Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun matan da ke takarar majalisar dattawan Najeriya a zaɓen 2027
Yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar hankali a Najeriya, wasu fitattun mata sun shiga fafatawar neman kujerun Majalisar Dattawa a sassa daban-daban na ƙasar.
Matan sun hada da tsofaffin ƴan majalisa da masu riƙe da muƙaman siyasa da kuma wasu da suka yi fice wajen fafutikar siyasa a matakin jiha da ƙasa.
A jerin sunayen ƴan takarar da INEC ta fitar a baya-bayan nan, mata daga manyan jam'iyyu sun bayyana a yankuna daban-daban, lamarin da ke nuna ci gaba da ƙoƙarin ƙara yawan wakilcin mata a siyasar Najeriya.
Sai dai duk da ƙaruwar yawan matan da suka shiga takara a wannan karo, babban ƙalubalen da ya rage musu shi ne shawo kan ƙalubalen da ke gabansu na lashe manyan zaɓukansu.
Aƙalla 22 mata ne suka bayyana a cikin jerin sunayen da INEC ɗin ta wallafa da sunan ƴantakarar majalisar dattawa a 2027.
Ireti Kingibe - Abuja
Sanata Kingibe na ɗaya daga cikin fitattun ƴansiyasar Abuja kuma mai riƙe da kujerar Sanatan Babban Birnin Tarayya guda ɗaya tilo a yanzu haka.
Ta yi suna a siyasa bayan nasararta a zaɓen 2023, inda ta zama ɗaya daga cikin mata ƴan majalisar dattawa .
Tuni kuma ta ƙudiri aniyar komawa majalisar a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Natasha Akpoti-Uduaghan - Kogi
Natasha Akpoti-Uduaghan lauya ce kuma ƴarsiyasa da ta yi fice saboda yadda ta shiga tsakiyar wani ce-ce-ku-ce da shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akpabio.
Ta shahara a siyasance ne sakamakon fafatawa da ta sha yi kan kujerar Sanata.
Tana daga cikin matan da suka fi jan hankali a siyasar Najeriya a yanzu.
Iyabo Obasanjo – Ogun
Iyabo Obasanjo ƴar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce, kuma ta taɓa zama Sanata mai wakiltar Ogun ta Tsakiya.
Likita ce kuma gogaggiyar ƴar siyasa da aka daɗe da sani a siyasar Najeriya.
Komawarta takarar Sanata a 2027 ya sake jawo hankalin masu bibiyar harkokin siyasa.
Frances Ottah Agbo - Benue
Frances Ottah Agbo ta fito takarar Sanatan Benue ta Kudu a ƙarƙashin APC.
Ta kasance daga cikin fitattun mata da suka samu tikitin jam'iyya a yankin Arewa ta Tsakiya.
Takararta na ƙara fito da mata a sahun gaba na siyasar jihar Benue.
Risikat Motunrayo Abdullahi - Kwara
Risikat Motunrayo Abdullahi ita ce ƴartakarar ADC a Kwara ta Tsakiya.
Tana cikin sabbin fuskokin siyasar jihar Kwara da ke neman wakilci a Majalisar Dattawa.
Nasararta za ta ƙara yawan mata masu wakiltar Arewa ta Tsakiya a majalisar.
Rose Bitrus Mwanti – Plateau
Rose Bitrus Mwanti tana takarar kujerar Sanatan Plateau ta Arewa a jam'iyyar ADC.
Ta fito daga jihar Plateau inda take neman wakiltar yankin da ke ɗaya daga cikin muhimman yankuna a siyasar jihar.
Takararta na nuna ƙoƙarin mata na shiga fafatawar manyan mukaman siyasa a arewacin Najeriya.
Rabi Aliyu - Kano
Rabi Aliyu na daga cikin matan da suka tsunduma siyasar Kano, jihar da yawan mata masu neman manyan kujeru ba su da yawa.
Ta fito takara a ƙarƙashin jam'iyyar AAC, tana neman wakiltar Kano ta Tsakiya.
Shigarta takara na ƙara faɗaɗa zaɓin masu kaɗa ƙuri'a a yankin.
Jamila Muhammed – Kano
Jamila Muhammed tana cikin matan da ke son samun gurbi a Majalisar Dattawa ita ma daga jihar Kano.
Ta fito ne a ƙarƙashin jam'iyyar NDP, tana neman nuna cewa mata ma na iya taka rawa a manyan kujerun siyasa.
Takararta na zuwa ne a lokacin da ake kira da a ƙara bai wa mata dama a siyasar Najeriya.
Idiat Oluranti Adebule - Lagos
Idiat Oluranti Adebule tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas ce kuma Sanata mai wakiltar Lagos ta Yamma.
Malama ce kuma gogaggiyar ƴarsiyasa da ta daɗe tana riƙe manyan muƙamai a gwamnati.
A zaɓen 2027 tana neman takarar Majalisar Dattawa a ƙarƙashin APC.