Iran ta sake aika sharuɗɗan kawo ƙarshen yaƙi ga Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Mohammad Baqer Qalibaf ya soki masu ra'ayin da ke ƙoƙarin jefa ƙasar cikin “yaƙin da babu raar ƙarewa.” Sannan ya kuma tabbatar da cewa Iran ta aika da saƙonni da kuma sharuɗanta ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani.
A wani jawabi gabanin zaman majalisar dokokin Iran, shugaban majalisar ya ce wasu “suna magana ne kan yaƙi amma ba su da wani tsari ko hanyar da za a kawo ƙarshensa.”
Ya ce irin wannan ra'ayi, ta hanyar ƙin amincewa da duk wata mu'amala ko diflomasiyya ba tare da yin la'akari da yiwuwar abubuwan da za su iya faruwa ba, “a zahiri yana jefa ƙasar cikin tsananin yaƙi da ba shi da iyaka.”
“Dole ne mu yi yaƙi, amma a gefe kuma mu riƙa shiga tattaunawa,” in ji shi.
Mista Qalibaf ya kuma jaddada cewa: “An isar da saƙonni tare da bayyana sharuɗɗanmu ga ɗaya ɓangaren ta hannun masu shiga tsakani.”
Ya ce matuƙar ba a cika sharuɗɗan da Iran ta gindaya ba, “ba za a koma kan tsarin shawarwarin da aka yi a baya ba, kuma ba za a bude mashigar Hormuz ba.”
A jiya, Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Iran, ya sanar da cewa Tehran ta isar da sharuɗɗunta na tattaunawa ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar da Pakistan.
Ya ce yanzu Iran na “jiran martanin Shugaba Trump.”



















