuma Kano na daga cikin jihohin da ya samu gagarumar nasara.
Tun daga lokacin, an samu sauye-sauye a siyasar jihar da kuma cikin dangantakar wasu daga cikin manyan ƴan siyasar da ke da alaƙa da Kwankwaso.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya ci zaɓen 2023 ƙarƙashin NNPP, ya koma jam'iyyar APC a shekarar 2026.
Shi ma Kwankwaso ya sauya matsayinsa na jam'iyya a cikin shirye-shiryen siyasar 2027.
Waɗannan sauye-sauyen sun sa ake sake duba taswirar siyasar Kano kafin zaɓen.
Amma Dr Sufi ya ce bai kamata a ɗauki tasirin Kwankwaso a matsayin abin da zai tabbatar da sakamakon zaɓe ba.
"Ba za a ce baki ɗaya ba, amma lallai zai taimaka wa jam'iyyarsa. Amma lallai takararsa ta samu tangarda saboda ya rasa wasu manyan abokan tafiyarsa. Duk da haka zai yi ƙoƙari, amma zai iya fuskantar tangarda."
Kano na da tabbataccen tsarin ƙuri'a?
Duk da tarihin siyasar jihar, ba ce za a iya hasashen inda ƙuri'un Kano za su dosa a 2027 ta hanyar amfani da zaɓukan baya kawai.
A wasu zaɓuka, wata jam'iyya ta samu rinjaye sosai; a wani zaɓen kuma, masu kaɗa ƙuri'a suka sauya akalar goyon bayansu.
Wannan sauyin na iya kasancewa sakamakon abubuwa daban-daban, ciki har da halin tattalin arziki, aikin gwamnati, ƴan takara, ƙawancen siyasa da kuma yadda masu zaɓe ke kallon al'amuran da suka shafi rayuwarsu.
Dr Sufi ya ce: "Babu wani tabbataccen yanayi ko tsarin zaɓe na jihar. Ana iya samun sauyi a lokaci guda su canja akalar ƙuri'unsu."
Wannan na nufin cewa duk wata magana kan wanda zai lashe Kano a 2027 kafin zaɓe za ta kasance hasashe ne, sai dai idan ana magana ne kan sakamakon zaɓen da aka riga aka gudanar.
Me za a sa ido a kai kafin 2027?
Akwai wasu abubuwa da za su iya taimakawa wajen fahimtar yadda siyasar Kano za ta kasance yayin da zaɓen ke ƙaratowa.
Tarihin jihar a siyasar Najeriya, yawan jama'a da masu rajistar zaɓe, da kuma kasancewar ta wajen samar da manyan ƴan siyasa, duk suna cikin abubuwan da ke sa manyan jam'iyyu da ƴan takara ke kallon jihar da muhimmanci.
Abin da tarihi da ƙididdiga za su iya nuna shi ne irin nauyin da Kano take da shi a tsarin siyasar Najeriya. Amma ba za su iya tabbatar da inda ƙuri'un jihar za su dosa a 2027 ba.
Yayin da ranar zaɓe ke ƙaratowa, sauye-sauyen jam'iyyu, ƙawance, ƴan takara da batutuwan da suka fi damun masu zaɓe za su kasance daga cikin abubuwan da za a sa ido a kansu.
Kuma kamar yadda Dr Kabiru Sufi ya ce, siyasar Kano na iya sauya akala cikin ɗan lokaci.